Nai jinkiri akan soyayya harshe na yayi nauyi sosai
wadda zuciyata ke so kunya tai shamaki da abota
1. Ni a yau zare da abawa zan warware gare ku abokai
zan batu akan soyayya ni lamarin ta ya dauren kai
dan kwa naga babu ruwanta mai hada attajirai da musakai
in taso tayo wani juyin sai ta hada talaka da musakai
ni a yanzu tai min hadin da ban so ba ko ince na mugunta
2. Kunga kar kuce na zauce kaina kalau bara kuji sosai
surkuki da sarkakiyar so na shige abin gwanin ban tausai
wadda zuciyata ke so ta rurrufe ido da gilasai
bata ma ganina amma sonta a zuciya yai rassai
yanzu yaya zanyi in furta ko kuma azuci in fidda ta
3. Sanda ni na fara ganin ta saida tassakani narrike baki dan kwa naga ta hadu sosai kyawun ta ne ya ban mamaki
doguwa fara mai gashi hancinta mai tsaho har baki
lokacin naso in furta sai naji ni nayi nauyin baki
sai kawai na canja tunani ni da ita muka kulla abota
4. Yau da gobe hausawa sunce wai asara gun duk mai rai
yanzu mun riga mun saba ni da ita ba batun bacin rai
ban ganinta bata ganina saidai muna waya mai cinrai
sonta ko yana dada yado zuciya kamar da an dasa tsirrai
wannan makauniyar soyayya sai yaushe nikwa zan warketa?
5. So nake ku sani a hanya nai makuwa ina ta bulayi
na rigada na shaida muku kome ake ciki ya zanyi
sonta yazamo wani sashen raina taba shi jinya zanyi
kunya ta hanani in furta ni jan'aji nake yin shayi
kar naje na tafka asara na dade rabon da inga irinta
6. Tsuntsun so yana shawagi yaka yaka zo ka kai mini sako
in ka tashi in kai gabas cikin garin da ba'a kyamar bako
ka tambaya ina wadda sunana da nata yai kama daga farko
zaka ganta mai kyawun sura sai ka zayyana mata sako
kace ta ringa daukar haske domin ta gane duk mai sonta
Alhamdulilla!
Da fatan sanaah yuseef (ummi) za ta karanta wannan waka danai domin ta
Ashe kai mawaki ne. Toh, Allah yasa Ummi taji