KanoOnline.com Forum

General => Islam => Topic started by: hashms on February 22, 2005, 08:16:10 PM

Title: KIN FADIN GASKIYA DON GUDUN MATSIN MASU MULKI DA MATSAYI.
Post by: hashms on February 22, 2005, 08:16:10 PM
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Hausawa na cewa: RAYUWAR DUNIYA TSUNTSUWA CE, TA KAN TASHI YAU DAGA WANI TA SAUKA A KAN WANI, kuma suna cewa: KOMAI NISAN JIFA, KASA ZAI DAWO. Hakika sun yi gaskiya, duk inda mutum ya kai ga matsayinsa, wata rana zai wayi gari, in ba a nan Duniya ba, to a gidan gaskiya, babu wani matsayi, sai abinda ya aikata zai tarar, haka kuma idan ya kasance yana gadara da ikon da Allah Ya bashi ne, idan ya yi ba dai-dai ba, ya hana a fada masa gaskiya, to, akwai dai ranar kin dillanci, wato ranar da hajar mai gari ta bace. Ita gaskiya, ya 'yan'uwana samari, daya kawai take, kuma ku yi hakuri, idan bata bayyana ba yau, to ku saurari bayyanarta gobe. Na gode da samun wannan 'yar gajeruwar damar, Allah Ya sadamu a wani jikon, amin.
Title: Re: KIN FADIN GASKIYA DON GUDUN MATSIN MASU MULKI DA MATSAYI
Post by: mlbash on April 04, 2005, 10:38:02 AM
Quote from: "hashms"Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Hausawa na cewa: RAYUWAR DUNIYA TSUNTSUWA CE, TA KAN TASHI YAU DAGA WANI TA SAUKA A KAN WANI, kuma suna cewa: KOMAI NISAN JIFA, KASA ZAI DAWO. Hakika sun yi gaskiya, duk inda mutum ya kai ga matsayinsa, wata rana zai wayi gari, in ba a nan Duniya ba, to a gidan gaskiya, babu wani matsayi, sai abinda ya aikata zai tarar, haka kuma idan ya kasance yana gadara da ikon da Allah Ya bashi ne, idan ya yi ba dai-dai ba, ya hana a fada masa gaskiya, to, akwai dai ranar kin dillanci, wato ranar da hajar mai gari ta bace. Ita gaskiya, ya 'yan'uwana samari, daya kawai take, kuma ku yi hakuri, idan bata bayyana ba yau, to ku saurari bayyanarta gobe. Na gode da samun wannan 'yar gajeruwar damar, Allah Ya sadamu a wani jikon, amin.

waalaikumussalam warahmatullah wabarakatuh.

sannu malam da wannan nasiha taka, Allah yasa wadanda akayi dansu suyi amfani da shi, tare da mu baki daya.