News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

Amurka tayi kira a sanyawa Iran takunkumi cikin makwani masu zuwa

Started by bamalli, March 31, 2010, 12:49:38 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

bamalli

Amurka tayi kira a sanyawa Iran takunkumi cikin makwani masu zuwa
 
Shugaba Obama ya ce, yana son ganin an sanya takunkumi masu tsauri kan Iran cikin makonnin dake tafe a maimakon watanni, domin hana ta kera makaman nukliya.
A lokacin da yake tattaunawa a fadar White House tare da shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, shugaban Amurkan ya ce ma'aikatansa na aiki tukuru domin cimma wannan buri.

Shugaba Obama ya ce, akwai wa'adin da suka debar ma kasar, kuma idan ba su ga wata nasara ba zuwa karshen shekarar nan, to zasu yunkura wajen kakabawa Iran takunkumi

A dayan bangaren kuma ,shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Fransa ,ya ce zai yi iyakacin kokarinsa wajen neman goyon bayan abokane kasar sa dake tarayyar turai wajen sanyawa Iran takunkumi masu tsauri.

 

Bashir Ahmad

Above All Fear Allah (S.W.A)