News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother

Started by admin, October 25, 2007, 10:48:29 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

_Waziri_

Quote from: mustidoc on October 26, 2007, 01:01:21 AM

Innah Lillah Wa Innah Ilaihi Rajiun. Allah Ya ji Kan ta, Ya rahamshe ta, Ya yafe mata, Ya kuma sa ta a Aljannah Fiddausi, Ameen summa Ameen. Allah kuma Ya ji kan iyayuen mu da ka kannin mu baki daya, ameen. In tamu ta zo, Allah Ya sa mu chika da Imani, Ameen.

Amin Amin. Have been a way for too long it seems. Prof. my heart felt!

But am sure she is in God beneficence by now. If for anything, our culture, civilisation and faith has been blessed thru her in your person. You may not have an idea of how you shaped and still continue to shape minds in the mould of the truth towards appreciating God and his bouties in the 21st century using the Islamic, Hausa, West African spectacle. It gives us alot of pride as we remember to pray for her always as one blessed soul that outletted the adoring souvenir in you.

Allah Yayi mata rahama Yasa mu iya 'counting achievements' dinmu yadda tayi yanzu, 'at the point of our death too'.   

manasmusa

KULLU NAFSIN ZAIKATIL MAUTI. Tabbas, dukkan mai rai sai ya dandani mutuwa. Allah ya jikanta ya gafarta mata, ya kuma sa aljanna ce makomarta Allah ya bada jimirin jure rashinta. mu kuma in tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani mu tashi da shi. ameeen.
Such is Allah your Rabb, His is the creation and...

Abdalla

Lunar Horribilis - Godiya
Jama'a, Assalamu Alaykum,

A madadin iyali na da kuma ni kai na, ina mika dimbin godiya ga daukakin majalisa saboda sakonnin ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar mu, Hajiya Rabia't Muhammad Lawan da aka dinga aiko mana ta majalisa, ta tarho, ta imail da kuma da yawa wadanda suka dinga zuwa har gida tare da iyalansu, da kuma wadanda suka dinga zuwa ofis.

An haifi Malama Rabi'at, kamar yadda aka fi saninta, a garin Gwarzo, Kano, a shekarar 1942. Ta rasu ranar Laraba, 24 ga Oktoba 2007 da misalin 10.00 na dare a sakamakon arangamar ciwon asma da ke fama da shi da ya taso mata gadan-gadan lokaci guda.

Duk da cewa ba ta taba fitowa a wani dandalin da nake fitowa ba a wajen nazarce-nazarce na, amma ta yi wani babban fice a inda ba a zata. Masu karatu watakila za su tuna da wani ayarin haruffan Hausa ma su lankwashe-lakwashe  wanda a ke kira Rabiat (rabiat.ttf). To sunanta na sakawa wannan ayarin haruffan lokacin da na kirkiro gundarin haruffan rabiat.ttf ranar 2 ga Yuli, 1995. Na saka sunanta ne domin gode mata da irin gudunmowar da ta bayar wajen ilimintar da ni; saboda haka na sakata a cikin tunanin jama'a ko bayan ranta – sai kuwa ga shi duk da ta rasu, amma kusan dimbin jama'a da dama na tunawa da ita a duk lokacin da aka yi rubutun Hausa da ayarin haruffan Rabiat.

Mun gode mun gode mun gode bisa ta'aziyyar da aka dinga kawo mana har tsahon kwana bakwai-- kuma majalisa a wakilce ta ke sosai domin da yawa 'yan majlaisa suna tare da mu, tun da ga jana'izar har bayan share makoki. Wannan ya dada tabbatar min da muhimmancin wannan mattattar alheri domin zuwan su da kuma zaman su (wadansu ma har da iyalansu) ya taimaka kwarai wajen daurewa da wannan rashin da muka yi.

Mun gode da goyon baya, da kuma addu'o'in da a ka yi mana. Allah Ya karba. Allah Ya ba da lada. Allah Ya bar zumunci. Allah Ya jikan dukkanin Musulmai. Lallai rai dadi ne da shi; kuma rasuwa zafi ne da ita. Allah Ya sai mu cika da imani.

Abdalla, a madadin dukkanin iyalan Muhammad Uba Adamu Kantoma, Mazaunin Kano, Najeriya.


bb1and2

Allahu akbar!!! muna fatan Allah ya jikanta ya rahama mata kuma Allah yasa Aljanna makoma ita da dukkan musulmin da suka rigamu. Mu kuma Allah yasa mu chika da Imani idan tamu  ta zo. Ina kuma mika ta'aziyya ta ga kaninsa Ado Uba Adamu.

ajingi

Inna Lillahi wa inna Ilaihirajiun! May her soul rest in peace and ours to come in the glamors of faith.


Allah (SWT) ya jikanta da rahamah, Ameen!!
I object to violence because when it appears to do good, the good is only temporary; the evil it does is permanent.

IBB

Inna lillahi wa inna illaihir rajiun. Allah yaji  kanta yasa ta huta Ameen Allah bata gidan Aljannatul Firdausi. Allah ya ji kan musulmai kaba daya ya kyautata namu zuwan Ameen
IHS