News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

ALLAH WADAN WANNAN MUTUM

Started by HUSNAA, August 23, 2007, 08:15:35 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

HUSNAA

Ina sauraron BBC and I heard wannan labarin mai ban takaici da bakin ciki. Raina yayi mugun baci matuka. Labarin shine wai a Katsina wani mutum mai suna Abdurrasheed Abubakar ya sami dansa dan shekara biyu yayi masa dukan fitar hankali ya farfasa masa jiki da kunnuwa sannan ya wurga shi kofar gida ya barshi kwance cikin jini, sai uwar yaron ce ta zo ta dauke danta. Dan shekara biyu.
Uwar yaron ta kai karar mijin nata kotu, kuma an same shi da laifin son hallaka dansa an bashi daurin wata shida a gidan yari wai don ya nuna nadama.
Da aka tambaye shi dalilin duka irin wannan sai yace wai yaron na yawan yi musu kashi!! Don Allah kuji wannan abin takaici. Dan shekara biyu.. wanda inda iyayensa masu hali ne da har a lokacin ma yana cikin diapers!! kai jama'a!

Uwar yaron dai tace kiyayyar da mijin yake nuna mata ne ta  shafi yaron., don dama can bayan haihuwar yaron uban ya furta ya ce ba zai karbe shi ba koda an kai masa shi. Inji matar da tana bayani ta ce uban ya ce wai in am maido masa dan gidan sa, sai ya wurgo shi ta katanga ya fado kasa, kuma yace yaron ba daya yake da sauran 'yayan sa ba.
to wautar uwar da kuma magabatan ta shine da suka dauki yaron suka maida shi gidan alhali uwar ba ta gidan. Ni yaushe zan yi wannan gangancin duk iya talauci na? Tir Allah Ya Kyauta. Alkalin dai shi ma ransa ya sosu don ya sa an tura uban yaron  gidan kaso.

Shekaranjiya na gama karanta wani littafi  Dombey and Son,  (Charles Dickens) wanda makaman cin abin da yafaru ne a wannan labarin da bbc ta ruwaito yau. Shi ma dai uba ne ya kafa wa diyar sa karan tsana  tun ranar haihuwar ta har sai da Allah Ya rugurguza mutumin takwanan sannan ya gano kuskuren sa. Allah Ya sawwake.
Ghafurallahi lana wa lakum

Dan-Borno

Hajiya, kwarai da gaske, idan muka yi la'akari da
irin wadannan abubuwan da ke faruwa a kasashen
mu na arewa, zamu fahimci cewa wallahi tallahi
zunzurutun JAHILCI ne tare da rashin tarbiya wanda
a ka gada.  Fi sabilillahi, idan ba haukaba, ta yaya
zaka yi wa yaro dan shekara biyu dukan kawo wuka?

Musulunci ya tsara mana yadda zamu yi tarbiya wa
yayanmu ba tare da mun sha wuya ba.  Ba zan
manta ba, shekaru uku da suka wuce, mun tsinci
wani yaro a bakin post office na Maiduguri, dan
shekaru uku, muka ajiye shi da sunan cewa washe
gari zamu nemi ubansa,  Abin mamaki shine, washe
gari sai yace mana shi bazai koma gun ubansa ba
saboda yana yi masa duka kullum.  Ya dauke mu
tsananin lokaci kafin muka sha kan yaron yakoma
gun ubansa.

Na lura na gane cewa mafiya yawancin mu bamu
iya tarbiyar da yara ba, ban sani ba, ko dai saboda
yawan talauci ne ko yaya.  Saboda, mutumin da
bashi da sana'a kwakkwara amma sai kaga ya tanadi
iyalai wadanda suka fi karfinsa, sai kaga kowane da
ma kana jin haushinsa, baka kula da karatunsa ko
kuma lafiyarsa.  Wannann shine musabbabin jawo
irin tallace tallace da yan'mata suke yi domin su
rufawa kansu asiri.

A gaskiya muna bukatan mu tashi haikan wajen wayar
da kan jama'a, kuma hakki ne ya rataya akan mu
da muka fahimci hakan.
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

Mufi

#2
As a mother my heart aches when i heard of stories like this. Talauci da rashin abun hannu shi yake sa iyaye mata ke tsayawa cikin irin wannan mugun zama da miji zai ce wai baya san dan da aka haifa ;D ;D ;DAllah ya ganar da irin wadannan mutane Amin.

'Ya'ya amana ne daga Allah, ranar tashin kiyama za'a tambayemu yanda muka tarbiyantasu, ilmintarsu, da kuma yanda muka kula dasu ALLAH YA BAMU IKON YIN DUKA TSAKANI DA ALLAH DA KUMA YI DAIDAI AMIN. Yanzu shi wannan mutum bai sani ba wannan yaran ya zama shine mai jinkanshi anan duniya da kuma lahira.
Life is like a flower; more exquisite and precious when shared with others.

Bajoga

Quote from: mufi on August 23, 2007, 11:58:12 PM
;D ;D ;DAllah ya ganar da irin wadannan mutane Amin.

Hmm! wannan shine kawai abin fadi, Allah ya ganar dasu.

Mukuma Allah yasa mu kara rike namu da gaskiya tare da rikon amana.
HASBUNALLAHI............

bakangizo

Husnaa, ai muna cikin wani hali a nijeriyar arewa. Muna da matsala sosai, fiye da yadda kike zato. Wannan ma ai kadan ne daga cikin abubuwan da ake tabkawa a kullum. Amma sam hankalin mu yana wani wurin dabam. Wato abin yana da alaka ne da rashin ilimi (boko da addini) da tsabar talauci. Idan har bamu yi maganin wadannan abu biyu ba, to haka zamu kasance har "yaumuttanadi".

amira

Subhanallahi Allahsarki :'( gaskiya wannan abun dayawa yake dan yaro fa!! a blessing from Allah who would one day take care of him when he comes to his old age, who will make prayers for him when he passes away. Wannan abu dai ba imani, duniyar ta fara lalacewa ko kuma ince tana cikin lalacewar. Anya kuwa mutumin bashi da tabin hankali me yakai yakawo da zai gibji dannan, sai kace wanda aka aiko daga sama >:( dan kawai da nayi masu kashi. Wannan ma hauka ne kawai tir da irin wannan halin.

Allah shirya wannan lamarin ya kawo sauki ameen
*Each day is definately defining me and finding me*

HUSNAA

Hankalin sa sarai Amira. You should have heard him talk on BBC. and the guy is at least in his mid fifties. Allah Sarki poor kid. He reminds me when my kid was about that age and my newly acquired houseboy at that time took him out to go and buy something that I'd sent him to buy. Along the way, he met a cousin of my husband's who was going to unguwa as it was evening, and she took the baby with her. Ta goya shi ta tafi da shi. Meanwhile my houseboy came back and as I wasnt aware he had taken my son with him I didnt ask him where he was and he never told me that he'd taken him with him or that my husband's cousin had taken him with her to where ever she was going. Kuma there was no light in the house. My house boy kuma was dressed to the nines and wanted to go somewhere urgently. so he deposited what ever it was and went away. Meanwhile there I was thinking that my son was probably with his granny. About an hour I went in search of him as no one had brought him as a result of one thing or other (yana kuka and all that kind of excuse). I was told he wasnt there. Muka hargitsa gida looking for him and he was nowhere to be found. Then someone told me that he'd seen someone go off  with him. What he meant was my house boy. but as my houseboy was new in the house not many ppl knew him very well. A kind of helpless frustration stole over me. I went weak all over and my knees gave way. Sai na fara karanta one sura or other, cant remember.  Da Allah Zai takaita almarin, sai someone said ai its that new houseboy of yrs that took him with him. So luckily kuma one of my inlaws happened to just arrive as there was no transportation in sight at the time. We went in search of the houseboy and found him at his house which was just two streets away from us. there he was sitting on a dakali with no baby. My heart sank further. However, he told me ai wance ce ta karbe shi daga hannu na. I mean I swear I am not given to ashariya amma a lokacin ban san lokacin da na danna masa ashar ba. I was so wound up! anyway the long and short of it was that I couldnt rest easy till the woman came back and she came  back wajen 11 PM lol! I was marching up and down like wadda aka sata aikin 'yan sanda.... kai! So u can imagine I am transported to that time da naji labarin wannan dan karamin yaron... poor kid!!
Ghafurallahi lana wa lakum

Dan-Borno

 ;D  ;D Hajiya kenan, feathers of the same bird.....
Mata da jaraban yaro.  What about my Uncles reaction?
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

Muhsin

Quote from: amira on August 24, 2007, 04:22:52 PM
Subhanallahi Allahsarki :'( gaskiya wannan abun dayawa yake dan yaro fa!! a blessing from Allah who would one day take care of him when he comes to his old age, who will make prayers for him when he passes away. Wannan abu dai ba imani, duniyar ta fara lalacewa ko kuma ince tana cikin lalacewar. Anya kuwa mutumin bashi da tabin hankali me yakai yakawo da zai gibji dannan, sai kace wanda aka aiko daga sama >:( dan kawai da nayi masu kashi. Wannan ma hauka ne kawai tir da irin wannan halin.

Allah shirya wannan lamarin ya kawo sauki ameen

Though, everything has been said before, but I think I'll support Amira's words. Don't think, completely, a sane, real sane person could ever do something like such to his biological son. Don't you think Husnaa that if that scenerior happen in countries like America, England or any other developed countries, that that man would have been checked psychologically before proceeding to court?
Get to know [and remember] Allah in prosperity & He will know  [and remember] you in adversity.

amira

Quote from: HUSNAA on August 24, 2007, 06:26:41 PM
Hankalin sa sarai Amira. You should have heard him talk on BBC. and the guy is at least in his mid fifties. Allah Sarki poor kid. He reminds me when my kid was about that age and my newly acquired houseboy at that time took him out to go and buy something that I'd sent him to buy. Along the way, he met a cousin of my husband's who was going to unguwa as it was evening, and she took the baby with her. Ta goya shi ta tafi da shi. Meanwhile my houseboy came back and as I wasnt aware he had taken my son with him I didnt ask him where he was and he never told me that he'd taken him with him or that my husband's cousin had taken him with her to where ever she was going. Kuma there was no light in the house. My house boy kuma was dressed to the nines and wanted to go somewhere urgently. so he deposited what ever it was and went away. Meanwhile there I was thinking that my son was probably with his granny. About an hour I went in search of him as no one had brought him as a result of one thing or other (yana kuka and all that kind of excuse). I was told he wasnt there. Muka hargitsa gida looking for him and he was nowhere to be found. Then someone told me that he'd seen someone go off  with him. What he meant was my house boy. but as my houseboy was new in the house not many ppl knew him very well. A kind of helpless frustration stole over me. I went weak all over and my knees gave way. Sai na fara karanta one sura or other, cant remember.  Da Allah Zai takaita almarin, sai someone said ai its that new houseboy of yrs that took him with him. So luckily kuma one of my inlaws happened to just arrive as there was no transportation in sight at the time. We went in search of the houseboy and found him at his house which was just two streets away from us. there he was sitting on a dakali with no baby. My heart sank further. However, he told me ai wance ce ta karbe shi daga hannu na. I mean I swear I am not given to ashariya amma a lokacin ban san lokacin da na danna masa ashar ba. I was so wound up! anyway the long and short of it was that I couldnt rest easy till the woman came back and she came  back wajen 11 PM lol! I was marching up and down like wadda aka sata aikin 'yan sanda.... kai! So u can imagine I am transported to that time da naji labarin wannan dan karamin yaron... poor kid!!

Ai lallai kuwa Hajiya kinga ta kanki, shi ma dai da wawta yake he should have told you that he has taken so and so, at least ki rage haushi knowing that it wasnt a complete stranger that took him.

Allah kawo sauki kuma ya kiyyaye Ameen.
*Each day is definately defining me and finding me*

waduz

Wato da farko dai, a irin namu fahimtar shine Allah SWT ke halitta kuma ya rayar, ba wani dan adam ba. Wannan yaro da shiga wannan hali, in sha Allahu rabbi sai ya zamu abin mamaki a nan cikin duniya. Sakaiya kuma Allah swt zai yi wannan mutum daidai gwargwadon abin da ya aikata na aikin assha da mugunta.

Amma abin dubawa anan, shin kowane magidanci ne ya ke da cikakkiyar hankali da zai iya mallakar iyali? Anya kuwa wadansu magidantan ba miyagun mashayan kwayoyi bane? Fisabilillahi ban ga ta yadda mutum, mai cikakkiyar hankali, mai mutunci, kuma haifaffe na kwarai da zai aikata wannan abin takaicin ba. Ai ko ba dansa na cikinsa bane, irin wannan mugunta tsantsa ga yaro ba ta dace ba. Amma dai dansa ne kuwa, ko dai yana zargin uwar yaron ne da aikata wani abu? :-[

Bajoga

Quote from: HUSNAA on August 24, 2007, 06:26:41 PM
Hankalin sa sarai Amira. You should have heard him talk on BBC. and the guy is at least in his mid fifties. 

To!! Gaskiya HUSNAA (da kuma sauran jama'a) in dai ace hankalinsa sarai, to akwai abun dubawa.
1- Shin anya shi cikakken musulmi ne kuwa?
2- Shin yana da ilmin addini da na zamani kuwa?
3- Shin aurensa da matarsa anyi shi bisa ka'idar musulunci kuwa?
4- Akwai hukuma a garin? kima wane mataki suka dauka?

Lallai idan akwai matsala daga cikin wadannan tambayoyi, to ko za'a samu matsala sosai a society.

Allah ya karemu ya kuma ganar da masu irin wannan dabi'a.
HASBUNALLAHI............

Al-Nazeer

Ina so ku bincika menene asalin maganar da baban yaron yasa ya fada cewa bazai kamanta yaron da sauran yaransaba. yana iya faruwa akwai wani sirri a boye. nagode

Mohammed Nazeer Dayyabu kazaure
kazaure1@yahoo.com
The hard way the only way

HUSNAA

#13
Quote from: Al-Nazeer on August 30, 2007, 04:30:30 PM
Ina so ku bincika menene asalin maganar da baban yaron yasa ya fada cewa bazai kamanta yaron da sauran yaransaba. yana iya faruwa akwai wani sirri a boye. nagode

Mohammed Nazeer Dayyabu kazaure
kazaure1@yahoo.com

To in ma akwai wani sirri na boye, (wanda baka nufin komai illa cewa dan shege ne), to ina ruwan yaron? Shi yace a haifeshi? Ba kurum Kaddara ta fado kansa bane? Sai kuma a azabtar da shi saboda haka? Kuma ma ai a kwai misalai da dama na inda iyaye maza suke kin kaunar 'yayan su saboda kurum sun kafa wa uwar 'yayan kahon tsana.
Ni personally na san matar da mijin ta saboda tsananin rashin so, a lokacin da take da juna biyu, ya furta wai wannan cikin bana sa bane. Da Allah Ya tashi wanke ta, sai ta haiho dan da duk cikin 'yayan nasa ba mai kama da shi kamar wannan yaron da yayi kazafi akai.

Maza dai, Allah Ya dora musu raggaggen tausayi wajen kula da iyali. Kuma ba komai bane illa cewa daya daga cikin jarraba war da aka dora musu ce dan saboda sune masu nauyin kula da iyali.

To BJG, mutumin cikakken musulmi ne mana. In so far as yadda shi yake kallan kansa da kuma yadda da yayi da Allah SWT. Batun ilmi kuwa wannan akwai tambaya akansa kam. Ilimi kam akwai bukatar kari gare shi. Auren sa da matar sa kuma, Allahu 'a'alam. Amma ina kyautata tsammani ba dansu na farko bane tare. Hala suna da wa'yansu 'yayan. Inma ka bibiya, itace matarsa ta lalle, tunda irin haka tafi faruwa da matan da aka fara aurowa. Kuma ma ko auren yana bisa kaidar musulunci ai ba zai hana aika aika da ta faru ba. Ina masu kashe 'yayan su wai su suna kare mutuncin iyalin su? Kaji uba ya sa 'yarsa cikin swimming pool ya danna kanta cikin ruwan har sai ta daina lumfashi? Wai shi ta kunyata su? Me za kace da wannan? Ko kuwa yarinyar da ta ji labarin an sayo akwatun da za a jefa gawarta bayan dan uwanta ya kashe ta, kuma da sanin uban ta. Allah Ya Sa kwananta na gaba ta samu ta gudu da ga gidan uban nata ta shiga buya? Meza kace wa wannan ma? Kuma in both cases duk musulmai ne.
Ghafurallahi lana wa lakum

Bajoga

Maza dai, Allah Ya dora musu raggaggen tausayi wajen kula da iyali. Kuma ba komai bane illa cewa daya daga cikin jarraba war da aka dora musu ce dan saboda sune masu nauyin kula da iyali.
[/quote]

Wato gaskiyar magana bawai maza bamu da tausayi bane, kinsan kowane mutum da irin nasa halin.

Karki manta akwai matan da idan sun haifi dan shege (musamman a boding school), sai su kashe yaron ta hanyoyi daban-daban, wasu ma su wurgar ta yaron wa bula, me zakice da irin wannan kuma?
All what i believed dai shine kowanne dan adam da irin nasa halin. Allah shi kyauta, amin.

Batun musulcin mutum kuma wannan wani abune dayake da wuyan sha'anin wajen gane gaskiyar abin, sai dai Allah kawai.
Mu dai musulmai munsan cewa sallah kyakkyawa tana kawar da mugun alkaba'i, to ashe idan muka ga mutun yana sallah kuma munanan ayyukansa suna karuwa, to akwai ayar tambaya akansa.

Allahu a'alamu.
HASBUNALLAHI............