Masoyi kake ko Makiyi
Da farko zan gaya maka cewa wanna reply ya kunshi wasu kalamai da me yiwuwa ka gani kamar cin zurufin ka ko makamancn haka. Na rubutane domin na fahimtar dakai wani abu bada wata manufa ba sai dan gyara. Allah ya baka hakuri idan kaji Haushi kuma yasa wanna ya kawo gyara a yadda muke ganin abubuwa. Allah ne Masani.
Bara a fara tabbatar maka da cewa duk wanda yake ganin ManU za suyi kasa nan bada dadewa ba to baya gani sosai. Abu da yake a fili kiri kiri bawai sai an tsaya ana magana dashi ba. Ina so ka fahimci wasu abubuwa da nake tunani,
Na farko dai kayi maganar cewa kai fans din ManU suna ta cika baki da sauransu kuma duk buge ne da dai sauransu. Anan zan dan yi wasu zato wanda ina fatan zaka gyara min in ba haka bane. Saboda yadda kake magana, zan dauka kai irin hausawannanne wadanda basa tsayawa su duba abu da idan basira kafin su bada martani akan wani abu. Zan dauka cewa kai irin Hasawannanne da basu da ra'ayi duk da cewa kace kai kana son Arsenal babu hujjar da tasa kake son Arsenal. Sannan zan dauka cewa kai irin hausawannanne da basa san gaskiya akan lamarin ball. Bayan lissafa wadannan halaye da nake tunanin kana dasu a dalilin yadda kake magana, zan fara.
Ka sani cewa wadanda kakeji suna son ManU (wato ManU Fans da kake tare dasu kuma suke "cika baki" kamar yadda ka fada. Ka tsaya kai nazari akan ilimin su a kan ManU. Kawai yan kallan ball ne a gidan kallo kuma suyi magana akan kawai kallan ball din ko kuma suna dubawa suga abubuwan da suke faruwa a club din. Watau sun san wani abu akan club din banda abin da suke yi a filin ball. Kaga kwa indai hakane to basu cancanci su juyar da hankalina ba daga gaskiya. Kuma basu cika masu san club dinba.
Kana maganar cewa wai duk wanda yayi sama zaiyi kasa. Wannan ba magana bace ta mutum mai tunani saboda mudai baa gaya mana haka ba a Kurani kuma akwai mutane da organisations da kamfanoni da da koma menene da dama da sukai sama kuma basuyi kasa ba. Wannnan irin karin magana ne na Hausawa da suke jawo asara (failure). Ban ki cewa wata rana ManU zasu bar premiership ba (watau suyi kasa). Wannan abu ne da bamu sani ba kuma bai kamata ma muyi magana akai ba yunda ya zama gaiba kuma Sanin Gaibu sai Allah.
Yadda ManU suke wasa a yanzu kai da ka gani kasan cewa akwai kuruciya a club din kuma sama yake yi kullum.
Ni ban san yadda zan maka bayani sosai ka fahimci raayi na ba amma dai maganar itace kaima kamar yadda kake fada cewa fans din ManU suna ta kuri to kai yunani ka fada min kai me kake yi yanzu. Menen hujjar ka ta fadar haka da zata fitar dakai daga layin masu kuri. Allah ne masani kuma mu abun da muka sani yanzu shine ManU sune suka fi ko wanne club "kyau" a kalla ma dai a cikin Ingila in ba a duniya ba.
Abun da nake so ka dauka daga wanan dogon bayani nawa shine ka yi tunani kafin kayi furuci kuma ka bada hujja mai karfi wadda kai a tunanin ka wani bazai iya kada ta ba. Misali
nace ManU sunfi kowanne club "kyau" a Ingila. Kaga kai baka yadda ba to sai na baka hujja ta wadda nasan cewa baka da damar da zaka kada su. sai ince maka ManU sun ci premiership guda takwas a cikin sha daya ( sai ka fadi wanda nashi yafi haka). ManU sun fi ko wane club a ingila consistency a Champions league (Ba ingila bama kawai wanan duk Europe ne) sai in ce sun ci sau daya a kwanakin baya kuma shekara kamar goma haka suna zuwa a kalla quarter finals (Sai ka fada min wanda yafi haka) Sai ince maka sunfi kowa masoya a duk fadin duniya da Arziki (Sai ka fada min wanda yafi haka) Sai inta lissafo su da dama amma kuma duk gaskiya ne baka da yadda zakai ka karyata wadannaan. ( Nace maka sune a kan gaba a yanzu a premiership din?)
Don Allah Masoyi ayi tunani kafin a ambata zance. Allah ne masani kuma ya taimakemu.