Ban gane "Tanko" ba!
Please explain pronto!
Kana tsakiyar mata kenan, kokuwa an haife ka bayan an hayayyafi yara mata.
Sanin halayen matan ne da naga ka lakanta yasa na ce ko kai Tanko ne, having observed the behavior from yr sibling sisters!!

Abun da ke bani mamaki da ke fati duk hakurin ki kuma ace ke anti-polygamy ce. Mun taba wannan argument din dake. Look at it daga point of view na mazan mana.mu mata sai dai hakuri. Kinsan wani abu, bana tsoron kishiya, ta zo tayi ta balain ta. Ta gaji ta daina. tunda dai ina son mijina zan iya tolerating. kuma Allah ya ce su auri har 4 in har zai yi adalci. Maganar Bakangizo hakkun. Hafsa Allah ba da zama lafiya
Lol sister, kishiya fa ba tada dadi. Maza kuma ba sa iya adalci. Dole akwai wace tafi kwanta musu a rai, kuma yawanci ba mai yin hakurin ne da su ba. Wacce take yi musu yanga a cikin matan nasu, itace su ka fi zumudin ta. Amma kuma bayan haka, komai me wucewa ne, kuma a karshe halin mace da dabi'o'in ta ne ke sa ko miji yayi fatali da ita ko kuma ya rusuna mata.
Akwai kuma wata hikima ma wacce Allah Yasa a auren mace fiye da daya. Ita kanta macen ta fi son zama da mijin bayan yayi mata kishiya, fiye da inda ita kadai ce. Wannan ma baiwa ce da ga Allah da ke dada dunkule aure dan kada ya sukurkuce. Amma sai dai anyi hakuri din dai, tun da instinct din mace a farko shine ta fice ta bar gidan bayan anyi mata kishiyar ko gabanin yimata. Sai kuma daga baya tai ta nadama.