KanoOnline.com Forum

General => General Board => Topic started by: Sas on November 20, 2004, 07:53:26 AM

Title: 9/11 Sha Daya ga watan Satumba
Post by: Sas on November 20, 2004, 07:53:26 AM
Salamu Alaikum,

Mutane da dama da nai magana da a Kano basu yarda cewa Usama Bin Laden ne ya hada wannan hari a WTC ba. Ko kadan bani da wasiwasi a zuciyata cewa Osama ne ya hada wannan hari.

Amma kuma sai gashi naga a cikin amurkan kanta wasu suna tunanin ba hakan bane. Kuma da nai tunanni sai naga cewa, lallai hakane, duk da yake ban tashi daga bakana na cewa Osama ne ya hada harin ba, maganganun da wadannan mutane suka fada (turawa yan asalin amurka) ya sa nayi tunani kadan.

Sun ce ai ba makawa Bush ne ya hada wannan hari da kansa ba laifin wani Osama. Na dakata anan tukunna...Na baku dama kuyi tunani akai tukunna

Bissalam