Assalam,
ina da tambaya, shin ko akwai wanda zai fayyace min banbancin da kuma fassara wadannan kalmomi kamar haka.
a-hurwa
b-ahu
c-nunkufurci
d-babakere
e-nukusani
banbance tsakanin wadannan-
fundum,tsundum,tsulum
sharhi-mai arziki ko a kwara ya sai da ruwa,komai nisan jifa kasa zai fado,komai nisan dare gari zai waye.
if you win i will dash you my silver tooth :lol:
[/b]
Though i dont want the silver tooth,rather if u have gold one.
a-hurwa,shine mutum ya fadi a kasa don neman wani abu a wajen wani yan dungurar kasa,musamman wajen tuba,wannna yafi faruwa wurin yarbawa,kuma an fi yiwa wani mai sarauta.
b-ahu, :?
c-nunkufunci
d-babakere,mutum yayi kane-kane kan abu ya hana kowa samu shine yayi babakere
e-nukusanci,is like a form of roko da wasu kanyi wa manyan mutane
difference between fundum,tsundum,tsulum
fundum-----no idea
tsundum----in ka fada cikin ruwa mai yawa za a ce ya fada tsundum
tsulum------opp of tsundum may be ruwan ba yawea ko wanda ya fada bashi da nauyi sai ace yayi tsulum
Sharhi----mai arziki ko a kwara ya saida ruwa,most of the time ana amfani da kwara a matsayin wuri da yake dauke da ruwa mai yawa don haka in mutum yazo wurin ba zai gwada musu maganar ruwa ba,ana amafani da hakan a nuna if you are successful no matter what you will continue to remain so.
komai nisan jifa kasa zai fado-----kowa ya san in anyi jifa to komai nisan sa zai dawo kasa ya fadi,don haka whatever you are doing one day you have to come to the end
komai nisan dare.....same as above
Ithink i will be accorded with the title of ....hausa :D
ahu - wani kudi ne da ake amfani da shi a da
nunkufurci - ana amfani da wannan kalma don a bayyana mutun mai riko a zuci. wato wanda bai da saurin mantuwa ko yafewa in an yi masa laifi.