ASSALAMU ALAIKUM

DISCLAIMER: {This web site contains information about and regarding among others, present-day Kano State of Nigeria. However, the information here is not necessarily sanctioned by or is not an official information from the Government of Kano State of Nigeria.}

 

Bikin Sallah A Kano

  • PDF

Bikin Sallah A Kano

 

Magaji Galadima

 

A gargajiyance tun daga ranar sallah har zuwa bayan sallah da kwana hudu kobiyar akwai hawa da Sarki yake yi tare da hakimansa da dagatai dakekarkashinsu.  Kullum akwai hawa na musamman da ake yi zuwa wuraredabam-daban.  Da farko akwai hawan ranar sallah, haka kuma rana ta biyuakwai hawan Daushe, sai rana ta uku ayi hawan Nassarawa, a rana ta hudu akanhuta, sai a rana ta biyar ayi hawan Dorayi ko Panisau.  A wannan hawa narana ta biyar akan samu dan sabani. A da can akan yi hawan Dorayi, sannankashegari ayi hawan Panisau amma a `yan shekarun da suka wuce, in an yihawan Dorayi to ba za'a yi hawan Panisau ba, in kuma anyi hawan Panisau toba za'a je Dorayi ba.  Watau dai akan zabi guda ne a hau, wannan ina ganinsaboda nisan wuraren shi yasa.  Wani lokaci kuma yanayin damina yakan zo asamu ba'a girbe amfanin gona ba, to in haka ya faru ba za'a je hawan Dorayiba.  Saboda akwai gonaki a hanyar kum gashi hanyar `yar }arama ce dole saian shiga ta gonakin.

 

To yanzu kuma bari nayi cikakken bayani game da wadannan hawa guda biyar dana zana.

 

Hawan Ranar Sallah

 

Idan aka ce yau sallah ce, to Sarki zai shirya ya bar gidansa da sassafe,ya fita ta kofar Fatalwa ya shiga ta lungun Rimin-kira ya bullo ta filinshahuci ya bi ta gaban asibiti, ya fita ta kofar mata inda nan ne masallacinidi yake. Duk ranar sallah sarki yakan yi shigar fari-da-fari, wato duktufafinsa farare ne haka kuma yasa farar alkyabba wacce kuma yake rufakokuwar, in banda ranar sallah ko juma'a sarki baya rufa kokuwar alkyabba.Bayan an idar da sallah sai Sarki ya hau doki bayan an buga bindiga shimadokin akan hau kili wato fari tas, lokacin da zai zo masallaci baya hawadoki, a kasa yake takowa yana dogara tagwayen masu. Sannan kuma ba a kida kobusa sai dai zagage ne kawai ke yi wa sarki ishara da cewa akwai gangare agabansa ko kuma akwai tudu ko kuma akwai kwana.  Bayan sarki ya hau sai duk sauran hakimai da yaransu suma su hau.  Ananzaka ji wajen ya rude da kade-kide da algaitu da kakaki da tambura, fadawada zagage da farin sarki da `yan ma'abba kuma su rude gaba daya suna yiwasarki kirari.

 

Bayan an gama jeruwa sai makama wanda shine hakimin da a ranar sallah ketsayawa a  can kan gaba ya ja a tafi a shiga ta kofar Wanbai sai a bi taZage a bullo ta Hanga ta filin Shahuci, akan dade kafin a bullo sabodalungun zage yana da matsi kwarai.  Sai abi ta bayan masallacin Juma'a zuwakofar gidan Sarki inda za'a tarar manyan mutane, su gwamna da saurankusoshin gwamnati da Turawa suna zaune akan rufin gidan Shettima,  ko wanehakimi in ya zo daidai rumfar nan sai ya tsaya yayi jinjina sannan ya wucehar Sarki ya iso shima yayi jinjina yana daga kan doki.  Sai gwamna ya tashiyayi jawabi, bayan ya gama sai Sarki ya je ya tsaya a kofar kwaru sai dukhakimai su zo a sukwane su kawo masu gaisuwa ta Jahi.  Sannan shima sai yayijawabi, duk dai yana daga kan doki.  Bayan ya gama, sai ya shiga gida takofar kwaru a buga bindiga ya sauka.  Shikenan sai duk hakimai kowa ya juyaya koma gida.

 

Yawanci duk ranar sallah Sarki ya kan yi shigar fararen kaya ne kamar yaddana fada a baya, yasa farar al'kyabba, ya daura wukar yanka a tsintsiyarhannunsa na dama (hannun riga ya rufe ta shi yasa ba'a ganinta) sannan yarike carbi a hannunsa na dama ya rataya bakan Dabo a kwuibinsa na dama yarataya kwarin a barin hagu, sannan ya rike tagwayen masu, amma lokacin dazai yi jawabi a kofar kwaru sai a karbi tagwayen masun a ba shi wani dogonmashi ya rike sai ya gama jawabi sannan ya sake karbar tagwayen.

 

Da yamma kuma sai dukkan Hakimai suzo a motoci su gaishe da Sarki ayi danFadanci a tashi, shikenan hawan sallah ya kare.

 

Ko da yaushe sarki yayi hawa akwai tsari na musamman da ake bi.  Da Sarki yahau sai ko wane hakimai ya samu wajensa ya tsaya yadda zasu jeru su fitar dalayi.  A ka'ida in anyi hawa dukkan Hakimai wadanda ba `yan cikin gida ba toduk a gaban Sarki zasu tsaya, sune kamar Dan Makwayo, da Dokaji, da Durbi,da Magajin gari, da Magajin Rumfa, da Magajin Mallam da Mai unguwarMundubawa, da Makama, da Gado da masu da Marafa da Matawalle, da Sarkin Bai,da Sarkin Gaya da sarkin Karaye da sarkin Rano da Sarkin Dawaki mai tuta daSarkin Fada, da Sarkin Fulanin Ja'i danawa da  Fagaci da Baura, da Kachalla,da Bunu da Zanna da Sarkin yaki da sauransu. Dukkanninsu wadannan suna yinkunne daya ne a rawaninsu.Haka kuma akwai wasu hakimai wadanda 'yan cikin gida ne, to amma suna zama agaba saboda yanayin sarautarsu.  Misali kamar Dan'iya wanda bayan `yan bangato babu wani mai doki a gaban Sarki sai shi. Ko yaushe Sarki yayi hawa,makama shine ke tsayawa a can gaba, amma ranar hawan Daushe da yake a cikingari ne sai Sarkin shanu wanda shine hakimin cikin gari sai ya wuce kangaba.

 

Akwai kuma masu tsayawa a bayan Sarki wadanda yawancinsu `ya'yan Sarki ne.Sune kamar Barde, da Yarima da Barde Kerarriya, da Ciroma da Dallatu, da Dan'amar, da Danburam, da Dandarman, da Dan'isa, da Danlawan, da Danruwata, daDanmadami, da Dan Lawan da Sarkin dawakin tsakar gida da Galadima da Tafidada Turaki, da Wambai,  sai Madaki wanda shi ba dan cikin gida bane amma yanatsayawa a bayan Sarki.  Sarkin Karaye shine yake tsayawa daga karshe. Su`yan cikin gida suna yin kunnuwa biyu a rawaninsu.

 

To wadannan sune masu tsayawa a gaban Sarki da kuma bayansa.  To akwai kumaainihin masu tsayawa tare da Sarki wato `yan banga. A tsarin hawa dagaDaniya ya wuce sai tawagar Sarki.  Da farko akwai `yan sulke, sai `yanLifida daga su kuma sai  Sarkin Dogarai da ciromansa sai Dan-mori yana kandoki shi da ciromansa sai farin doki an rambatsa masa kwaliya, shi wannandoki ana ce dashi "Dangaba", daga shi sai amaryar Taguwa, bayanta kuma sai`yan baka, sai `yan bindiga wadanda sarkinsu shine mai-ta-fari, sai kuma`yan takubba, sai `yan kagira, sai farin Sarki sai Masu sai Zagage kowanneya yafa gwado ya rike buta ta azurfa sai `yan sanda sannan sai Giwar Sarkiwadda ita ce ainihin tawagar sarki.  Sarki yana daga tsakiya. A dama daSarki ga shamaki, hagunsa kuma ga Danrimi, santar bayansa kuma ga SarkinDawakin tsakar gida. Sauran wadanda ke tsayawa tare da sarki a cikin giwa aal'ada akwai, Sallama, da Wazirin Hawa da Turakin Shamaki da Ciroman Danrimi. Duk wadannan manyan bayin sarki ne.

 

A tarihi akwai wasu manyan nakusa da sarki wadanda ba bayi bane amma  saboda kusancinsu da sarki, ko kuma suma 'yan gidan sarautar Kano ne ta bangare iyeye mata,da sauransu, to sunashiga cikin giwa, misali anan akwai Dan-Sarai , da Jakadan Garko da Galadiman Maitsidau (sarautar gidanmu kenan!).Sannan akan samu wani mai jinin sarauta ya bunkasa amma kuma ba a nada masawata sarauta ba tukuna, kuma saboda kasaita ya wuce ace yana bin hakimi, toanan ma akan yi masa izni ya shiga giwar sarki har zuwa lokacin da za samiwata sarauta ta fado a nada masa. Misali Alhaji Ali Ibrahim kafin a nada shiMatawalle, kasaitarsa ta kai kasaita, don haka yake shiga giwa, to duk dayanzu an yi masa Matawalle saboda kusancinsa da kuma samun fada wajen sarkihar yanzu yafi zama a cikin giwa in anyi hawa.Daga giwar sarki kuma  sai masu tambari suna kan rakuma, sai Dawakin Zagesu kuma kiwatattun dawakai ne kamar guda arba'in duk anyi masu ado, wanilokacin ana tsayawa sarki ya canja doki a cikinsu. sai maja sirdi yana biyeda su.  Sannan sai `yayan Sarki wato `yan Fulani, suma akan dawaki, sannansai masu algaita da sauran makada. Akwai kuma fadawa da zagage wadanda subasu da takamaiman wajen tsayawa sai dai su rika kaiwa da kawowa suna gyaratafiyar takama ta dawaki da kuma daidaita jerin layi. In waje ya cushe kokuma anyi ricibi to `yan Lifidda sune suke zuwa su buda waje, wani lokacinda duka.  Ko yaushe in Sarki zai hau doki ko zai sauka to sai an buga bindiga.

 

Comments  

 
+1 #1 Saminu Yahaya 2012-08-16 12:51
To gashi yanzu an hana wadannan hawa wanda hakan kwata-kwata baiyiwa mutanen Kano dadi ba. Me zakuce game da wannan.
Quote
 

Add comment


Security code
Refresh

You are here: Bikin Sallah A Kano