KanoOnline.com Forum

States... => Jigawa State Forum => Topic started by: alkanawi on February 01, 2007, 05:24:28 PM

Title: Ina Saminu Turaki?
Post by: alkanawi on February 01, 2007, 05:24:28 PM
Jama'a Saminu ba tserewa kuwa ya yi ba? Yau na karanta wai an rantsar da SSG dinsa a matsayin gwamna.
Title: Re: Ina Saminu Turaki?
Post by: HUSNAA on February 02, 2007, 09:32:58 PM
Ni ma dai naji a Radio Deutche Welle sashen hausa, wai ya dauki hutunsa na duk shekarun da yayi yana gwamna da bai dauka. Ato in yaji dadin hutun ai baya dawo ba kenan, kaga ya samu ironclad excuse for kauracewa EFCC.
Ashe dai a 'Kowane Gauta' naji wannan hutun nasa, kuma ya barwa  alhaji ya'u roni SSG, rukon Jigawa, bayan mataimakin sa yananan kan mukamun sa. Ai bashi da ikon yin haka, kokuwa?
Title: Re: Ina Saminu Turaki?
Post by: ADO BELLO IBRAHIM BIRNIN-KUDU on April 03, 2007, 03:10:11 PM
A gaskiya ina ganin kana da 'yar gaskiya domin kuwa shekaru dai-dai har takwas yayi yana mulkin wannan Jiha amma bai taba tunanin ya huta ba ko da dai-dai da kwana daya saboda tsananin aikin sa, saboda zai iya kwana yana yawo da sunan aiki, sannan kuma yazo ya wuni yana barci kamar kasa, kaga kenan tunda yana amsa sunan shi musulmi ne sallah ma in har zai yi sai dai ya hada na wuni guda yayi su a lokacin da ya farka.

Kuma in ma hutun zaiyi ai hutun sa ya fi karfin na wata uku sai dai na wata takwas (8) koda kuwa shi karamin ma'aikacin gwamnati ne balle gwanan Jiha guda wato kwatankwacin wata daya kenan akan kowace shekara daya daga cikin shekaru takwas da yayi yana mulki, amma ina ganin bayan zabe zaiyi sauran hutun wata biyar din da suka rage masa.

Allah ya dawo da mai girma Gwamna daga hutun sa lafiya.[abibrahim90@gmail.com ]