Show Posts

This section allows you to view all posts made by this member. Note that you can only see posts made in areas you currently have access to.


Messages - Sas

Pages: [1] 2 3 ... 9
1
General Board / What Do You Love About Nigeria?
« on: February 14, 2006, 11:31:18 PM »
Quote
I wont ask you why in your opinion you think Niugerians are the unhappiest people cos obviously you dont consider palestinians that don't really have a country of their own...or Somalian who have known nothing but starvation and war all thgeir lives....or Afghans,Iraqi's,who have aliens as leaders and are constantly and literaly living in war zones...... yup there ARE other unhappy people in the world....


Well you did mentioned these poor "unhappy" people. However you fail to mention also that generally the westerners are the most unhappy people in the world! Nothing seems to be sufficient and they are always having problems either personal or financial...Hence some kill themselves or any one aroud them... I think those people you mention could be even happier than your average Brit or American!!! Just an opinion.

2
General Board / Kano City etc
« on: December 05, 2005, 09:00:48 PM »
Try Google Earth Dave! It should remind you of Kano although I must say a newer Kano!!

3
General Board / Want to fly over Kano...you can!!!...for FREE...NOW
« on: December 05, 2005, 08:54:54 PM »
Hi all,

Note: This is not an advertisement but I just thought this might be of interest to some of you!

How amazing is this; I was able to fly over my house in Kano from the comfort of my room in the U.K; I was able to glimpse around the great city of Kano from the air while still in the UK; I was able to see how smaller/bigger my house was to my neighbours'; I was able to visit my Secondary school and saw those roofs that I had studied under for many years; Most importantly, I was able to see most of the places in Kano that I hadn't seen for over a year!!!

All this due to the advancement in technology and the Amazing thing that Google has become today.

With "Google Earth" you can do all these now for K-town, the first city in Nigeria to have this improved feature. Download it now and start flying over the city.

Other cities are on their way, its just that right now they started with Kano because, what else, its K-town, the best city in 9Jah! Yaro ko da me kazo an fika!!!

this is the website to download from <<http://earth.google.com/>>

With Peace!!

4
General Board / Shawara ga gwamnan Kano
« on: December 16, 2004, 04:47:48 AM »
Salaam,

Gyara anan daya da zanyi maka Indabawa shine bance lallai wai ya kamata a daina turanci kwata kwata a wannan "forum" dinba ballanta nace a rinka Hausa kawai. Manufata itace matsala ce da na gani a tare da Hausawa a yanzu da Hausar ma in ba ai sa'a ba sai ta bace daga bakin 'ya'yanmu ko jikokinmu. Wannan shine abun da Turawa suke nema kuma da alama suna kan hanyar samun nasara.

Kawai abun da nake nufi kenan. Da fatan ka fahimta! A huta lafiya.

JAK

5
General Board / Lokacin jarrabawa
« on: December 11, 2004, 08:52:56 PM »
Salaam,

A taya mu addua lokacin jarrabawa ya karaso, Allah ya taimakemu baki daya. Ameen!

Bissalam

6
General Board / Shawara ga gwamnan Kano
« on: December 11, 2004, 08:50:12 PM »
Salaam,

Da kyau ganin cewa wasu ma suna tunanin cewa lallai ya kamata ayi wani abu game da yadda yaren Hausa yake sulalewa daga bakin mutane. Manufarmu anan itace abun takaici ne duk da cewa wai ana kiran wannan zauren "KANOonline" amma ace wai yawancin mutane daga Kano bazasu iya fahimtar me ake tattaunawa ba.

Ina ganin cewa wani yana karya baiyi daidai ba sai dai in ka tabbata cewa hakkan karya yake yi, kuma duk da haka bai kamata ka karyata shi a fili ba.

Allah ya zaba mana abin da yafi alheri kuma ya daukaka harshen mu a duk fadin duniya.

Mu huta lafiya.

7
General Board / Shawara ga gwamnan Kano
« on: December 07, 2004, 03:58:05 AM »
Salaam,

Na gode. Ai dalilin da yasa nake rubutu da Hausa shine ni ban ga dalilin da zaisa ace wai lallai sai nayi magana da turanci sannan mutane(Hausawa) zasu fahimta. Dalili kuwa shine in kuka lura da illar da turanci yakeyi mana a kasarmu, to Wallahi kafin mu ankara sai 'ya'yanmu sun tashi ko Hausar ma basaji.

Ku lura kuga shekara kamar talatin baya ai Hausa tafi karfi akan yanzu. In na duba naga yadda 'yan Chana ko Japan, ko "Turawa" kai har ma larabawa, abun yana bani sha'awa yadda suke karantar kusan komai da harshensu. Sai kaga mutum yazo daga Chana ko turanci baya ji amma in fannin math ne ko physics ko ma aikin likita ne, wanda yake jin turancin bai yaga masa ba.

Inaga wani abu ma da Gwamnan ya kamata yayi shine ya samo hanyar da zamu karfafa Harshen mu ya zama cewa bai bata ba nan ba da dadewa ba.

Wani abun dariya shine rannan ina magana da dan uwana a "MSN Messenger" saiyace ai wai lalle sai nayi mashi rubutu da turanci. Naso ace a gabana ya fada da na...

Bissalam

8
Kano Forum / Taimakon yayi kadan.
« on: November 24, 2004, 08:01:44 AM »
salaam,

Amma munji kunya. Na tsani naga muna daukar wani abu da yazo daga amerika muna likawa kanmu. Hatta kaya da nake gani a jikin mutane almajirai, magidata, yara da kowa ma in dai suna nuna mana wani abu daga aladar amurika na tsani abun. Abun da su amerika din suke so kenan mu kuma muna dauka kamar...kamar...kamar...."yan Nigeria!!!"

9
General Board / Shawara ga gwamnan Kano
« on: November 24, 2004, 07:46:58 AM »
Salam,

Wani abu da zamu duba muga shine:

Ina duban Nigeria ne kamar tsintsiya. Danko ne yake rike da zaborin. Mutum yana iya ciran guda da kanshi, ko dakansu suna iya faduwa kuma da zarar an warware dankon nan ko tsintsiya ta rabu kenan.

Zamu iya kallon Nigeria a halin yanzu kamar haka. Kwnakin baya ina magana da wani dan kudu yake ce min ai shi a nashi raayin shine a raba Nigeria gunduwa gunduwa shine zai kawo zaman lafiya a ssassr mu. Wannan kalamai nashi sunsa nayi tunanin ashe akwai mutane da dama da suke tunanin haka kuma bamu sani ba cewa nan gaba ko wannan raayi nasu zai yi tasiri. Yanzu idan Nigeria ta rabu (yaya gari kamar Kano zai tafiyar da alamurran sa?-- A gaskiya banga yadda zaai ba, jira muke sai hakan ta faru sannan mu yi hankali).

Manufa ta anan shine bamu san abun da zai faru ba a nan gaba ba kuma hakika akwai damar da cewa Nigeria zata iya rabuwa da babu abun da zai hana in hakan ya taso da karfi. Kuma me kano zatai in hakan ya faru?

Bissalam
10
General Board / Shawara ga gwamnan Kano
« on: November 20, 2004, 08:32:14 AM »
Salamu Alaikum,

A ko yaushe ban taba tunanin menene dalilin da yasa Gwamnatin tarayya ce zata bawa Jiha jiha kudin da zasu tafiyar da alamuran jahohin ba. Sau da dama sai naji ance ai Gwamnatin tarayya ce bata aiko da kudi ba saboda haka Gwamnatin jiha basu da halin gudanar da wani abu. Gaskiya a tunanin na wannan ba dai dai bane.

Kama tayayi a ce jiha kamar dai Kano yadda allah ya bamu saar cinikayya da amfanin gona mu muke daukar nauyin yawancin aiyukan cikin jihar mu ba Obasanjo ba. Dalili na anan shine, kasancear samu Mai da akai a wasu sassan kasar tamu yasa duk jikin mu yayi sanyi akan mu mu tashi muyi aiki da baiwar da Allah ya bamu mu tashi kudade daga jihar mu. Kafin a samu mai, shin akan wa muka dogara? Ji nake da kanmu muka dogara?

Ina ganin ya kamata daya daga cikin abubuwan da Shekarau ya kamata ya fara dubawa shine yayi zai samu ya tada tattalin arzikin jihar kano ya zamana bamu dogara akan Gwamnatin tarayya ba. In yaso in Man da muke ji dashi ya kare, a kalla muna da abin da zamu ci gaba da amfani da.

Bissalam,

11
General Board / Birnin Iko Kano
« on: November 20, 2004, 08:23:36 AM »
Salamu Alaikum,

haba mutanen Kano? Me yake damun mu? Zuwa na birnin iko yan kwanaki da suka wuce nayi mamakin yadda da wuya ka samu mutum mai karfi a jikinsa yana yin bara. Kwata kwata basu yarda da wannan ba. A takaice, abun da ya bani mamaki shine maimakon matasa kamar mu su rinka yin bara sai kaga suna sayar da abu buwa da dama dan dai su samu abun da zasu ci. Amma a kano fa? Inaa ai gwara na yi bara ko tumasanci na samu naci da dai na samu ina sayar da wani abu. A kan hanya a iko zaka samu abubuwa da dama kamar su kayan moto, taya, tip, kayan keke, abun sha, abun ci, tumatur, allayahu, dankali, kaset na bidiyo da CD. A takaice dai komai.

Wannan yana nufin cewa muma yan kano mu fito kan titi mu sayar da Tubani ko masa? AA!!! Amma dai ya kamata mu lura muga cewa bara ma kanta baa yarda mutum yayi ta a addinin mu ba kuma ace mutum da karfinsa yana bara? Allah ya kiyaye. Gwamnati bata aikinta a wannan fannin yadda ya kamata.

Bissalam

12
General Board / Shin menene niyyarku a rayuwarku????
« on: November 20, 2004, 08:14:35 AM »
Salamu Alaikum,

Sau da dama in nayi magana da mutane sai suce min ai suna da niyyar su aiwatar da wasu abubuwa a rayuwarsu da zasu kawo ci gaban Hausawan mu.

Amma sai abun mamaki manyanmu basa yi iyaka karfinsu domin suga sun aiwatar da abubuwan da suka bukaci aiwatarwa lokacin suna da kuriciyarsu duk da cewa suna da halin yin hakan.

Me yasa kuke ganin hakan yana faruwa kuma ko kuma zaku zama kamar hakan??

amma babban dalilin wannan shafi shine idan kana da wasu abubuwa da kake so ka aiwatar da kake ganin zasu kawo ci gaban mutanen Hausawa da ma dukkan Nigerian to ka fade su in da hali.

Misali kada ka/ki ce zan samar wa da mutane abinci ka/ki dakata anan. Wannan ba shine abun da nake nufi ba. Ka/ki na iya cewa misali insha Allahu zanyi kokari naga ta hanyar kaza...kaza...kaza zanyi kaza...kaza...kaza da zai samar wa da mutane kaza...kaza...kaza.

A takaice ba fadar cewa zanyi kaza ba amma yaya zakai kaza din?

Ni musali in Allah ya yarda in ina da hali zan ga na samar da wata Gasa ta yara yan firamare da sakandare wanda ya samu nasara zan dauki nauyin karantunsa (In ina da hali). In duk Shekara mutum daya attajiri a kano zai dauki nauyin yaro daya da karatunsa, kuma in ace duk shekara an samu attajirai dari sun yi hakan, bayan shekara goma, an samar da mutum 1000 masu ilimi kuma hakan zai taimakemu da izinin ubangiji. Idan ko wane attajiri zai dauki nauyin mutum biyu kuma dauk shekara a samu atajirai dubu....kuyi lissafin.

Bissalam

13
General Board / Zuwa sararin Samaniya
« on: November 20, 2004, 08:02:47 AM »
Salamu Alaikum,

kwanakin baya wasu masu ilimin Kimiya sun samu nasarar harba "jirgi" zuwa sararin samaniya da niyyar cewa nan bada dadewa ba zasu fara kai mutane fasinja. Me yiwuwa nan da shekaru kalilan.

Tambaya anan itace, shin zaka/zaki? ka/ki amsa tambayar ba tare da tunanin me yiwuwa kudin zaiyi yawa ba sosai. Kawai kina ko kana tunanin zaiyi kayu zuwa gurin ko kuwa?

Bissalam

14
General Board / manyan makarantun Duniya???
« on: November 20, 2004, 07:59:08 AM »
Salamu Alaikum,

Dan Allah inada tambaya amma inaso idan ka/kin bada amsa ki/ka fadi a inda kake in da hali. Inaso naga a cikin wadannan makarantun, CAMBRIDGE, OXFORD, HARVARD, MIT, YALE, CALTECH, etc wacce ce tafi suna a duniyar ka/ki?

Nasan misali wadanda suke a amurka (yan asalin amurka) kwata kwata bama su san wasu makaranta CAMBRIDGE ko OXFORD ba so dole su zabi HARVARD, MIT... a saman su.

Ku sani cewa bawai ina tambayar wacce makaranta ce tafi ba. Kawai waccece tafi suna.

Misali. Da wanda yace maka a Harvard ko Oxford yazo, wannene yafi kima a gurinka.

Bissalam

15
General Board / 9/11 Sha Daya ga watan Satumba
« on: November 20, 2004, 07:53:26 AM »
Salamu Alaikum,

Mutane da dama da nai magana da a Kano basu yarda cewa Usama Bin Laden ne ya hada wannan hari a WTC ba. Ko kadan bani da wasiwasi a zuciyata cewa Osama ne ya hada wannan hari.

Amma kuma sai gashi naga a cikin amurkan kanta wasu suna tunanin ba hakan bane. Kuma da nai tunanni sai naga cewa, lallai hakane, duk da yake ban tashi daga bakana na cewa Osama ne ya hada harin ba, maganganun da wadannan mutane suka fada (turawa yan asalin amurka) ya sa nayi tunani kadan.

Sun ce ai ba makawa Bush ne ya hada wannan hari da kansa ba laifin wani Osama. Na dakata anan tukunna...Na baku dama kuyi tunani akai tukunna

Bissalam

Pages: [1] 2 3 ... 9

Powered by EzPortal