News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

HELP ME TRANSLATE

Started by MySeLf, January 16, 2007, 06:21:17 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 6 Guests are viewing this topic.

waduz

Quote from: EMTL on December 09, 2007, 10:58:24 AM
Assalamu alaikum,
Wadannan fa?

cirko cirko - an tsaya an rasa abinda za'ayi

koli koli - sama-sama

karera -  wake da murya mai dadi

laferu - wannan fulatanci ne, ko?

almanzuriya - larabci? ban sani ba, ko guddiranci ne? ko sunan kuliya ne?

garnas - abinci: gyada da suga ake soyawa

kuyafa - umarni: mutane su yafa gwado?

kundukuki - wani bangare ne a jikin mutum, ko?

A karemu masana.....



EMTL, a gaskiya ka dan tagaza! Amma dai sai da taimakon zaure! Muda, all the words are Hausa, we still wait for more translations from the "hausanicious" with apologies. ;D

ummutameem

koli koli................can sama
laferu...................pillow(hausawan ghana)
kundukuki..............body part( not sure what)

MySeLf

Angaisheku!
Gaskiya kuna hausa mai fasa kai wurin nan....... Hhmm ???
!!!........................I STAND 4 ISLAM..........................!!!

amira

Ai kuwa, i was thinking of that word koli koli yesterday
didnt know what it meant but now i see.
an gaisheku like Myself said ;).
*Each day is definately defining me and finding me*

Dan-Borno

what of these words?

1.   facala
2.   gwamutse
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

HUSNAA

Quote from: Dan-Borno on December 11, 2007, 12:14:05 AM
what of these words?

1.   facala
2.   gwamutse


Facala means wife of one's husband's senior or junior brother.
gwamutse means  all mixed.
Ghafurallahi lana wa lakum

IBB

Facala: Also means Facaka (Splendour) Facala da kudi
IHS

ummutameem

facala also 'kishin sauri' ie ur husband's bro's wife like husnaa said

waduz

Quote from: waduz on December 08, 2007, 11:17:50 PM
Wadannan fa?

cirangami

cirko cirko

koli koli

karera

laferu

almanzuriya

garnas

kuyafa

kundukuki

A karemu masana.....


Bari mu gani ko.....

cirangami.......the blanket like portion of the large intestin.

koli koli........in ana fada sai wanda yafi karfi ya dinga sama da dayan yana bugawa a kasa. Wato yayi koli koli da shi.

karera.......same as cirangami.

laferu........wani tsumma ne da ake daurewa a karkashin wutsiyan jaki don ya kama shimfidan sosai.

almazuriya......girman kai.

garnas.........groundnuts! amma gyada ne da suga ake hadawa ana yanka gutsure gutsure ana saidawa.

kuyafa...........cokali kenan.

kundukuki.........muscles dake kafa ta baya kasa da gwiwa.


Amma dai kam hausawan asali sai su taimaka wajen yin fassara sosai, don ba tabbas anan.










MySeLf

Waduz, Amma dai wannan ba hausa bace zunzurutu ko? ga dukkan alamu da larabci ciki...
ko kuma wani yare...
!!!........................I STAND 4 ISLAM..........................!!!

waduz

Da yawan kalmomin kam hausa ne. Amma kaman su almanzuriya ina ga larabci ne. Garnas kam ai daga ji ma an shortening groundnuts ne, don haka turanci ne. ;D

ummutameem

kundukuki.........muscles dake kafa ta baya kasa da gwiwa.

kundukuki acc. to ur definition, doyar kafa kenan











[/quote]

HUSNAA

Quote from: waduz on December 12, 2007, 09:08:15 AM
Garnas kam ai daga ji ma an shortening groundnuts ne, don haka turanci ne. ;D

hahahahaha! La haula wa la kuwwata illa Billah! Lallai garnas kam! Bahaushe kenan!! Allah Ya dada jan zamanin sa!  ;D ;D
Ghafurallahi lana wa lakum

MySeLf

Quote from: waduz on December 11, 2007, 10:37:45 PM
cirangami.......the blanket like portion of the large intestin.
karera.......same as cirangami.
laferu........wani tsumma ne da ake daurewa a karkashin wutsiyan jaki don ya kama shimfidan sosai.
almazuriya......girman kai.
garnas.........groundnuts! amma gyada ne da suga ake hadawa ana yanka gutsure gutsure ana saidawa.
kuyafa...........cokali kenan.

Wallahi tunda nake bantaba jin above kalmomin ba......
Really Interesting though.... Keep them coming!
!!!........................I STAND 4 ISLAM..........................!!!

waduz

Myself, the "k" in karera is pronounced as "Q", okay?