Inna illahi wa inna illaihi raji'un.
Allah (S.W.A) ya yiwa tsohon gwamnan jihar Kano farko a farar hula wato Alhaji (Dr) Abubakar Rimi rasuwa jiya ranar 4/4/2010 akan hanyarsa daga Jihar Bauchi zuwa Jihar Kano.
Allah (S.W.A) ya jikanshi ya bawa iyalanshi da sauran al'ummar Musulmi hakurin jure wannan rashi. Ya saka mai da gidan Aljanna Firdausi, Ameen.
Allah ya jikan Alhaji (Dr.) Muhammad Abubakar Rimi.
Allah ya rabbil alamina ya gafarta masa yaba iyyalinsa haquri... ALLAHU AKBAR!!
Assalamu alaikum,
Allah (SWT) Ya Jikansshi da sauran dukkainin Musulmai marigaya. Muma Muna rokonSa(Ubangiji) Ya kyautata tamu karshen-amiyn.
Allah ya jikan musulmi.
what are the circumstances behind his death?
The circumstances behind his death was as sakamakon cutar hawan jini
Dubban daruruwan mutane ne suka halarci jana'izar gwamnan tsohuwar Jahar Kano na farar hula na farko,
Alhaji Muhammad Abubakar Rimi, wanda ya rasu a daren ranar Lahadi sakamakon cutar hawan jini.
Ciwon ya taso masa ne baya da 'yan fashi suka tare su a garin Darki, yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Kano daga garin Bauchi.
Jama'ar da suka halarci jana'izar tasa sun hada da shugabannin gwamnatoci, da sarakuna, da malaman addini, da 'yan siyasa da kuma dimbin jama'a.
Na'ibin Limamain Kano Malam Nazifi Dalhatu ne ya jagoranci sallar, bayan an shafe kimanin sa'o'i uku ana jiran isa da gawar fadar mai martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, inda aka yi jana'izar.
Mutuwar ta sa ta ruda jama'a da dama a jahar ta Kano, musamman ma masoyansa, duba da yadda ya baiwa jahar ta Kano muhimmiyar gudunmawa lokacin da yake mulkin jahar a 1979-1983.
A great loss indeed. Allah Ya jikansshi, Ya gafarta masa, amin.
May Allah in His Infinite Mercies Blessings and Mercies rest his Soul in peace.
May He fine forgiveness and Mercy with Allah (AMin)
The second best gov in Kano after Abdu Bako.