Show Posts

This section allows you to view all posts made by this member. Note that you can only see posts made in areas you currently have access to.


Messages - nene

Pages: [1]
1
chit-chat / Re: How are you feeling today?
« on: June 08, 2007, 05:40:05 PM »
i feel good

2
chit-chat / Re: Forum Avatars
« on: April 26, 2007, 11:58:53 AM »
shaidan wani laananne ne da idan dan adam ya yardar masa yake shiga jikinsa ya aikata babbar illa.yakan shiga jikinka yayi aiki da zuciyarka da imaninka da kuma tunaninka ma dan aikata wasu abubuwan biyan bukatarsa.kuma ta wannan hanya ne zaka ga baka da babban burin da ya wuce hada husuma hakan nan dai ta wannan hanya ne zakaga kana zaune ka fara tunanin wane fa ina jin barawo ne ko kuma wannan mutumin tabbas mashayi ne.kai dai biyan bukatarka ka tada fitina(wadda munsan annabin rahama yace fitina bacci take Allah ya laanci mai tada ta).
shi fa wannan shaidanin shine zai ci gaba da amfani da zuciyarka yayi ta yyana maka abubuwa daganan sai ka fara mafarke_mafarke kai in ka tashi ma sai ka rantse da allah saukar maka akeyi.ana fa tafe sai ka fara tunanin ta ina zan yi wa wani kage daganan sai ka halicci wani suna wanda zaka zo kace kai ka tabbatar wannan shine wane.dole kuma ya zama kamar gaskiya tunda da taimakon shaidan ka halicci wannan suna kuma ka rubuta abinda kakeso a sanda kakeso a gurin da kakeso da kuma lokacin da kakeson.
A lura da yawansu yan rakiya ne  duk randa ta kwabe a tsakiyar titi ma zasu barka har mota tana iya kadeka.A dada lura bana magana sai an yi min magana.
Allah ya laanci shaidan.

3
chit-chat / Re: Forum Avatars
« on: April 25, 2007, 06:46:14 PM »
sallama.
kaico sai in ga kamar babu babban abun tausayi da kunya irin abinda baka sanshi ba kuma kayi ta fallin ka sani din.to bana jin falli zai yi amfani a wannan a harka dan kuwa zunubin rubutacce ne.
dan maiduguroye(haka ake ce maka ko)kai ne babban masanin cewa bama ka bukatar amsa. 8) :)
Hajja husna da zaki daure ki dinga yi mana wannan murmushin naki mai cau zai fi gayyan hakoran da kike sawa.
Alhaji,oga,chief  ;) kasan duk abinda hajja ta fada to anbi dan kuwa ita mafarke mafarkenta yawa ne dasu :P,sai na tausaya mata kar ta dada yin wani duk da dai karin abinyi take samu.

4
chit-chat / Re: Forum Avatars
« on: April 16, 2007, 07:47:35 PM »
assalamu alaikum.
Ina jin dai kamar dai zargi haramun ne,amma ban sani ba ko batan kai nayi.Amma dai koma menene duk abinda ka hakkake akansa ka tabbatar hakane to zaa iya tsai dakai ranar shaida ka kawo ta.wannan tabbas.
Dan maiduguri muna jiranka fassara avatannan dan ba abinda zai sameni ko dameni dan anyi hakan. :)

5
chit-chat / Re: Wata Sabuwar Member
« on: March 19, 2007, 05:07:16 PM »
Assalamu Alaikum.
Gaskiya ba karamar dariya kika bani ba :) ;D ;D,jinjina gareki ya fateez.

6
chit-chat / Re: Wata Sabuwar Member
« on: March 16, 2007, 03:33:36 PM »
Assalamu Alaikum.
Da fatan kowa yana kalau.Ina yi muku barka da jumaa.Wallahi dan maiduguri ina nan banje ko ina ba,banajin ma kuma ina da niyyar tafiya ko ina.Dan haka kananan tare dani zamu tashi tare mu fadi tare.

7
Guestbook & Feedback / Re: A new memeber
« on: March 02, 2007, 10:24:30 AM »
assalmu Alaikum.
Na bawa dan maiduguri amsa,na bawa husna amma jigon zancen akan hajia da kanta nayi shi.wallahi ban san ma da mace nake magana ba da ma dana sani da tuni zan gano bakin zaren.Maganar da nake ita ce hoto wanda hajia ta nuna damuwarta akai dan idan aka duba sakonta guda biyu zaa ga cewa na farko tace ana tallan kai na biyu kuma tayi zancen tsaleliyar budurwa.A tawa fahimtar matsalar dai bata wuce me yasa wata zatazo tasa hoton da yafi na kowa koda kuwa ba ita bace a jiki.
Malama husna na gode kwarai sai dai kinyi magana akan cewa in nice a hoto dan haka kina shakka. A kano kike?yiwa Allah ki aiko min da adireshinki zanzo idan kinaso zan kai ki har gaban iyayena.

8
Guestbook & Feedback / Re: A new memeber
« on: March 01, 2007, 02:39:34 PM »
Alhamdulillah.
Jahilci mummunan abune muna rokon Allah yai mana tsari dashi.Suna inkiya,gwaggo,iya,inna,baba,umma,mama,mami,dada duk suna ne na iyaye.Idan danka yaci sunan mahaifyarka a wani gurin wasu sukan kira wannan da da ainihin abinda suke kiran uwar nan tasu.a garin bauchi suna kiran yaya da sunan dada amma a wani garin dada yana nufin kaka ne.Idan ka haifi yarka kasa mata sunan uwarka kake kiranta da umma to tabbaci hakika ita wannan ya ta tashi daga yar kwana bakwai ta koma yar shekara hamsin dan ana kiranta da sunan uwarka haka kake nufi ko?dan haka duk mai suna iya a fadin duniya tsohuwa ce tukuf.Akwai ka da basira mun karu kwarai da ilminka.
Idan kadaukeni yarinya,bazawara,matar aure tsohuwa yar shekara dari kai kanka idan kai tunani sai kaga bazai kare ni da komai ba,kai hasalima ka nuna ka damu ne shi yasa har kake da lokacin ayyana ni wacece.
Kasan Allah ban taba tunanin meye sunanka bama balle kai wanene,kaikuwa kasamu lokacin tunanin karya nayi ko gaskiya,fara nake ko baka,yarinya nake ko tsohuwa wannan shi ake kira damuwa da wani.Na gode kwarai da kulawarka. :)  8)

Baa rama zagi da zagi duk wani na gari yasan wannan,gaskiya ma kuma babana bai koya min hakan ba.sai dai nasan abu guda idan kaga mutum a kwararo yana zagin uban wani to tabbaci hakika kafin ka kai karshen wannan loko zaka jiyo shi ya kalli danuwansa da suke uba daya ya ce kai ubanka, kai daya zagi babanka me zaka ji Allah sai dai kayi dariya kawuce.Dan haka nima na dara
Malama husna hoto kikace ko ko da zolaya kikayi nacire angama.

9
Guestbook & Feedback / Re: A new memeber
« on: February 27, 2007, 08:13:01 PM »
Assalamu Alaikum.
Da fatan kowa kalau.malam kana maganar ribbons ina jin dai baza ashiga aljanna dasu ba ko?wallahi ribbons din ko na gaske ne mutumin da bai san mutuncin wani dan adam ba a doron kasa to ina tabbatar maka a tafe yake kawai amma ba mutum bane shi.Da zaka daina bari bacin rai yana rinjayar abinda zaka fada da sai kafi bada maana.Rubutu kayi amma ciki fal shirme dan kana so ka kare abokinka akan an bashi amsar maganar da yayi wanda shi baka ga laifin da yayi ba sai ni.
ba sunana nunun ba sunana zatu yarana suna kirana da nene na tabbatar baza arasa wanda ya sanni ba a fadin wannan guri.mutum yana da wani hali na kushe abinda yayi mishi dai dai dan jerantuwa  acikin wata alumma:raina bai baci ba sam magana akayi na bada amsa.

10
Guestbook & Feedback / Re: A new memeber
« on: February 26, 2007, 06:51:29 PM »
salamu alaikikum.
Wannan shine shigowa ta ta uku cikin wanna forum din ban sani ba bawan Allah ko a ina ka sanni?a tsarin musulunci bana jin ko mijin da nake aure yana da ikon da zai min magana kamar wata baiwar sa balle kai da ban sani ba.kana da matsala ne dani?dan kuwa abun ya dauren kai a duk alummar da suke wannan guri kazabi sunana wanda bayan gaisuwa da nai muku ban kara cewa komai ba kai min magana yanda ranka yakeso ko kana da hujja?ina da aure kuma ni ba wasa na zo yiba nan gurin dan haka in tsarin wasan yan forum dinnan ne haka to ai sai a dinga bayani kafin mutum ya shigo.na san akwai shugaba a wannan gurin dan haka dan allah ya dinga shawartar members dinsa su dinga rike kansu da girma da mutunci.

11
Hausa Music and Poetry (Kade-Kade da Wake-Wake) / Re: RE-Ahmed S Nuhu
« on: January 11, 2007, 09:26:48 PM »
Allah ya jakanshi,ya sa Aljanna ce makomarsa.
Allah yaba families din shi hakuri,Ameen.

12
Guestbook & Feedback / A new memeber
« on: January 11, 2007, 06:14:11 PM »
Salam,
just want to say hello to everybody.Am a new member.Hope i
will be welcome.
nene

Pages: [1]

Powered by EzPortal