KanoOnline.com Forum

General => General Board => Topic started by: bamalli on March 31, 2010, 12:47:12 PM

Title: Wata sabuwa wai Gaddafi Yace A Raba Nijeriya Tsakanin Kabilunta
Post by: bamalli on March 31, 2010, 12:47:12 PM
Gaddafi Yace A Raba Nijeriya Tsakanin Kabilunta 
Marubuci Ibrahim Alfa Ahmed
30/03/2010
 


Muammar Gadhafi

Shugaba Muammar Gaddafi na Libya ya bayar da shawarar a raba Nijeriya kasa-kasa tsakanin kabilunta kamar yadda aka yi ad tsohuwar kasar Yugoslaviya, domin kawo karshen tashin hankali a kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a nahiyar Afirka.

Wannan furuci nasa na jiya litinin, ya biyo bayan shawarar da ya bayar a makon da ya shige cewa a raba Nijeriya tsakanin kasar Musulmi da ta Kirista domin a kawo karshen zub da jinin addini.

A bayan kalamin na sa na makon jiya, Nijeriya ta janye jakadanta daga kasar Libya, tana mai bayyana kalamun na Gaddafi a zaman "maras karbuwa", wanda kuma bai kamanci shugaban da ke kururuta hada kan Afirka ba.

A lokacin da yake mayar da martani a jiya litinin, Gaddafi ya sake nanata ra'ayinsa na a raba Nijeriya, amma a wannan karon ba kasa biyu ba, a raba ta zuwa kasashe da dama kwatankwacin kabilunta.

Ya kwatanta Nijeriya da tsohuwar Yugoslaviya, wadda ta kasu zuwa kasashe da dama a bayan rushewar tsohuwar Tarayyar Soviet.

Gaddafi ya ce duk wani matakin da za a dauka na raba kasar da dukiyarta, ya kamata a yi ta hanyar tattaunawa da cimma yarjejeniya ba wai ta hanyar zub da jini ba.

Title: Re: Wata sabuwa wai Gaddafi Yace A Raba Nijeriya Tsakanin Kabilunta
Post by: Bashir Ahmad on April 05, 2010, 08:22:39 AM
Gaskiya ni a tunani na Mu'ammar Gaddafi shugaban kasar libya maganarsa akwai kanshin gaskiya domin Nigeria tayi kabilu da yawa ga kuma rikice rikicen kabilanci.

Don't hate me, and don't hate Gaddafi.