KanoOnline.com Forum

Member Showcase => chit-chat => Topic started by: waduz on January 30, 2009, 10:18:56 AM

Title: MEANING AND USE OF HAUSA PROVERBS:
Post by: waduz on January 30, 2009, 10:18:56 AM
In this thread, we should contribute by posting a proverb and try to give its meaning, how it can be well understood to correctly apply it when making comments or writing in Hausa language. Here is one for a start:

"KA DAUKO KAN JAKI BA BABBAKA"   :-X
Title: Re: MEANING AND USE OF HAUSA PROVERBS:
Post by: EMTL on January 30, 2009, 10:08:34 PM
Assalamu alaikum,
Ana amfani da karin magana do boye bayani da kuma gajarta shi, ko?
Title: Re: MEANING AND USE OF HAUSA PROVERBS:
Post by: waduz on February 02, 2009, 07:44:12 PM
A'a, akaramakallah. Ai harshen hausa yana da luggogi da dama. Kuma ka ga kaman wannan karin maganan, "ka dauko kan jaki ba babbaka" ai a ganina yana nufin wato kamar mutun ne ya bude asirinsa. Shin in ka dauko kan jaki kam ba'a babbake shi ba, ai za ka ba mutane mamaki. Na farko dai za'a zachi kila ko ka dan tabu ne, ko kuwa kana cin naman jaki ne! To amma in a babbake ka dauko shi fa? Kowa ya hango ai zai yi tsammanin kan sa ne, ko kuma na rago, ko makamancinsu.

Ma'ana dai, shine mu rika rufa asiranmu. Amma dai kam muna bukatan sharhi daga hausawanmu na K/L, kada mu yi noma a gonarsu! Ina ganin in muka dan yi nisa da wannan, zai kara mana ilmin sanin wannan kasaitaccen harshe da kuma inganci wajen iya magana da shi.

Ga wani "KOWA YA YI RAWA, BARE DAN MAKADA." Menene maanarsa? Kuma akan wane zance ya kamata mai magana yayi amfani da shi?
Title: Re: MEANING AND USE OF HAUSA PROVERBS:
Post by: MySeLf on March 30, 2009, 11:33:14 PM
WAduz,
Dauko kan jaki ba babbaka, na dauka yana nufin katono abinda yafi qarfinka kenan? kamar tsokano wanda kake zaton ba abinda zai iyya yi amma inna "watar qaiqai yake sai kasa hannu"

So bari in barku da
LUMBU LUMBU WUTAR QAIQAI