'Yan wasan Hausa Na wannan karni sufara kaucewa dokoki da kaido jin wansan hausa Mu sammamma Al'adum Hausawa, Yaza a yi a ciyo kansu
a kuma dorasu su daidaitu kan al Adummu na hausawa?
Gaskiyar ka, amma ni yadda na dauka lokaci ne, kuma zai wuce da sannu za a zo lokacin da za su canja su koma yin irin wanda kake ganin shine daidai, don da haka ci gaban wasan kwaikwayo ke farawa a ko ina.
Ina nufin yana farawa ne daga kwaikwayon wasu.
Quote from: "salizone"Gaskiyar ka, amma ni yadda na dauka lokaci ne, kuma zai wuce da sannu za a zo lokacin da za su canja su koma yin irin wanda kake ganin shine daidai, don da haka ci gaban wasan kwaikwayo ke farawa a ko ina.
Ina nufin yana farawa ne daga kwaikwayon wasu.
gaskiya ban yarda da kai ba. domin kuwa daga yadda take taken su yake gamai hankali da hangen nesa, wallahi kiris suke jira su fada ramin kura! ina fata ka gane inda na nufa. ina ganin lailai ne gwamnati ta kara dagewa ka kula da tsarin hausa fim kafin lokaci ya kure mana. domin kuwa idan mu mun tsira, tofa kannanmu da 'ya'yenmu na tasowa!
ALLAH ya shirye mu.
A gaskiya dai a duba a gani domin yadda abubuwa suke kasancewa game da yana yin fina-finan hausa abin sai dai addu`a kuma gaskiya batun wai zasu daina (lokaci ne) bai ma taso ba, domin in aka yi la`akari da yadda indiyawa suka soma to za ka tarar cewa lallai in ba an dauki matakai ba to lallai wataran za muyi da na sani, domin tarihi ya nuna cewa farkon fara fina-finan indiya, kusan ba a samun mace ta zama jarima, sai dai ayi wa namiji kwalliyar mata ya rika acting kamar mace saboda tsabar al`ada da kunya irin tasu amma sannu a hankali sai gashi yau indiyan fim ya zama tamkar fin din America. saboda haka muyi hattara, domin hausawa sun ce tafi dai Guga................
duba min hanya abokina!
kafin kurinka fadin irin wadannan kalmomi yakamata ku shiga cikin masu wannan wasanni kuyi nazari :twisted:
Assalam Alaikum!
Ni a gani na komai na bukatar lokaci, domin kuwa idan ka yi la'akari da samuwar fina-finan Hausa za ka ga abin jariri ne, idan ka kwatanta shi da suaran wasu abubuwa na Adabi. Kuma shawara a nan ina ganin ya kamata a shiga wannan harka ta fina-finai a santa ciki da waje, sannan a gano inda ta yi gibi, to unsha allahu wata rana za su dace da rayuwar Hausawa.
Ma'assalam.
Jama'a jinku nake kurum ko kuwa karanta ku nake kurum. Ina ga wa'yanda suke cewa ayi hattara in ba hakaba al'a dun mu na hausa za su bace? Abin da nake so in janyo hankalin marubuta shine, abin da 'yan wasan kwaikwayo ke yi ba wani abu bane illa kwaikwayar yadda zamani ya kasan ce. Duk abinda suke nuna wa abin da ake aikatawane a yanzu. Ba su suke canza al'adar Hausawaba, kuma ba su za su can za taba. Abin da suke gani a nayi a cikin alumma shi su ke kwaikwaya suna fito da shi fili. Shi yasa a ke kiran su 'yan wasan kwaikwayo.
Misali, yawanci ana sukar 'yammatan wasan kwaikwayo da rashin saka kayan da muka gada a aladance. Watau suna sa kananan kaya- dogon wando da t shirt ko makaman tansu. Yanzu ina ce duk yara yaran 'yammatan yanzu ba haka suke dressing ba? In ka ga yarinya ba tayi ba, to batada halin yi ne, kokuwa gidan su a tsakiyar cikin birni Kano yake inda baza ta samin sukunin yin haka ta fita ba. Amma ba abin da ke hana ta a cikin gidan iyayen ta. Kuma sanin kowa ne cewa su 'yammantan masu yin wasan kwaikwayon basu su ka fito da al'adar sa kananan kaya ba. Do min na san cewa a wani lokacin ma, in sun tafi yin film musamman ma in a gidajen mutane ne (watau private residence) har aron kayan sawa ake basu don suyi fim din. Ni wannan na gani da ido na.
Na biyu kuma duk akan kaya. Yanzu yan mata nawa ne ke lullubi in za su fita? Ba wani dan karamin gyale ake yafawa a ka ba yana yi yana zame wa yana nuna adon gashin yarinya ita kuma ta na dan karkata shi wai ita tana gyara lullubi? 'Yan wasan Hausa ne suka bullo de wannan yayin? Ina Stella Obasanjo? Style din riguna da sukayi tashe a 'yan shekarun da suka shige. Tabbas ana ganin 'yan wasan kwaikwayo suna sa irin wannan sitturar amma ba su suka kirkiro da style din stella obasanjo ba.
In kuma ana batun soyayya fa? E to, ba a ganin mace da namiji suna rawa kamar yadda ake nunawa a fim din Hausa, amma kuma ko ni nan lokacin ina daliba a BUK, naje irin liyafar nan da ke shiryawa watau night parties. A wurin akwai mata da maza a hade. Kuma anayin raye rayen disco da makaman tan su. Saboda haka ba'a ce wai 'yan wasan kwaikwayo ne za su canza mana al'adu ba. Sun riga sun fara canzawa, tun shekaru aru aru.
Bayan da haka da mu Hausawa bamu nuna matukar mugun sha'awar finafinan Indiya ba, su 'yan wasan hausan baza su kwaikwaye su har mu kuma muzo muna korafi wai za a canza mana aladu. In mun san abinda 'yan fim din Indian suke yi bashi da kyau, me yasa muka rika kallon finafinan nasu? Har dan azabar lakance indian films wa'yansu ma da basu taba zuwa India ba sun fahimci harshen Hindi abakin su kamar jakunan Calcutta ko Mumbai ;D.
Dan Allah a ruka sara a na duban bakin gatari. Ba ruwan 'yan finafinan hausa da gurbata al adun Hausawa, Kwaikwayo kurum suke yi kamar yadda lakanin nasu yake.
Lallai kuwa Babbar Malama ta gama zancen gaba
daya a dunkule.
Abin da zamu ce shine, kowa ya fara gyara daga
kansa da iyalinsa.
Assalamu Alaikum,
A gaskiya na ji dadin bayaninki HUSNAA kwarai da gaske, Allah ya saka da alheri, Allah kuma ya sa 'yan uwa su gane.Domin kuwa abin da kika fada gaskiua ne, ba 'yan wasan Hausa ba ne suke bata tarbiyyar 'ya'yan Hausawa ba, su dai suna nuni da irin abubuwan da suke faruwa ne a zamani, domin a yi hattara
Ashe daman akwai JAKIN MUMBAI ;D, wallahi ban taba ji ba sai a wajenenki
Ma'assalam
Quote from: HUSNAA on March 14, 2007, 01:24:07 PM
Misali, yawanci ana sukar 'yammatan wasan kwaikwayo da rashin saka kayan da muka gada a aladance. Watau suna sa kananan kaya- dogon wando da t shirt ko makaman tansu. Yanzu ina ce duk yara yaran 'yammatan yanzu ba haka suke dressing ba? In ka ga yarinya ba tayi ba, to batada halin yi ne, kokuwa gidan su a tsakiyar cikin birni Kano yake inda baza ta samin sukunin yin haka ta fita ba. Amma ba abin da ke hana ta a cikin gidan iyayen ta. Kuma sanin kowa ne cewa su 'yammantan masu yin wasan kwaikwayon basu su ka fito da al'adar sa kananan kaya ba. Do min na san cewa a wani lokacin ma, in sun tafi yin film musamman ma in a gidajen mutane ne (watau private residence) har aron kayan sawa ake basu don suyi fim din. Ni wannan na gani da ido na.
Na biyu kuma duk akan kaya. Yanzu yan mata nawa ne ke lullubi in za su fita? Ba wani dan karamin gyale ake yafawa a ka ba yana yi yana zame wa yana nuna adon gashin yarinya ita kuma ta na dan karkata shi wai ita tana gyara lullubi? 'Yan wasan Hausa ne suka bullo de wannan yayin? Ina Stella Obasanjo? Style din riguna da sukayi tashe a 'yan shekarun da suka shige. Tabbas ana ganin 'yan wasan kwaikwayo suna sa irin wannan sitturar amma ba su suka kirkiro da style din stella obasanjo ba.
Wallahi kin fadi gaskiya. Yan wassan hausa kawai reflecting abin da
ke faruwa a society suke yi. Ba ruwansu da kikiro abubuwan da ake
laka masu. Kuma mutanen da suke zagin yan film idan an bincika irin
abubuwan da suke yi ya fi haka baci ma...
Allah dai ya shirya gabaki daya.
Quote from: HUSNAA on March 14, 2007, 01:24:07 PM
Jama'a jinku nake kurum ko kuwa karanta ku nake kurum. Ina ga wa'yanda suke cewa ayi hattara in ba hakaba al'a dun mu na hausa za su bace? Abin da nake so in janyo hankalin marubuta shine, abin da 'yan wasan kwaikwayo ke yi ba wani abu bane illa kwaikwayar yadda zamani ya kasan ce. Duk abinda suke nuna wa abin da ake aikatawane a yanzu. Ba su suke canza al'adar Hausawaba, kuma ba su za su can za taba. Abin da suke gani a nayi a cikin alumma shi su ke kwaikwaya suna fito da shi fili. Shi yasa a ke kiran su 'yan wasan kwaikwayo.
Misali, yawanci ana sukar 'yammatan wasan kwaikwayo da rashin saka kayan da muka gada a aladance. Watau suna sa kananan kaya- dogon wando da t shirt ko makaman tansu. Yanzu ina ce duk yara yaran 'yammatan yanzu ba haka suke dressing ba? In ka ga yarinya ba tayi ba, to batada halin yi ne, kokuwa gidan su a tsakiyar cikin birni Kano yake inda baza ta samin sukunin yin haka ta fita ba. Amma ba abin da ke hana ta a cikin gidan iyayen ta. Kuma sanin kowa ne cewa su 'yammantan masu yin wasan kwaikwayon basu su ka fito da al'adar sa kananan kaya ba. Do min na san cewa a wani lokacin ma, in sun tafi yin film musamman ma in a gidajen mutane ne (watau private residence) har aron kayan sawa ake basu don suyi fim din. Ni wannan na gani da ido na.
Na biyu kuma duk akan kaya. Yanzu yan mata nawa ne ke lullubi in za su fita? Ba wani dan karamin gyale ake yafawa a ka ba yana yi yana zame wa yana nuna adon gashin yarinya ita kuma ta na dan karkata shi wai ita tana gyara lullubi? 'Yan wasan Hausa ne suka bullo de wannan yayin? Ina Stella Obasanjo? Style din riguna da sukayi tashe a 'yan shekarun da suka shige. Tabbas ana ganin 'yan wasan kwaikwayo suna sa irin wannan sitturar amma ba su suka kirkiro da style din stella obasanjo ba.
In kuma ana batun soyayya fa? E to, ba a ganin mace da namiji suna rawa kamar yadda ake nunawa a fim din Hausa, amma kuma ko ni nan lokacin ina daliba a BUK, naje irin liyafar nan da ke shiryawa watau night parties. A wurin akwai mata da maza a hade. Kuma anayin raye rayen disco da makaman tan su. Saboda haka ba'a ce wai 'yan wasan kwaikwayo ne za su canza mana al'adu ba. Sun riga sun fara canzawa, tun shekaru aru aru.
Bayan da haka da mu Hausawa bamu nuna matukar mugun sha'awar finafinan Indiya ba, su 'yan wasan hausan baza su kwaikwaye su har mu kuma muzo muna korafi wai za a canza mana aladu. In mun san abinda 'yan fim din Indian suke yi bashi da kyau, me yasa muka rika kallon finafinan nasu? Har dan azabar lakance indian films wa'yansu ma da basu taba zuwa India ba sun fahimci harshen Hindi abakin su kamar jakunan Calcutta ko Mumbai ;D.
Dan Allah a ruka sara a na duban bakin gatari. Ba ruwan 'yan finafinan hausa da gurbata al adun Hausawa, Kwaikwayo kurum suke yi kamar yadda lakanin nasu yake.
Kai, amma naji dadin wannan bayani naki. Wallahi a duk lokacin da nake kokarin kare 'yan fim a kan zargin suna bata al'adar hausa ina kawo wasu dalilai irin nawa, amma ban taba tunanin wannan ba. Ni dai abin da na sani shine dama can al'adar mu ta dauko lalacewa tun gabannin fara wasannin hausa. Kuma in ma ance a daina kallon wasan hausa, ai dai yawancin mutane yanzu suna da satelites a gidajen su. To ana nufin kallon American films da Indian Films da Nollywood yafi alheri, tun da dai ba za'a iya hana mutane kallon film ba gaba daya?
Na yarda akwai gyare-gyare a harkar fim din hausa, kuma ya kamata a dau matakin gyara, amma cewar su ke bata al'adar mu ba'a yi musu adalci ba.
Ai dama husnaa ta iya bayani da bada amsa mai kyau. ;)
Amira u r 2 kind........thanks for the flattering comment ;D ;D ;D
to ai gaskiya ne malama husnaa :D
Quote from: Sirajo Ibrahim on June 08, 2005, 08:51:07 PM
'Yan wasan Hausa Na wannan karni sufara kaucewa dokoki da kaido jin wansan hausa Mu sammamma Al'adum Hausawa, Yaza a yi a ciyo kansu
a kuma dorasu su daidaitu kan al Adummu na hausawa?
ni a ganina ya kamata ayi ta addu'a allah ya shiryemu gaba daya. kuma matakin da gwamnatin kano ta dauka a kansu yayi kadan. abin da ya faru ya riga ya faru.Allah ya kiyaye mu da aikin da na sani.ameen
A halin yanzu kam, da alamar abin bai karbe mu ba, kamar likita a godiya, kaman sirdi akan kare!.........
to nasake dawowa malama husna kinyi kokari alasa kar ace kema yar wasan hausace domin kinfadi gaskiya irin wadda komai hassadar mutum bazai kawo wasu dalilai daza ayarda akan cewa wai yan wasan kwaikwayone suke bata tarbiyar yara mutundai yakula da tarbiyar yaransa tun daga gida alasa mudace amin
[/i] :-X[/color]
Mallam Nura na gode. Ai koma an ce ni 'yar wasar Hausa ce ai ba laifi akayi ba, tunda ba duk a taru a ka lalace ba. Kuma ma in an tashi kwatantani, ba za a sani a cikin 'yan yara yaran ba da suke tashe yanzu. Za a tunkuda ni layin su Kasimu Yero ne, watau retired tsofaffi, saboda haka ba aibu. ;D
Can ma, nan ma? Kai, wasan hausa ya... ;D
Quote from: Muhsin on August 25, 2007, 11:38:45 AM
Can ma, nan ma? Kai, wasan hausa ya... ;D
Ai kuwa this hausa fim is everywhere ;D
Hakane amira. Amma kam ai abu ya dagule musu fa! :o
Wannan zamani....a kawai problems.
Quote from: HUSNAA on August 23, 2007, 05:29:54 AM
Mallam Nura na gode. Ai koma an ce ni 'yar wasar Hausa ce ai ba laifi akayi ba, tunda ba duk a taru a ka lalace ba. Kuma ma in an tashi kwatantani, ba za a sani a cikin 'yan yara yaran ba da suke tashe yanzu. Za a tunkuda ni layin su Kasimu Yero ne, watau retired tsofaffi, saboda haka ba aibu. ;D
Gaskiya ne Husna. Akwai wasan hausa wanda yana da kyau da kayatarwa. Misali, Samanja mazan fama, Jauro Dan Fulani, Cokali da Karkuzu. They promote our cultures but today's own, NO COMMENT my dear.
Quote from: amira on September 28, 2007, 09:44:20 PM
Wannan zamani....a kawai problems.
Bundles of problems Amira. We have succeeded in creating more problems and troubles for ourselves than solutions. Hausa society is now turning into something else. These Hausa Dramatists NA WA WO!!!
Gaskiya kam ya kamat a duba a gani. A yanzu dai ya kamata tunda an ce anai wa komai doka, to wadanda Allah I ba wannan damar su duba su yi dokar da ta dace. Ai muna da al'adu, a bi su man. Sannan a karantar da su masu wasan kamar yadda Sinaw (Chanis) su kan yi. Duk abin da su ke lallai akwai makaranta da kan koyar da shi bisa dokokin qasar su bisa al'adun su.
Da kwai wani fim da na gani, rigar da dan wasan i sa irin ta shiga yanayin qanqara (winter) ce, qila ya saye ta a gwanjo. Sai ga wandon kuma na yanayin zafi (summer). Yarinyar da ke tare da shi ta sa qananan kaya kuma suna wajen da ke da hasken rana ainun,da alamun zafin ranar kuma suna rawa! Haba jama'a! Alamun rashin yawo da rashin wayewar kan ta fito qarara a wannan fim.
Allah kyauta.
Quote from: Sani Danbaffa on July 06, 2011, 01:02:17 AM
Da kwai wani fim da na gani, rigar da dan wasan i sa irin ta shiga yanayin qanqara (winter) ce, qila ya saye ta a gwanjo. Sai ga wandon kuma na yanayin zafi (summer). Yarinyar da ke tare da shi ta sa qananan kaya kuma suna wajen da ke da hasken rana ainun,da alamun zafin ranar kuma suna rawa! Haba jama'a! Alamun rashin yawo da rashin wayewar kan ta fito qarara a wannan fim.
Allah kyauta.
Har ka bani dariya ;D Toh, dama ai irin matsalar da ta jawo abin ya rage armashi kenan. Suna yin abu ne yanzu ba basira, ba tunani, ba hankali. allah ya kyauta.
A gani na, yana daga dalilan da suke hana masu shirya fina finan Hausa nuna al'adu tsantsa, musamman tsofaffin al'adu, rashin isassun kudi.
Galibin lokuta, idan zasu nuna zallar al'adar Bahaushe to sai sun dinka sababbin tufafi, su Gina sabin gidaje ko kuma su yiwa wadansu gidajen kwaskwarima. A bangare guda kuma, idan sun sha wahala sun gama yin wannan aiki, sai wadansu su sace suyi ta bugawa suna sayarwa ba bisa yardar mashiryan fim din ba.
Saboda haka, ina gani hanyoyi guda uku zasu magance wannan matsala ko su rageta: 1. Gwamnatoti da 'yan kasuwa su rika sanya jari 2. Ayi kokarin magance matsalar satar fasaha 3. Masana al'adu na jami'o'i su rika jawo su a jiki suna yi musu gyara maimakon nesanta daga gare su da suke da kuma sukar su.