KanoOnline.com Forum

General => General Board => Topic started by: Sas on November 20, 2004, 07:59:08 AM

Title: manyan makarantun Duniya???
Post by: Sas on November 20, 2004, 07:59:08 AM
Salamu Alaikum,

Dan Allah inada tambaya amma inaso idan ka/kin bada amsa ki/ka fadi a inda kake in da hali. Inaso naga a cikin wadannan makarantun, CAMBRIDGE, OXFORD, HARVARD, MIT, YALE, CALTECH, etc wacce ce tafi suna a duniyar ka/ki?

Nasan misali wadanda suke a amurka (yan asalin amurka) kwata kwata bama su san wasu makaranta CAMBRIDGE ko OXFORD ba so dole su zabi HARVARD, MIT... a saman su.

Ku sani cewa bawai ina tambayar wacce makaranta ce tafi ba. Kawai waccece tafi suna.

Misali. Da wanda yace maka a Harvard ko Oxford yazo, wannene yafi kima a gurinka.

Bissalam