KanoOnline.com Forum

States... => Kano Forum => Topic started by: Anonymous on December 25, 2001, 09:22:46 AM

Title: Cinkoso a manyan titinan Kano.
Post by: Anonymous on December 25, 2001, 09:22:46 AM
? ?Assalamu alaikum, ? ? ? ina ganin lokaci tuni yayi da al,ummar wannan babban birni na Kano za su yinkuro suga lallai an magance irin cinkoso da manya da kananan titinan Kano suke yi, musamman titin da ya taso daga Ibrahim tayo road zuwa shataletalen gidan Murtala, wanda ya kamata ace an sami gadar sama irinta manyan birane , wacce ina ganin zata magance irin cinkoson abubuwan hawa da wannan babban birni yake samun karuwarsu akoda yaushe, bawai yin wasu sako-sakon kananan titina ba kamar ramin beraye. Ina fata jama,a za su tattauna wannan matsala domin samun waraka mai inganci, Wassalamu alaikum, Abubakar M.Abdullahi.
Title: Cinkoso a manyan titinan Kano.
Post by: Anonymous on May 04, 2005, 09:05:50 PM
Guest I totally agree with your words.