KanoOnline.com Forum

Member Showcase => chit-chat => Topic started by: kinta kunte on April 17, 2005, 11:20:16 AM

Title: Pyade
Post by: kinta kunte on April 17, 2005, 11:20:16 AM
Kwanaki kadan da suka wuce, an samu wani mummunan labari daga jihar Kano.Wai an kama wasu maza su biyu (kattai),sun dauki wata yarinyar me kemanin shekara uku da haihuwa,sun mata pyade(wato saduwa ta karfi).A dalilin haka ta rasu.Bugu da kari kuma Musulmai ne.Nayi matukar bakin ciki da jin wannan labari.

  Yanzu dan Allah dan annabi,yaya za'a yi ace kana musulmi,ka dauki yar shekara 3 ka sadu da ita.Wace irin zuciya ce da kai?Menene yake damun kwakwalwar ka da zaka aikata wanna bakin aiki.Ko kafiri ai bana jin zai yi haka.A gaskiya namiji bai kyauta.Ya kamata mu dinga duba kuma muna tunani.Kada a manta akwai Ubangiji.Ranar sakayya za ta zo kuma.
Title: Pyade
Post by: Anonymous on April 18, 2005, 11:47:57 AM
Subhanallahi
Title: Pyade
Post by: gogannaka on April 28, 2005, 08:29:26 PM
A sad news indeed.