KanoOnline Online Forum

General => General Board => Topic started by: SAAHIB 92 on August 17, 2004, 05:44:34 PM

Title: FATA NA GARI LAMIRI
Post by: SAAHIB 92 on August 17, 2004, 05:44:34 PM
Assalamu alaikum.

Godiya ta tabbata ga allah,aminci ya tabbata ga fiyayyen halitta.

Fatana allah ya kara taimako, da kwarin gwiwa ga dukkan wadanda suka yi gagarumin aiki wajen hada wannan dandali na zumunci.[kanoonline]

Godiya ta musamman ga mashahurin malami abdallah,salisu danyaro da sauransu,bisa hana idonsu barci da kokarin nunawa duniya cewa .....karan jihar kano ya kai tsaiko.....domin ta isa magana a bangaren sha'anin yanar gizo.

Kira na musamman ga dukkan matasa da al'umar jihar kano har da arewa baki daya,cewa mu yi amfani da wannan dama ta hanyar da ya kamata. mu kuma goyawa manazartan wannan dandali baya domin su sami karfin gwiwar cigaba da wannan shiri na hadin  zumunta da kuma wayar da kan jama'a ta fuskoki daban-daban. MA'ASSALAM[/b]
Title: FATA NA GARI LAMIRI
Post by: FARI on August 17, 2004, 06:49:28 PM
Haka yake .......amma dai barka da zuwa.....