KanoOnline.com Forum

General => General Board => Topic started by: Bajoga on November 23, 2007, 05:23:29 PM

Title: Away From The Forum!!!
Post by: Bajoga on November 23, 2007, 05:23:29 PM
Assalamu Alaikum!!!

Ina so inyi amfani da wannan dama don neman gafara ga duk wanda na batawa either knowngly or unknowngly. Wannan ya faru ne sakamakon shirin tafiya Saudi (Hajji) da nakeyi a yanzu (Kuma hakan nema ya kamata ga dukkan musulmi), kuma i believe za'a iya neman mu a kowane time, kuma may be bazan samu damar yin bankwana ga members ba, that is why i decided to post this topic a matsayi neman afuwa da kuma bankwana.

A bangarena, ni har ga Allah na yafewa duk wanda ya bata mini kuma ina rokon nima a yafemin duk abubuwan da nayi ko ta fannin rubuto ko dai wani abu, Allah kuma ya yafe mana duka.

I will be keep visiting this memorable forum till lokacin da aka nememu don tafiya. Saboda haka in anji shiru dai, tooo................

Daga karshe ina yiwa dukkan members na wannan forum godiya da irin yadda kowa yake bada irin tasa gudun muwa don ciyar da majalisar gaba. Allah ya taimake mu baki daya, amin

In mun dawo Allah ya sada mu da alkairinsa, in kuma Allah ya dauki rayukan mu, to Ubangiji ya sadamu a gidan Aljanna.

Wassalamu Alaikum!
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: Dan-Borno on November 23, 2007, 05:32:08 PM
Addu'a ta farko da muke so in ka sauka lafiya
itace Allah ya sa duk yan forum dinnan Allah ya
kira su zuwa hajji na badi.

Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo da kai cikin
iyalanka lafiya.
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: Bajoga on November 23, 2007, 05:44:48 PM
Quote from: Dan-Borno on November 23, 2007, 05:32:08 PM
Addu'a ta farko da muke so in ka sauka lafiya
itace Allah ya sa duk yan forum dinnan Allah ya
kira su zuwa hajji na badi.

Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo da kai cikin
iyalanka lafiya.

I will try my possible best in sha Allah don yin addu'a ga dukkan memers na wannan forum din.

Thanks you very much.
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: gogannaka on November 23, 2007, 11:23:17 PM
Bajoga Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo da ku lafiya.

Kada ka manta ka yi wa dukkannin iyaye, yanuwa da abokan arziki addu'a.
Allah ya sa kayi hajjin a sa'a.Allah ya karba.


Ka yiwo wa Dan-borno sautun charbi da jallabiya.
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: HUSNAA on November 24, 2007, 03:45:07 AM
Allah Ya kai ka lafiya Ya sa Hajjin karbarbiya ce. Bayan yi wa iyaye da 'yan uwa addu'a, mu ma anan forum, kada a manta da mu. A samu a addu'oin. Duk mai bukata, Allah Ya biya masa ameen. Kuma Allah Ya gama mu gabadaya 'yan forum a aljannatul fir dausi  bi'iznillah (we can hold a similar forum there!!!! ;D ;D ;D)
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: Bayya on November 24, 2007, 07:02:26 AM
Allay ya kaika lafiya ya dawo dai kai lafiya.
Ayi mana addu'a Allah yasa mu dace, ya
gyara kasar mu, ya kuma taimaki musulmi
da musulunci amin.
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: amira on November 25, 2007, 12:20:47 AM
Ameen Wa'alaikumus Salam Bagoja
Allah kaiku lafiya kuma ayi ibada a sa'a, katina damu a cikin adduar ka, Allah taimake kasar mu da sauran musulmai Ameen.
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: manasmusa on November 26, 2007, 10:57:51 AM
Allah ya kiyaye hanya and hope Za'a samu a cikin addu'a in particular and the forum at large. may Allah(s.w.t) accept our ibadah. Allah ya ciyar da wannan dandali gaba ya kuma hada fuskokinmu wata ran. Ameen
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: Muhsin on November 26, 2007, 12:20:57 PM
Bajoga,

Allah yasa aje lafiya a dawo lafiya--Amin.
Two wishes:
          1-Allah ya bawa marasa damar zuwa a wannan shekarar suje wata, kamar         
             ni.
           2-Allah yasa Bajoga ba zai manta da tsarabar Kanoonliners ba.
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: sdanyaro on November 26, 2007, 02:15:48 PM
Bajoga

Allah ya kaiku ya dawo mana da ku lafiya. Allah ya sa ayi a sa'a. Amin summa Amin.
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: Rais on November 26, 2007, 02:47:28 PM
Quote from: Dan-Borno on November 23, 2007, 05:32:08 PM
Addu'a ta farko da muke so in ka sauka lafiya
itace Allah ya sa duk yan forum dinnan Allah ya
kira su zuwa hajji na badi.

Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo da kai cikin
iyalanka lafiya.
amin dan Barno Zan yi amfani da wannan damar ga Bagoja da yai min addua a dakin Allah domin ya yayemin wani irin ciwo danai fama dashi mai bantsoro sannan ya yayewa muslim ummah baki daya .Sannan ina baran addua ga dukkan yan uwa yan forum Nagode!!!!!!
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: MySeLf on November 26, 2007, 06:06:08 PM
Bajoga Allah ya kaiku lafiya yasa ayi hajji karbabbiya!


Quote from: Rais on November 26, 2007, 02:47:28 PM
Zan yi amfani da wannan damar ga Bagoja da yai min addua a dakin Allah domin ya yayemin wani irin ciwo danai fama dashi mai bantsoro sannan ya yayewa muslim ummah baki daya .Sannan ina baran addua ga dukkan yan uwa yan forum Nagode!!!!!!

Kash! Sorry to hear that Rais...... Ubangiji Allah ya sawake, yabaka lafiya cikin sauri...

Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: Bajoga on November 26, 2007, 07:38:07 PM
Quote from: Rais on November 26, 2007, 02:47:28 PM
Quote from: Dan-Borno on November 23, 2007, 05:32:08 PM
Addu'a ta farko da muke so in ka sauka lafiya
itace Allah ya sa duk yan forum dinnan Allah ya
kira su zuwa hajji na badi.

Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo da kai cikin
iyalanka lafiya.
amin dan Barno Zan yi amfani da wannan damar ga Bagoja da yai min addua a dakin Allah domin ya yayemin wani irin ciwo danai fama dashi mai bantsoro sannan ya yayewa muslim ummah baki daya .Sannan ina baran addua ga dukkan yan uwa yan forum Nagode!!!!!!

:) I will in sha Allah try my possible best don ganin idar da sakonka.


Ga sauran members kuma, nan in Allah ya yadda zan gabatar da irin sakon yan'uwa da abokan arziki.

Kuma gaskiya naji dadi kwarai da irin yadda members suka rika min addu'a da fatan alkairi akan wannan tafiyar ibada da muke da niyyar yi.

Daga yau, in sha Allah na tafi sai kuma in mun dawo (da iznin ubangiji)

Allah ya sake sadamu da alkairi.
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: hafiz amin umar on November 27, 2007, 05:16:57 PM
ALHAMDU LILLAH,addua'u saiful mumin inji annanbi,ALLAH yasa karbabbiyace.
Title: Re: Away From The Forum!!!
Post by: IBB on November 27, 2007, 07:50:30 PM
Allah dawo da kai lafiya Allah kuma yasa Hajjin karbabbiyace Ameen. To all the prayers members have posted Ameen