News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

Hausa Films

Started by Anonymous, March 01, 2002, 08:10:53 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 2 Guests are viewing this topic.

Anonymous

Assalamu Alaikum!
Nada de ina kallon film din hausa wanda ake shiryawa a kano da sauran wurare inda hausawa sukai kakagida, amma abun ban mamaki shine har yanzu banga alamar suna cigaba ba sai ma komawa baya ake ko mi yasa? Na sani dayawa mutane zasu ce karya nike amma nafiso mutane su rinka magan objectively domin mu munaso muga sun cigaban domin koba komai ana yada harshen hausa da kuma addinin musulunci. sai anjima.

Anonymous

a gaskiya na yarda da kai da kuma kishin da ka ke da shi game da matsalar fina-filan hausa. wato abin mamaki da kuma ban haushi shine cewa sun kan su masu yin fila-filan ba su san alkiblan su ba. sai kawai su ka zama ya amshin Shatan wasu. Ina dalilin kwaikwayon al'adun wasu marasa ma'ana da kuma cusa su cikin al'adun mu. Dalilan da ya sa na daina sayen su shine saboda ban ga dalinlin da zan sayin abin da basu da ma'ana ba.

Anonymous

A gaskiya na yarda da duk abin da kuka fada akan wasanin kwai kwayoda hausawa mu suke yi          
     ni inna daya daga cikin masu son suyi kalan wasanin hausa   Azato na dauka an dada cigaba fiye da yada nabiri,kamar wasn DANWANZA dasauransu .amma sainaga cewa har wasanin da yafi nayanzu tsari  wake wake mace danamuji ba alada hausa bane saboda haka DONALLAH SU DAI NA NAWAKENAN  WASALAM
                             FROM CHICAGO

Anonymous

Maria Mohammed, naji dadin response dinki domin ya burge ni kuma yayi maana, amma babban abun takaici shine su wadanda muke maganar basu ko damu dasu tuntubi kanoonline ba ballema suga ana sukan su don su himmatu wajen gyara. In ma sun karanta basu bamu amsa ba domin nace ko miyasa basu cigaba, amma har yanzu cikin su masu wasa ko producers ko directors ko kuma uwa-uba ita mujallar fim wadda take yadasu ba wanda yace komai, to ya zaayi muci gaba, ca nake idan mutum yasoke ka sai kakare kanka idan abunda kake yana da maana kamar yadda suke cewa, amma sai sukai shiru kamar matsorata. Wasalam da fatan zas gane abinda muke nufi.

Anonymous

Maria Mohammed, naji dadin response dinki domin ya burge ni kuma yayi maana, amma babban abun takaici shine su wadanda muke maganar basu ko damu dasu tuntubi kanoonline ba ballema suga ana sukan su don su himmatu wajen gyara. In ma sun karanta basu bamu amsa ba domin nace ko miyasa basu cigaba, amma har yanzu cikin su masu wasa ko producers ko directors ko kuma uwa-uba ita mujallar fim wadda take yadasu ba wanda yace komai, to ya zaayi muci gaba, ca nake idan mutum yasoke ka sai kakare kanka idan abunda kake yana da maana kamar yadda suke cewa, amma sai sukai shiru kamar matsorata. Wasalam da fatan zas gane abinda muke nufi.

Anonymous

>:(   Hausa Films have become an embrassment to all Hausas who are devout muslims. They are highly unsophisticated, and discourage creativity in the Society. They send messages of problems existing in the Society without providing adequate solution. Furthermore, they encourage nudity and nothing more! Singing and dancing using indian dancesteps and music tunes is certainly irresponsible, and is a demonstration of the lack of creativity of the film directors, writers and producers.

I personally do not know how to classify Hausa Films. The films seem to be talking only on a very boring subject- Love!    

The Hausa film industry is growing in to a million Naira industry. This so unfortunate, for it is providing income to people are not contributing an iota to the Country's GNP. This is only helping the useless illiterates of our Society to spread the gospel of irresponsibility, indiscipline and bad language. In the end such films would never help in providing stable jobs, for such films would never excite a sophisticated audience. They would certainly be crushed by competition.

Directors of hausa films seem not to have understood the art of film-making. For example, special effects are put at scenes where they do not fit to impress an unsophisticated audience of course! The makers do not realize that those watching movies are not supposed to understand the kind of special effects used at various scenes by watching the movies instantly.

Anonymous

Assalamu Alaikum! da fatan duk kuna nan lafiya a kanoonline. ni magana ta ba a kan lalacewa ko rashin ta na finafinan hausa ba ne, sai dai ni ina so ne in yi magana a kan mujallar ku ta kanoonline.

Ada na dauka anfanin mujallar a website wanda zai iya zama opportunity ga masu internet shine, idan sun bude website din ku za su iya karanta mujallar ba tare da wani wahala ba, amma sai ni ga abin ba haka ba ne ba.

magana ta a nan ita ce, don Allah ku yi kokari ku yi mujallar ku ta zama kamar sauran jaridu na kasa wanda idan ka je website din gamji za ka iya bude duk jaridar da ka ke so ka kuma karanta ta page by page. Don Allah muna rokon haka.

Zancen lalacewar al'ada a cikin finafinai, sai dai a yi ta addu'ar gyara a hankali don abinda suke yi din ma bai baci sosai ba kuma suna kokari matuka gaya don ba kowa ne zai yi abinda suke yi ba. a karshe zan ce ina yi muku ta'aziyyar balaraba, Allah Ya ji kan ta, amin.  

Fulanizzle

Assalamu alaikum.....

Hausa films? please don't mention ::) ::) ::). A friend sent a bunch of hausa films to me. And I just couldn't believe what I saw. They are so unIslamic....and the stories in each movies are almost the same...

And the ?indian-wanna-be ?in the ?movies are just too much.
The girls act with no veil on, and keep dancing in front of the cameras. ?:o
Hausa films aren't promoting good and proper morals to the young, Islamic society. They aren't even showing a good image of the true Northern way of life. ?
Here, many people praise the Northern Nigerians for being good and devote muslims.
But I hide the hausa films now inorder to prevent those people from taking back their words.

sad story,
May Allah help and guide us all.
Ameen.
)

Anonymous

Salama Alaikum yan'uwa!
Agaskiya na yadda da duk abinda kuka fada game da Hausa films.
Amma abinda nakeso kugane shine sai da rarrafe ake tashi.
Kuma zuwana nigeria naga abida wadannan films suka haifar:- Nafarko sonsa anrage kallum foreins films.
Sunyi amfani da Al'adu na hausa sosai, kuda kuwa son taba na india kona turawa, kutunafa komai koyone.
Suna providing entertaiment ga yara harma da manyan, a chikin harshenmu nagado da suturun mu.
Sha'anin chudanya kuwa maza da mata ai duk office din dakaje hakane ko?
So ni inna ganin balaifi saidai dan gyare gyare da yakamata suyi.
Dariya da raha is part of human nature. ? kuma is good in zamu samu chikin harshen mu da al'addun mu.
wassalam

Anonymous

Assalamu alaikum wa rahmatullah
Bayan haka.
Gaisuwa zuwa ga kanoonline da duk masu gudanar da ita da ma masu rubuta koma karanta shafikan da suke cikinta
A gaskiya tsokacin da yawancin ?yanuwa da suka yi akan ?fina-finan hausa? musamman ma dan?uwa ?Aliyu Abdullahi? ya ba ni sha?awa sosai; don haka ne ma na ga ya kamata na dan tofa albarkacin bakina, koda yake kusan duk abin da zan fada ?yanuwa sun riga ni .
Ba shakka  duk wani  abu na duniya zai yi wahala a ce wai alheri ne zallansa, ko sharri ne tsagwaronsa; dole ka ga ya  dan yafuto wani abu daga kowane bangare; ko dai ya dan tsakuro sharrin kadan, ya kamfato alherin da yawa, ko kuma sunkuyan haka.
Fina-finan hausa duk da cewa suna kunshe da ?yan fa?idodin da ba?a rasa ba, amma a gaskiya ni a ganina  ba ta fi cikin cokali ba, in aka kwatanta da gubobi da kuma dodo-dodon sharrin da suke dauke da su, hakannan abubuwan da suka kunsa na  cin-zarafi, da batanci da suke yi wa yaren hausa, hada da al?adun hausawa, da ma duk wani bahaushe ko bahaushiya a bayan kasa.
?Abin mamaki; kare da tallan tsire? Yawancin ?yan wasan fim din nan da masu goya musu baya za ka ji suna ta babatun wai kokari suke yi su yada al?adun hausawa, su kuma burunkasa harshen hausa .
Hakika nakan tausayawa irin masu wannan furuci, domin wanda duk zai yi wannan magana, ko dai bai san su waye hausawa ba, kuma ya al?adunsu suke, kuma wacce hausa ce ?yar halak, wacce ce kuma haihuwar kan hanya ba, ko kuma akukuturu ne kawai; ya ji ana fadar abu ne shi ma sai ya kama maimaitawa, amma shi kansa bai san abin da yake fada ba.
Duk wani dan bahaushiya koda bai zama sha-kundum a hausa ba, ya san cewa masu fina-finan  nan ba wasu al?adun hausawa na a zo-a gani da suke yadawa.
To dauka ma da gaske ne  al?adun hausawan suke yadawa don Allah ga wasu ?yan tambayoyina ina so ?yanuwa su taimake ni da amsoshinsu. Amma saboda gudun tsawaitawa zan takaita akan guda daya kawai
?      Shin wai mu  hausawa  har mun  kai kololuwar ci gaban da yanzu ba abin da ya rage  mana  sai   kona lokacinmu wajen shirya wasan kwaikwayo ko babbaka shi wajen kallonsa?
?      Hausawa nawa ne suka jahilci addininsu kamar yadda suka jahilci ajalinsu?
?      Hausawa nawa ne  har yanzu ko karatu da rubutu ba su iya ba?
?      Hausawa nawa ne suke kwana su wuni ba su da abin da za su ci?
?      Hausawa nawa ne har yanzu suke siyasa ta kudi ba su da wayewar da za su yi ta  mutunci da manufa ?
?      ?Ya?yan Hausawa nawa ne karatu ya gagare su, nawa ne kuma suka shiga sace-sace, nawa ne kuma suka fada zinace-zinace duk galibi saboda talaucin iyayensu?
?      Dadai matsalolin da suka addabi bahaushe wadanda ba sa kirguwa  
To in kuwa haka ne da wane hankalin muka zabi mu mayar da himmarmu  wajen yada al?andun Hausawa  har mu rika alfahari da haka, maimakon mu mayar da hankali wajen  tunanin yadda al?ummarmu za ta ci gaba, cigaban da ba irin na sarkin-baka ba, mu kuma yi kokarin fahimtar da mutanenmu mahimman matsalolinsu hada da ba su maganin da ya dace kuma ta hanyar da ta dace
?      Yanzu dan bahaushen da ya jahilci addininsa,  da duniyarsa,  kai bai ma san inda kansa yake masa ciwo ba, ballantana ya san inda ya dosa a rayuwarsa. da  mai zai cutu idan bai san wasu al?adun hausawa ba. Bayan al?adun ma ba ko wadanne ne masu kyau  da suka cancanci a yayata su ba.
?      Don haka ni ina bai wa ?yanwa masu shirya wadannan fina-finai ya zama wadancan manufofi da makamantansu su ne a gabansu ba wai ya da al?adu ba
?      Don da me za mu amfana in mun yada al?adun maguzanci na bori da bokanci da tsubbu, kari akan al?adun masu bautar saniya (Indayawa) da ballagazai masu bautar kawukansu da soye-soyen zukatansu da suke so kowa ya zama dabba irinsu (Turawa)
      Wassalamu alaikum
       Nura Abdullahi

Anonymous

A gaskiya kamar kun shiga zuciya ta, ni ina da interest a wassan hausa matuka har ma a shekarun baya ina daya daga cikin zakarun wani wasan kwaikwayo eco in the dark, har ma mun taba yin kungiya da tunanin yin film din hausa domin yadawa tun kafin wadannan indiyoyin hausawa su fara.
Sai dai kash sai nazo na yin tafiya ,to amman yanzu duk sati biyu ina kano, don Allah duk wanda shike da sha awa ya iya yi min E mail ko waya 064 666569, domin mu zauna mu tattaauna yadda zamu chanja wannan bakuwar al ada achikin fina finan mu na hausa. ni na yarda in taimaka da lokacina da kuma dan abin da Allah ya hore min
Quote

A gaskiya na yarda da duk abin da kuka fada akan wasanin kwai kwayoda hausawa mu suke yi ? ? ? ? ?
? ? ?ni inna daya daga cikin masu son suyi kalan wasanin hausa ? Azato na dauka an dada cigaba fiye da yada nabiri,kamar wasn DANWANZA dasauransu .amma sainaga cewa har wasanin da yafi nayanzu tsari ?wake wake mace danamuji ba alada hausa bane saboda haka DONALLAH SU DAI NA NAWAKENAN ?WASALAM
? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?FROM CHICAGO

Anonymous

HAUSA MOVIES SUCK!!!!!!! BIIIIIIIIIG TIME!!!!!!  :-[

they're soooo bad!!!! the pic, the cast, the camera angles, the color, the quality, the storyline, the EVERYTHING!!!

they should be illegal  ;D

awwal

Assalamu Alaikum

A gaskiya babu shakka cewa fim din hausa da yanzu a ke yi ya rage wa mutane kallon fim din kasashen waje. To amma abin bakin cikin shi ne cewa wadannan fina-finai na hausa a wasu lokuta da dama maimakon su yada al'adun hausawa sai ma kawar da mutane su ke yi daga kyawawan al'adu na hausawan.

Misali a wasu lokuta irin wakan da suke yi da raye rayen duk sun saba wa al'adun hausawa, a takaice dai ma suna koyi ne da al'adun Indiya ko kuma ma na Turai, wanda ake kokarin guje musu saboda irin munin da suke da shi.

A shekarun baya idan muka dubi irin fina-finan hausa da ake yi wato a lokacin su Kasimu Yaro, Danhaki da dai sauransu, za ka ga cewa lalle suna yada al'adun hausawa. Amma yanzu sai ka ga ana rawa maza da mata, kuma rawanma wadanda suka saba wa al'adun hausawan da kuma ma addinin musulunci. Lalle a gani na wannan abin bakin ciki ne. Lalle akwai bukatan a yi musu gyara.

Maasalam

Anonymous


Anonymous

I agree with all statements made with regard to Huasa Movies. I however do not wish to see it go away. I will most pleasantly like to see it promote our Culture, Language, Religion, Society in general- in good light. Accentuate our hospitality, cultural openness, Civilization, History, our simplistic sophistication etc. Yes  I understand we have vices too, but currently all the movies overly emphasize these vices. It sends out a signal that an anomaly is very present in our culture and society!

Addressing this will preserve our proud culture, the Hausa movie industry and we; Hausawa and non-Hausas, will have pleasant entertainment :-/