Jama'a barka da war haka,
Bayan tsawon lokaci da kudurar wanni babban dan-uwan jama'ar kanoonline da yayi kokari ya jawo hankalin yan-uwa a kan su dunga zumuntar filin taron kanoonline, ya faskara.
Wanna dan-uwa wanda sunan sa an rufa saboda umarni da suka wuce karfin mu. yayi kokari ya yayi juyin mulki.
Amma da temakon manya manyan dakaru na jama'ar ta kanoonline wanna juyin mulki Allah bai bashi nasara ba.
Amma ko da haka ya temaka yan uwa daga nahiyar duniya sun rugo da gudu sun dawo filin taro don su nuna goyan bayan su ga wanna fili na kanoonline.
Koda yake wanna juyin mulki ya bata wa wasu daga jikin manya rai, wannan kokari ya jawo hankalin jama'ar zuwa ga gani ya dace a runka ziyara a kai a kai.
Sakamakon haka yasa wanna dan-uwa ya kunya ta, har yana lafazin zai bar wannan kungiya ta arewa ya koma ta masu zumunci da zunden yan arewa.
Da temakon wani zakaran filin wanda aka fi sani da suna Gogannaka ya samu ya sasanta al'amarin ya baiya nawa wannan dan'uwa wannan abu da yayi, yayi kyau saboda ya baiyana abin da ke damun sa, kuma wannan ya nuna sonda yake yi wa wanna majalisa ta yan arewa, da yasa har ransa ya baci, har yasa ya dauki wanna babban aiki, da ya so ya kawo karshen wannan kungiya.