KanoOnline.com Forum

General => General Board => Topic started by: SAAHIB 92 on August 24, 2004, 01:16:31 PM

Title: MENENE MATSALOLIN MALAM BAHAUSHE ???
Post by: SAAHIB 92 on August 24, 2004, 01:16:31 PM
kasancewar al'adun bahaushe sun siffatu da tsarin dabi'u irin na musulnci.sai halayyar bahaushe ta zamanto abin sha'awa da kwaikwayo, wani karon ma abin birgewa da kwatance a wajen ragowar kabilu abokan zaman mu.

sai dai kash!!! a gani na har wa yau bahaushe ya kasa fahimtar ainihin matsalarsa ta fuskar al'amarin rayuwarsa ta yau da kullum.

WAI SHIN MENENE MATSALARMU  NE HAUSAWA :?:

KIDA KO WAKA ?

MARABA DA BAKIN YAN RAWA A TITIN ZOO RD, KO SOYAYYAR 'YAN ZAMANI  :?:

DUK KWARYA TA GARI YA KAMATA TA KOKA....ME YA RAGE A TASKAR MALAM BAHAUSHE YANZU????

allah ya jikan (abubakar imam) da( ibrahim yaro yahaya).
ma'assalam
Title: MENENE MATSALOLIN MALAM BAHAUSHE ???
Post by: mlbash on September 07, 2004, 06:05:50 PM
MATSALOLINNANFA SUNA DA YAWA, ABOKINA, KAI DAI ALLAH YA SAUWAKA!
Title: MENENE MATSALOLIN MALAM BAHAUSHE ???
Post by: Nuruddeen on September 08, 2004, 08:42:33 PM
-Sharholiya
-lalaci
-rashin zuciya
-mutuwar zuciya
dss.
Title: MENENE MATSALOLIN MALAM BAHAUSHE ???
Post by: bakinganga on September 08, 2004, 09:00:43 PM
AI WATO IN GAYA MAKA,BAWANI ABUBANE ILLA SATO WASU AL ADU DABA NAMU BA SHINE KAWAI.[/i][/b]
Title: MENENE MATSALOLIN MALAM BAHAUSHE ???
Post by: alhaji_aminu on September 08, 2004, 11:03:23 PM
Sa'adu zungur ya ce... Bahaushe me ban haushi.
Lawan Dambazau ya ce muna bukatar yakin da lalaci, sakarci, jahilci da iskanci....

I have nothing more to add.
Title: MENENE MATSALOLIN MALAM BAHAUSHE ???
Post by: Eskimo on September 09, 2004, 08:09:07 AM
KADAN DAGA CIKI SUNE NURA DA AMIN SUKA LISSAFAKUMA GASKIYA INA GANIN KAMAR HAR YANZU BA MU SAN CIWON KANMU BA!!!
AMMA KUMA 'MATSALOLIN' DA SHAHIB YA ZANA A SAMA KUWA MATSALOLI NE BA SOLUTION NE BE GA WASU MATSALOLIN NAMU BA???????

MENENE HADIN SOYAYYA KO RAWA A ZOO ROAD GA MATSALAR HAUSAWA????
INA KAFIN BAHAUSHE YACI GABA SAI AN DENA RAWA DA WAKA A ZOO ROAD, AN DENA RUBUTUN SOYAYYA SANNAN. DUK RAN DA AKA DENA SU AN KARAWA BAHAUSHE MATSALA!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!

HEHEHEHE...PPLE CAN BE FUNNY.

:D  :D  :D