KanoOnline Online Forum

General => History => Topic started by: Nabulsi on October 22, 2005, 03:00:31 PM

Title: Mai kilago!
Post by: Nabulsi on October 22, 2005, 03:00:31 PM
Wai meye gaskiyar labarin aljani mai kilago ne? Ya daina cin mutane yanzu ne ko dama babu shi?
Title: Re: Mai kilago!
Post by: mlbash on November 04, 2005, 12:06:21 PM
Quote from: "Nabulsi"
Wai meye gaskiyar labarin aljani mai kilago ne? Ya daina cin mutane yanzu ne ko dama babu shi?

 NA DAUKA MAI KILAGO SHINE MAI TASHEN KAMA GWAGWARE?
Title: Re: Mai kilago!
Post by: Nabulsi on November 07, 2005, 12:52:27 PM
Quote from: "mlbash"
NA DAUKA MAI KILAGO SHINE MAI TASHEN KAMA GWAGWARE?mlbash kenan! Mai tashen kama gwagware shi ake kira "NA LAKO" ba "MAI KILAGO" ba.
Title: Mai kilago!
Post by: mlbash on November 08, 2005, 08:59:45 PM
TO!  UHM...... JIYA BA YAU  BA!
Title: Re: Mai kilago!
Post by: Sani Danbaffa on February 14, 2009, 06:11:57 PM
Kash, ku lura mana! Ai ni a tsammani na yawancin wadannan abubuwan manya ke qirqirar su domin tsorata yara su guji aikata wasu halaye mara sa amfani (kamar wankan kududdufi). Mai kilago dai ana cewa wai wani aljani ne a cikin kududdufi. Yana da kan mutum da jikin zaki. A zamanin kallo - kallo (1968 - 1974) haka ake nuna hoton sa. Amma gaskiya, babu shi. Akan ce yana cikin kududdufi (kuma akwai kududdufai da yawa a zagayen Birnin Kano, yara su kan je wanka kuma akan samu sau da yawa sukan nitse a ciki har su kan mutu sai a ce Mai Kilago ya cinye su. Ai da akwai labarin 'Yar Madabo ma! Wa i taba ganin ta? Sai labari mai ban tsoro.