News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

BABBAR NASARA: SIYASAR KANO A HANNUN MALAMAI

Started by Mai Halin Girma, September 12, 2009, 02:50:34 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Mai Halin Girma

BABBAR NASARA: KANO A HANNUN MALAMAI

KANO TA SHA BAM-BAM
Mu kananawa muna kara godiya ga Allah da ya bamu kyakkyawar siyasa a jiharmu karkashin jagorancin shugaba ja gaba Gov. Mal. Ibrahim Shekarau; siyasar da ta hada gwaraza daga kowanne fanni na kwarewar rayuwa: 'yan siyasa, 'yan boko, da kwararrun Malaman addini duk sun yi tarayya a siyasar Kano, wanda hakan shine ya banbanta mu daga siyasar sauran jihohi, kuma hakan shine sirrin nasarar mu. Mun tafka kuskure a baya da muke zaben duk irin dan takarar da aka kawo mana ba tare da mun tantance zurfin ilimin addinin sa, da na duniyar sa, da kuma akidar musulincin sa ba, wanda hakan shi ne ya jefa mu a cikin kangin da muka samu kan mu a baker siyasar mu ta jiya. Amma a yau ma sha'Allah, mun gyara kuskuren mu kuma munga amfanin gyaran namu da muka zabi Mal. Ibrahim Shekarau har karo biyu. Masanin lissafi a ilimin boko, masanin addini kuma mai akidar musulinci da muka zaba har karo biyu ya haifar mana da da mai ido, kuma idon mai gani ba makaho ba. Mal. Shekarau wa'adin sa ya kusa karewa kamar yadda tsarin mulikin kasa ya tanada, wanda hakan yasa muke da bukatar tantance wanda zai ci gaba da jogorantar shugabancin jiharmu mai albarka. Da yake Allah na son bayin sa da alkhari in har suka nema, katsam sai gashi jama'ar kano masu kishin ci gaban addininta da duniyarta suna burin ina ma a tsayar musu da Sheikh Mufti Malam Ibrahim Khalil, malami masanin addini, masanin alkalanci kuma wayayye a siyasar duniya ta yau, a matsayin dan takarar gwamna wanda tuni suka yi mubaya'ar cewa zasu zabe shi a zabe mai zuwa na shekarar 2011 in Allah ya so ya kuma yarda. Wannan fa shi ake kira Kano a hannun Malamai. Kai Allah ya cika mana burin mu na alkhairi ya kuma ci gaba da datar da mu a rayuwar mu, Amin.

'YAN BIYU KYAUTAR ALLAH
Mal. Ibrahim zai tafi Mufti Mal. Ibrahim Khalil zai zo; mai kishi da akida zai tafi mai kishi da akida zai zo; gwarzon Kano zai tafi gwarzon Kano zai zo in Allah ya yarda. Wake da irin tamu? Ku bani amsa babu. 'Yan Biyu Kyautar Allah, ai sai wanda Allan ya zaba. A bakar siyasar Kano ta jiya ba'a tabayin irin su ba, amma muna fatan Allah ya bamu fiye da su anan gaba. Hanya daya da zamu fassara kamalarsu shine muce: "They are Unique in nature and Unique in character". Jihar nan tamu fa ta Musulmai ce. Duk da cewa tsarin siyasar kasarmu na turawan yamma ce da suka kakaba mana, a koda yaushe muna kokarin shigar da manufofin tsarin siyasar musuluncin mu a ciki. A irin hakan nema yasa jama'ar jihar Kano suke gayyatar duk wanda suke yiwa kyakkyawan zato da fata na mulkin adalci da ya zo ya nemi takarar shugabantar su domin su zabe shi ba tare daya nema akan kansa ba. Mutum ya fararwa kansa neman shugabanci bai halarta ba a musulinci matukar ba jama'a ne suka nema masa ba ko suka neme shi da ya fito takara. Wannan masdarin shi ne tsarin siyasar musulinci wanda jama'ar Kano suka bi a lokacin zaben Mal. Ibrahim Shekarau, kuma irin tsarin dai za su bi wajen Mufti Mal. Ibrahim Khalil kamar yadda muke gani tun yanzu ma jama'a na hankoron sa da ya fito su zabe shi a 2011. Kunga kenan 'yan biyu kyautar Allah ba su suka nemi shugabanci a kan kansu ba; a'a jama'a ne suke nema musu ko kuma suke nemar su da su fito takara. Tambaya: waye a cikin 'yan siyasar mu na jiya dama 'yansiyasar sauran jam'iyyu nay au da ya taba bin wannan ka'idar a matsayin sa na musulmi mai kishi? Wannan kalu bale ne a gare su. Mu dai Allah yasa nasarar mu tana cikin shugabancin 'Yan Biyu Kyautar Allah' amin summa amin.

FATAN MU DAYA NE
   Daga farkon Kano ta bangaren arewa zuwa karshen ta ta bangaren kudu, daga farkon Kano ta bangaren gabas zuwa karshen ta ta bangaren yamma, mun ji kuma mun gani a zahiri cewa fatan mu, mafiya yawan jama'a jihar Kano shi ne Allah yasa Mufti Mal. Ibrahim Khalil ya zama shugaban mu a shekarar 2011. Dama idan Allah yaso bayinsa da alkhairi a cikin rayuwar su ta yau da kullum, sai yai ta kimsa musu shawara mai amfani da hikimomi da dabaru masu cike da alkhairi da nasara. Wannan shine misalin  abin da ya faru a lokacin da muka zabi Mal. Shekarau, kuma yake faruwa a wannan lokacin da muke son mu zabi Mufti Mal. Ibrahim Khalil. Ba dabarar mu ba ce ya Allah, hikimar ka ce da ikon ka. Allah yai mana jagora zuwa ga nasara a shekarar 2011. 

KIRA DAYA MURYA DAYA
   Ina fatan ba zan yi laifi ba idan na ce: a bayan hukuntwar Allah, sinadarin nasarar mu a zaben 2011 shi ne 'Kira Daya Murya Daya' (One Voice One Call). Dukkan mai zurfin hikima ya san abin da na ke nufi; ba komai ba ne illa hadin kan Musulmai a wannan tafiya tamu. Mu dalibai na boko da Islamiyyat mu muke da gagarumar gudun mowa a wannan tafiyar. Izala ka ke, Dariqa ka ke, ko Shi'a ka ka ke duk wannan ba shi ne abin tambayar ba ko a gaban Allah; kawai in kai Musulmi ne magana ta kare. Ka da mu rudu da bangarenci mu kwayewa wannan bawan Allan baya in har ya amince da ya tsaya wannan takarar. Kasancewar sa bai ta'allaqa da wani bangare na kungiyayin addini a zahiri ba, ba yana nufin mu mabiya bangarorin Izala, ko Dariqa ko Shi'a mu haramta masa kuri'ar mu ba. Saboda haka ni a gani na in har Mufti Mal. Ibrahim Khalil ya amsa kiran takarar da jama'a su kai masa, to ya kamata mu mabiya bangarori daban daban mu hada kuri'un mu waje daya mu zabi Mal. Khalil a zaben 2011. Manyan malamai na bangarorin addini su taimaka wajen jawo hankalin jama'a zuwa ga wannan hadin kan a zaben 2011. Zaben Mal. Khalili ina ganin shi yafi cancanta da mu zabi wani bare can wanda ba mu san inda ya dosa a addinin ba, kuma bamu san irin kishin sa da gudunmowar da ya ke bawa addinin ba. Hausawa na cewa "ko da me da me akuya tafi kare". Mu musulman kano mu yi hakuri mu ajje bangarancin mu a waje guda a tafiyar mu ta zaben 2011, domin mu hada kai mu zabi Mal. Ibrahim Khalil. Ya san zurfin ilimin Addinni, ya san ilimin zamani, ya san doka da alkalanci, ya san siyasar duniyar ta yau, kuma dadin dadawa ga shi da kishin addininsa da jama'ar jihar kano dama ita kanon kanta. Ni nasan a cikin 'yan takarar da zasu fito a zaben 2011, idan ma har da wanda za'a iya kiran sa cikakken kamili 100% bai wuce Mal. Khalil ba. Ka ga ke nan ido ba mudu ba ya san kima. Don haka kira na anan shi ne duk mai kishin ci gaban addininsa da jihar sa to ya sadaukar da kuri'ar sa ga Mal. Ibrahim Khalil a zaben 2011. Kira Daya Murya Daya, shi ne takenmu. Tuni na yi mubaya'a na ba da kuri'a ta ga Mal. Ibrahim Khalil. Ni fa ba na siyasa amma wannan karan zan fara saboda kishin addinina. Tun da har wanda a ka sanshi cikakken malamin addini wayayye zai fito takara, to ni fa ban ga ta zama ba har sai na ga abin da Allah zai hukunta. Zan ba da dukkan gudunmowa ta musamman ta fuskar rubutu wajen ganin babban Malamin nan ya kai ga nasara.

Tuni na yi mubaya'a na ba da kuri'a ga Mal. Ibrahim Khalil. Allah yai mana jagora wajen zaben shugaba na gari mai adalci, amin summa amin.

                        Submitted by Salimullah

gogannaka

Lallai kam.
Magana karl max daidai.
Religion is the opium of the masses.
Surely after suffering comes enjoyment

Abu-Safwan

could you believe in the words of marx; if the world were to be ruled by true religion of God there will be a greater and faster prosperity.

Muhsin

Quote from: Abu-Safwan on September 28, 2009, 12:19:17 PM
could you believe in the words of marx; if the world were to be ruled by true religion of God there will be a greater and faster prosperity.

Gaskiya ne.

BTW, I don't actually and sincerely welcome Khali's foray into politics. Its a murky water.
Get to know [and remember] Allah in prosperity & He will know  [and remember] you in adversity.