Salam. Sunana Bashir Ahmad ku ni sabon member a wannan shafin kuma ina fata za'a karbe ni hannu biyu kuma idan anga nayi kuskure ina farin ciki da kyara
barka da zuwa wannan dandalin, kuma munayi maka fatan
alheri. Bayan haka, kana iya tofa albarkacin bakinka a kowane
fanni da kaga zaka iya, banda kazafi da kuma zagin abokan
hira koda an baka haushi.
muna da manyan abokai irinsu GOGANNAKA (sarkin goraye)
BAKANGIZO (shugaban yan gudun hijira) MUHSIN (yaro da
kudi abokin tafiyan manya) MUDA (sarkin maska na kanoonline)
IBB (shugaban yan tawaye da yakin sunkuru) EMTL (durbin
duk duniya) HUSNAA (hankaka mai da dan wani naka)
PROF. ABDALLA (Kuliya manta sabo), IBRO2G (yaro man kaza)
TQTQ (Boka ci kaji), ADMIN (Sarkin yakin kanoonline),
ABU SUFYAN (Limamin malamai), ANAS (dan kunan bakin wake)
BABANSOYAYYA (special adviser on women affairs),
NURA JIBO (Zuma tafi da zakinki), WAZIRI (shugaban neman
yancin yan zaria kuma tsohon kwamishinan yan sanda na
kanoonline) da kuma ni DAN-BORNO duk muna yi maka marhaba
da zuwa.
Nagode Dan borno kuma idan Allah ya yarda zanyi amfani da wannan shawarar.