Wannan santin nina tafka shi, amma dai ya koya man hankali dan friends din basu man da wasa ba! Wato a wajen aikinmu aka gina mana sabon ofis. Ran da muka shige sabon ofis din da karfe sha biyu muka fito break. Da ma mu biyar ke taruwa kullum mu ci lunch mu koma aiki. To, a rannan dai, an hau kan su shinkafa da salad ana ta faman ci. Da cokali cike a hannuna, sai na daga kai na dubesu na ce, "yau fa mun koma sabon ofis din mu." Shegu, sai suka yi shuru kamar ba su ji abinda na fadi ba. Sai can wani daga cikinsu ya ce, "shago!" Aka tuntsure da dariya, har na tashi ina zaginsu na shiga daki.
