haba saraki ! idan baka sani ba bari in shaida maka wannan labarin da ka bayar duk mai nazari ya san cewa ma anar labarin shine sakkwatawa sun nuna fillanci ne,watau a maimakon su koya wa wannan bakon sun tura shi kano a koya masa ,ko ka fahimta?

sannan ina son ka san cewa sarkin musulmi bayan kasancewar sa babban sarki,har ila yau shine halifar mujaddadi shehu usmanu Danfodiyo saboda haka yana da saukin gani ga dukkan musulmi har ma wadanda ba musulmi ba sun sha musulunta a sanadiyyar karimcinsa .

dangane da batun hawan sallah kuwa wannan ya nuna cewa ba ka san sakkwato ba,ai ba sakkwato ko garuruwan da ke karkashin sakkwato suna hawan sallah