News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

KUNGIYAR TSANGAYAR ALHERI

Started by Bashir Ahmad, June 22, 2011, 08:38:47 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Bashir Ahmad

TSANGAYAR ALHERI kungiya ce mai zaman
kanta wato ba ta gwamnati ce ko ta siyasa
ba, wasu mutane ne hazikai masu kaifin
basira da hangen nesa, Allah ya basu ikon
kirkirarta domin fahimtar da al'umma game
da abubuwan da suka shafi al'amuranmu
na yau da kullum da kuma irin matsalolin
dake fuskantarmu a wannan zamani, mai
cike da rikita-rikita, da karancin jin tsoron
Allah a zuciyoyin jama'a, inda babba ke
danne karami, mai kudi ke danne talaka
wato zaman kashin dankali kenan.

Manyan Manufofin wannan kungiya sune:
Ilmintar da al'umma gami da sada zumunta,
hakan tasa kungiyar taci sunan TSANGAYAR
ALHERI sannan kaso 75% na aikin wannan
kungiya na wakana ne a shafukan Yanar
Gizo kamar Yahoo Group, Facebook da
sauransu, ta nan ne kungiyar ke samun
damar aika sakon da take son aikawa ga
al'umma.

TSANGAYAR ALHERI kungiya ce ta kowa da
kowa (wato Maza da Mata, Matasa, har ma
da Dattijai) musamman yan arewacin
Najeriya (Nigeria). Sakamakon mafiya
yawan yan wannan kungiya Hausawa ne,
hakan tasa kungiyar ke gabatar da
harkokinta da harshen Hausa gami da
koyarwar addinin Musulunci. Amma haka ba
yana nuna cewa kawai Musulmi dan arewa
ke da damar shiga kungiyar ba. Indai
mutum dan asalin Nigeria ne da ya haura
shekaru 18+ yana da damar shiga kungiyar
kai tsaye tare da yardar shugabannin
kungiyar.

Kungiyar na zama meeting dan tattaunawa
sau biyu a duk sati. Ranar Talata da Ranar
Juma'a, ranar Talata shugabannin wannan
kungiya na zama don tattauna abin da ya
dace a gabatar ranar Juma'a (Agenda) wato
zasu duba ne a cikin satin da ya gabata
wane abu ne ya faru da ya dace a tattauna
akansa don samun mafita. Idan ba abin da
ya faru cikin satin shugabannin cikin irin
basirar da Allah ya hore musu zasu kawo
wani abu da yake damun jama'a don
tattaunawa.

Ranan Juma'a ranan ne za'a hadu da
dukkan dan kungiya daga jihohi daban-
daban a fadin kasar nan, anan za'a tattauna
abin da shugabannin suka yanke ranar
Talata. Daga karshe kuma a bawa kowa
dama da yayi tambaya akan abubuwan da
aka tattauna ko wani abu da ya shige masa
dahu a cikin wannan kungiya. Sannan
bayan tambaya sai a bawa masu kawo
shawara dan cigaban kungiya dama da su
fadi shawarwarinsu.

Na san za ayi mamakin jin cewa ana
haduwa meeting da mutanen jihohi daban-
daban, to wannan meeting dai ana zamansa
ne cikin iska, wato ta wayar hannu
(Handset) da misalin karfe 12:30 na dare
(Free Call / Conference Call) sannan kuma
wasu johohin masu members da yawa suna
yin meeting cikin sati biyu biyu, amma
wannan ba ta waya ake yin shi. A zahiri yan
kungiya ke haduwa don tattauna abubuwa
da dama game da kungiyar.

Ga duk mai sha'awar zama daya daga cikin
dan wannan kungiya to kofa a bude take
kuma cikin sassaukar hanya, misali idan
mutum na amfani da shafin sadarwa na
Facebook zai iya binciko kungiyar ta hanyar
rubuta sunanta (TSANGAYAR ALHERI) anan
zaiyi rijista/joining sannan ka/ki aje
numbarka/ki ta MTN wadda za'a kiraka/ki
yayin meeting na kungiya. Kuma idan
mutum baya amfani da shafin Facebook zai
iya zama dan wannan kungiya ta hanyar
tuntubar wadannan bayin Allah:-

Jibrin Muhammad Yusi - Bajoga -
08034760327

Abdulqadir Sardaunan Facebook -
08039644376

Ali Adamu Jauro - 08032950453

A cikin wadannan mutane duk wanda
mutum ya tuntuba zasu yi masa cikakken
bayani game da wannan kungiya daidai
yadda mutum zai gamsu. Anan bazan wuce
ba sai nayi amfani da wannan damar
amadadin kai na nake godiya da addu'ar
Allah ya karawa wadannan jajirtaccun
mutane hikima da basira ya kuma daukaka
su a dukkan al'amuransu, sannan ya cika
musu wannan buri nasu na fahimtar da
al'umma, kamar yadda suke yi ba dare ba
rana. Allah ya saka da alheri.
Fatana Allah ya daukaka wannan kungiya
da dukkan yayanta baki daya. Allah ya
yalwata alheri a cikinta. Allah ya kara hada
kanmu, Ya cika mana burinmu game da
wannan kungiya ta TSANGAYAR ALHERI
amin.
A karshe ina kira da jama'a masu irin
wannan akida da son ci gaban al'umma da
su shigo wannan tafiya, su ma su bada tasu
gudunmawar ga al'umma. Da irin Ilmin da
Ubangiji ya hore musu. Don shi aikin alheri
baida kadan, kuma mutum bai san wane
aiki Ubangiji zai duba daga cikin ayyukansa
yayi masa Rahma da Gafasa ba. Don duk
abin da kayi shi don Allah ba don wani ya
gani ya fadi ba to tabbas Allah zai baka
mafificin lada. Allah ya shige mana gaba a
dukkan al'amuranmu na yau da kullum,tar da
harkokinta da harshen Hausa gami da
koyarwar addinin Musulunci. Amma haka ba yana nuna cewa kawai Musulmi dan arewa ke da damar shiga kungiyar ba. Indai mutum dan asalin Nigeria ne da ya haura shekaru 18+ yana da damar shiga kungiyar kai tsaye tare da yardar shugabannin
kungiyar.

Kungiyar na zama meeting dan tattaunawa sau biyu a duk sati. Ranar Talata da Ranar Juma'a, ranar Talata shugabannin wannan kungiya na zama don tattauna abin da ya
dace a gabatar ranar Juma'a (Agenda) wato zasu duba ne a cikin satin da ya gabata wane abu ne ya faru da ya dace a tattauna akansa don samun mafita. Idan ba abin da
ya faru cikin satin shugabannin cikin irin basirar da Allah ya hore musu zasu kawo wani abu da yake damun jama'a don tattaunawa.

Ranan Juma'a ranan ne za'a hadu da
dukkan dan kungiya daga jihohi daban-
daban a fadin kasar nan, anan za'a tattauna abin da shugabannin suka yanke ranar Talata. Daga karshe kuma a bawa kowa dama da yayi tambaya akan abubuwan da
aka tattauna ko wani abu da ya shige masa dahu a cikin wannan kungiya. Sannan bayan tambaya sai a bawa masu kawo shawara dan cigaban kungiya dama da su fadi shawarwarinsu.

Na san za ayi mamakin jin cewa ana
haduwa meeting da mutanen jihohi daban-daban, to wannan meeting dai ana zamansa ne cikin iska, wato ta wayar hannu (Handset) da misalin karfe 12:30 na dare (Free Call / Conference Call) sannan kuma
wasu johohin masu members da yawa suna yin meeting cikin sati biyu biyu, amma wannan ba ta waya ake yin shi. A zahiri yan kungiya ke haduwa don tattauna abubuwa da dama game da kungiyar.

Ga duk mai sha'awar zama daya daga cikin dan wannan kungiya to kofa a bude take kuma cikin sassaukar hanya, misali idan mutum na amfani da shafin sadarwa na Facebook zai iya binciko kungiyar ta hanyar
rubuta sunanta (TSANGAYAR ALHERI) anan zaiyi rijista/joining sannan ka/ki aje numbarka/ki ta MTN wadda za'a kiraka/ki yayin meeting na kungiya. Kuma idan mutum baya amfani da shafin Facebook zai iya zama dan wannan kungiya ta hanyar
tuntubar wadannan bayin Allah:-

Jibrin Muhammad Yusi - Bajoga -
08034760327

Abdulqadir Sardaunan Facebook -
08039644376

Ali Adamu Jauro - 08032950453

A cikin wadannan mutane duk wanda
mutum ya tuntuba zasu yi masa cikakken
bayani game da wannan kungiya daidai
yadda mutum zai gamsu. Anan bazan wuce
ba sai nayi amfani da wannan damar
amadadin kai na nake godiya da addu'ar
Allah ya karawa wadannan jajirtaccun
mutane hikima da basira ya kuma daukaka
su a dukkan al'amuransu, sannan ya cika
musu wannan buri nasu na fahimtar da
al'umma, kamar yadda suke yi ba dare ba
rana. Allah ya saka da alheri.
Fatana Allah ya daukaka wannan kungiya
da dukkan yayanta baki daya. Allah ya
yalwata alheri a cikinta. Allah ya kara hada
kanmu, Ya cika mana burinmu game da
wannan kungiya ta TSANGAYAR ALHERI
amin.
A karshe ina kira da jama'a masu irin
wannan akida da son ci gaban al'umma da
su shigo wannan tafiya, su ma su bada tasu
gudunmawar ga al'umma. Da irin Ilmin da
Ubangiji ya hore musu. Don shi aikin alheri
baida kadan, kuma mutum bai san wane
aiki Ubangiji zai duba daga cikin ayyukansa
yayi masa Rahma da Gafasa ba. Don duk
abin da kayi shi don Allah ba don wani ya
gani ya fadi ba to tabbas Allah zai baka
mafificin lada. Allah ya shige mana gaba a
dukkan al'amuranmu na yau da kullum,
amin!
Bashir Ahmad
bashahmad29@gmail.com
08032493020





































































































amin!
Bashir Ahmad
bashahmad29@gmail.com
08032493020
Above All Fear Allah (S.W.A)

bakangizo

Haven't actually read thru the whole post, but nonetheless great idea, noble initiative. Allah bada sa'a.