View more photos of Kano Badala
Ganuwar Birnin Kano: Matsayinta a Tarihin Wayewar Kan Bahaushe
daga
Yusuf Adamu
Geography Department, Bayero University, Kano.
(yusufadamu2000@yahoo.com)
http://www.kanoonline.com/yusufadamu/
Kano, Nigeria
© 2001
Ganuwar Birnin Kano: Matsayinta a Tarihin Wayewar Kan Bahaushe
Ko’ina mutum ya kewaya a birnin Kano yanzu zai lura da
wani abu guda da mamaye birnin a lokuna da lunguna.
watau shaguna. Kano ta zama ko’ina shago. Kila a iya
cewa ci-gaban harkokin kasuwanci ne suka kawo haka,
tunda Kano cibiyar kasuwanci ce tun shekaru aru-aru.
Ba za a ki hakan ba. Za a kuma lura da cewa a halin
yanzu mafi yawancin masana’antun dake Kano a rufe
suke, saboda haka a halin da muke ciki yanzu ba na
kera abubuwa a Kano kamar yadda ake yi a da, amma ana
ta gina shagunan sayar da kayayyakin da ake kerawa a
Legas da Onicha.
Akan yi wa Kano kirari iri-iri ciki har da cibiyar
kasuwanci, cibiyar addinin da al’adu ko ace gari ba
Kano ba dajin Allah, yaro ko da me ka zo an fika. I,
babu shakka Kano gari ne mai tsawon tarihi kuma
wadanda suka gina Birnin Kano shekara da shekaru ba
ragwaye ba ne ba kuma mutane ne masu son zuciya da
hadama da kuma rashin kishi ba. Mutane ne hazikai,
masu kishin birnin Kano da son kyautata bayansu. A
yadda na san mutanen Kano ‘yan shekaru kadan da suka
wuce, a halin yanzu sun zama kanawawa ba kanawa ba
domin kuwa Kano ba ta ransu. Abin da ke ransu abin da
zuciyarsu ke so. Duk wannan shimfida ce na ke yi
dangane da yadda aka sa ido ganuwar birnin Kano ta
zagwanye ta lalace ake kuma kokarin shareta daga doron
kasa duk da irin kimbin tarihin da ta ke da shi.Saboda
haka, za a lura da wani abu guda, an kusa share
Ganuwar Birnin Kano daga doron kasa. Wannan shi ya fi
damuna matuka gaya.
Tarihin Ganuwar Birnin Kano
Duk tsoffin birane a kasar Hausa wadanda aka kafa
kafin dauloli da ma wadanda aka kafa bayan kahuwar
dauloli ko bayan jihadi suna da Ganuwa. Tsofaffin
birane kamar su Kwatarkwashi da Birnin ‘Yandoto da
Birnin Katsina da Birnin Koga da kuma birnin Kano suna
da Ganuwa. Akan gina ganuwar gari ne kuwa domin a kare
gari daga hare-hare da suka yi yawa a wancan zamani.
Birnin Kano ko ace Daular Birnin Kano ta sha karawa da
Daular Katsina da ta Zamfara da ta Zazzau kai har ma
da su Damagaram.
Domin a kare birnin da kuma jama’arsa ne a cikin
karni na 12 (kusan shekaru 800 da suka wuce) aka fara
gina ganuwar birnin Kano. An fara gina Ganuwar Birnin
Kano a karni na goma sha biyu a zamanin Sarkin Kano
Gajimasu wanda ya yi zamani a tsakankanin shekarar
1095 zuwa 1134. An kammalata a zamanin sarkin Kano
Jusa. Kamar yadda Dr. Adamu Tanko na sashen labarin
kasa na jami’ar Bayero ya yi bayani, katangar a
zamanin ta kewaye ~angaren Dala da Gwauron Dutse ne.
Har yanzu in aka je wurin kofar Mazugal za a ga
burbushinta.
Daga nan sai ganuwar ta yi arewa ta bi ta Kofar
Ruwa/Linkwi ta kofar Waika da kofar ansakali. Daga nan
sai aka juya ganuwar ta yi gabas ta bi ta wajen
kurkukun Gwauron Dutse. Ganuwar ta gangaro tayo wajen
Masallacin juma’a na birni sannan ta yi wajen Asibitin
Murtala ta mike ta kofar Wambai. An zagaye birnin
lokacin kenan. A karni na goma sha biyar, saboda yawan
jama’a da ha~akar harkokin kasuwanci, birnin Kano ya
kara ha~aka. A sakamakon haka ne Sarkin Kano Muhammadu
Rumfa wanda ya kara fadada ganuwar Kano. Dr. Tanko ya
bayyana cewa Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ya kara
da’irar ganuwa da kusan kashi 51 kuma ya tayar da
gidan masarautar Kano ya matso da ita dai-dai inda
take a hali yanzu ta yadda ya shiga sabon birni, tunda
kafin ayi hakan, inda gidan Sarki yake a halin yanzu a
lokacin wajen badala ne. A wannan karon ne aka sami
kofofi kamar su Gadon {aya da Dan Agundi da kuma kofar
Na’isa har ganuwar ta tarar da kofar Kansakasli.
Lokaci na karshe da aka kara fadada ganuwar birnin
Kano shine a karni na goma sha bakwai a zamanin sarkin
Kano Muhammadu Nazaki, sarki na 28. Wani masani ya yi
hasa- shen cewa Wambai Giwa shi ne ya yi wannan
gagarumin aiki a lokacin da Sarki ya tafi yaki da
kasar Katsina. Ganin cewa shi wambai Giwa bashi da
lafiya a lokacin da aka tafi yakin, sai ya yi tunanin
me zai yi ya burge Sarki in ya dawo! An ce a lokacin
da aka yi wannan aiki sai da aka yanka shanu dari. To
ganuwar birnin Kano da muke gani yanzu, a wannan
lokaci ne aka ginata. Ba za a ce ba a kara yi mata
komai ba tun daga lokacin har zuwa lokacin Jihadi.
Babu ko shakka ana yi mata ya~e ana kuma kyautata ta.
Wannan dalili shi ne ya sa har ta kawo yau muke ganin
sauranta.
A taron Cikar Kano shekara 1000 da soma mulki, Dr.
Tanko ya yi tambayar cewa da anci gaba da fadada
ganuwar birnin Kano ina za ta kai a halin yanzu? Har
yana cewa da kila yanzu ta kai Kura.
Ba sai an yi dogon bayani ba. Kowa zai iya fahimtar
dalilin gina ganuwar gari. Kuma kamar yadda aka fada a
baya, ba birnin Kano ne kawai ke da ganuwa ba. Manyan
biranen kasar Hausa kamar su Katsina da Zazzau da
Sakkwato duk suna da ita, to amma in anje yau kila sai
dai a tarar da kaofofi kawai ba ganuwa. {anana
garuruwa ma kamar su Kausani a karamar hukumar Wudil
suna da ganuwa. Ana kyautata zaton cewa kafin zuwan
turawa akwai garuruwa fiye da dari masu ganuwa a kasar
hausa, amma yanzu duk sun zama tarihi saboda sakaci da
rashin kishin tushen da mutum ya fito.
Inda za a iya nuna mana majigin yadda ganuwowin birane
suke a kasar Hausa kafin zuwan Turawa da an burge mu
da kuma mun fahimci cewa kakanninmu wayayyu ne kuma
masu basira da fusaha. Ku duba yadda Turawan Mulkin
mallaka suka dauki bakar fata a matsayin koma-bayan
halitta, amma da suka zo cin Kano da yakI sai da suka
sara wa kakanninmu.Lord Lugard a 1903 da ya zo Kano,
ga ruhoton da ya aika Ingila dangane da Badalar birnin
Kano.“lokacin da dakaranmu suka iso Kano sun iske wata
babbar Katanga mai matukar kwari wadda ta kewayen
birnin. Wannan Katanga ta kwancewa hafsoshinmu kai
domin ba su yi tsammanin ganin wani abu kamar haka ba.
Ni kai na ban ta~a gani ko tunanin zan ga wani abu
irin wannan a Afirka ba. Ganuwar ta kai mil goma sha
daya tana da kofofi guda goma sha uku (13). Daga
bisani an auna ta an ga cewa tsawonta ya kai kafa 30
zuwa kafa 50, fadinta kuma kafa 40 ne. Akwai
kududdufai a gabanta da bayanta”
Makomar Ganuwar Birnin Kano
Tun daga farko-farkon shekara ta dubu biyu na fara
rubuce-rubuce akan matsayin Ganuwar Birnin Kano a
halin yanzu, an buga wasu a jaridar jihar Kano watau
Triumph. Ba komai ya sa na soma rubuce-rubuce ba sai
don ganin muhimmancin yin haka, a matsayina na malamin
Jami’a kuma marubuci, ina ganin ta hanyar rubutu ne
hanya mafi sauki a gareni in isar da sako ga wadanda
abin ya shafa, wadanda za su iya yin wani abu da kuma
wadanda ba za su iya yin komai ba.
Duk wanda ya zagaya birnin Kano yanzu zai lura da cewa
akwai alamar cewa a wani zamani da ya wuce tsohon
birnin a kewaye yake da ganuwa. Ita wannan ganuwa tana
daya daga cikin muhimman kayan tarihi da Kano ta dauri
ta bar mana. Sai kuma abin takaici shine gani yadda
aka yi sakaci har ganuwar ta zagwanye. A wasu wuraren
ma babu ita babu alamarta, misali daga kofar Nassarawa
(ta inda Nasara suka ci Kano) zuwa kofar mata babu
ganuwa. Amma daga kofar Nassarawan zuwa har kofar
Waika da sauran alamunta. Abin tambaya anan shi ne
laifin wanene?
Zuwan masu Jihadi Kano bai sa an wulakanta badala ba,
zuwan Turawan Mulkin mallaka bai sa an yi watsi da
kula da badala ba. Lalacewar badala ya somo ne bayn
tafiyar Turawan Mulki, bayan mulki ya dawo hannunmu.
Wannan ba karamin abin bakin ciki ba ne. Ta kai yau
kowa na da ikon sare badala ya yi bulo da kasar ko
kuma ya yi gini a bisanta kuma babu wanda ya isa ya ce
masa me yasa. Ta kai cewa harabar badalar ta inda mai
wucewa zai iya hangenta akalla ya tuna cewa kakannin
mu sun yi abin a zo a gani hukumomin Jihar Kano,
wadanda hakkin kare martabar mutanen Kano ke hannunsu
sun rabe wurare an yi manya-manyan gine-ginen shaguna
da wuraren ajiye ko sayar da motoci. Duba daga kofar
Nassarawa zuwa kofar Kabuga. Abin tambaya anan shin me
Masarautar Kano ke yi akan wannan barnatar da kayan
tarihi da ake yi? Me hukumar gidaje da wuraren tarihi
ta kasa take yi? Kuma me hukumar tarihi da al’adu na
jihar Kano ke yi? Sannan kuma me mutanen cikin birnin
Kano wadanda kakanninsu ne suka gina ganuwar, suke yi
akan hakan?
To, ba za a ce ba a yin komai ba, domin na sadu na
shugaban hukumar gidaje da wuraren tarihi ta kasa na
kusa tattauna da shi akan matsalar. Malam Musa Humbolu
ya yi mani bayanin cewa Masarautar Kano, musamman mai
Martaba Sarkin Kano suna yin iya bakin kokarinsu, sai
dai an fi karfinsu ne. amma ya koka akan cewa wane da
wanen Kano ne abin bai dame su ba kuma sune ke daure
gindin ~annata badalar Kano.
To a gaskiya da sake. Bai kamata mutane su zuba ido
ana kasha mana tarihi ba. In dai har za a rika cika
baki ana cewa gari ba Kano ba dajin Allah, yaro ko da
me ka zo an fi ka kuma Kano Jallah ce babbar Hausa,
amma a kasa kare mata kayan tarihinta a gaskiya an ji
kunya. Duk manyan mu sun zagaya duniya sun kuma ga
abubuwan tarihi da al’umu suka bari, sun kuma san
muhimmancin adana kaya da wuraren tarihi, amma a ce
sun kasa cewa uffan akan kyautata badalar Kano. A
kasar Hausa gaba daya fa ba mu da wasu muhimman kayan
tarihi da ya wuce badala. Bayan Rijiyar Kusugu da
Hubbaren Shehu da marina me muke da shi wanda zai nuna
ayyukan kakanninmu?
In har Turawa duk da wayewar kansu ta zamani za su
rika adana kayan tarihinsu don me mu ba za mu yi ba.
Lokacn da na je Ingila a 1998 na je wani wuri da ake
kira Stonehenge. Na sha karanta tarihin wajen a
littatafai kuma Allah Ya nufe ni da zuwa wurin.
Duwatsu ne aka yi a zagaye, sai masana sun ce an gina
wurin ne shekaru 5000 da suka wuce. Duk da cewa an dan
ta~a tsarin duwatsub har yanzu wurin na nan a killace
kuma mutane daga ko’ina cikin duniya suna zuwa kullun
suna gani. Ana kar~ar kudin shiga da kudin kuma ake
ci-gaba da kyautat wurin, bayan gudunmuwar hukuma da
masu kudI da sauran jama’a.
Kammalawa
Saboda haka, lokaci ya yi da mutanen Kano za su fara
tunanin dakatar da rushe ko kare badalar Kano da kuma
fara shirye-shiryen tada ita. Misali, in an yi niyyar
tada badalar Kano ba abinda zai hana. A fara daga
kofar Nassarawa zuwa kofar Ruwa. Daga bisani a tada
sauran ~angaorin. Wannan ba abu ne da zai gagara ba
sai dai in ba a yi niyya ba. Rashin niyya kuma mun san
ba zai kai mu ga nasara ba.
Idan da gwamnatin Jihar Kano tare da Masarautar Kano
da mutanen Kano za su daura niyya tada badala, na
tabbata Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Majalisar
Dinkin Duniya da wasu kungiyoyi da hukumomin kas ashen
waje ba za su kI taimakawa ba.
Amma mu kan mun yi kudurin ci gaba da fafutukar kare
badala da kokarin tada ita matukar rayuwarmu kuma ko
ba wanda zai yi wani abu a halin yanzu mu, mun fita
hakkI tunda mun fadakar mun yi nasiha mun kuma
ilmantar. Saura da me kila a wasu shekaru masu zuwa za
a sami wani Sarki Gajimasun ko Jusa ko Muhammadu
Rumfa, ko ma a sami wani Wambai Giwan da zai tada
badalar Kano, daga nan kuma a tada na sauran biranen
{asar Hausa. Muna fatan daga wannan rubutu mutane za
su fara tsumuwa.
Brought to you by Kano Online 2001
|