KanoOnline Online Forum

General => Culture => Topic started by: Hausa Error on April 06, 2003, 03:28:10 AM

Title: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Hausa Error on April 06, 2003, 03:28:10 AM
Assalamu alaikum yan-uwa da abokan Arziki na kano online,da wani dan karamin tunanine nayi naga kamar ya kamata mu dan  wasa kwakwalwa,mu dan gwada kacici-kacici (hausa/english riddles)

 Ga wasu nan dai  kan na samo wasu,wanda ya sanni ya ba da ansa. in kana/kina da wani ku rubuto


 - shanu na dubu amma madaurinsu daya.

 -baba na daka, gemu na waje

 -takanda ba kashi ba

 -baba ya zaga iya ta zaga basu hadu ba


 -yadda dillin yakanyi dillin haka ma dillin ya kanyi dillin

 - tsimagiyar kan hanya make yaro make babba


 Wanda ya san ansa ya bayar in kuma kun bada gari na fada maku ansar
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: IBB on April 08, 2003, 05:30:37 PM
Quote
Assalamu alaikum yan-uwa da abokan Arziki na kano online,da wani dan karamin tunanine nayi naga kamar ya kamata mu dan ?wasa kwakwalwa,mu dan gwada kacici-kacici (hausa/english riddles)

 Ga wasu nan dai ?kan na samo wasu,wanda ya sanni ya ba da ansa. in kana/kina da wani ku rubuto


 - shanu na dubu amma madaurinsu daya.

 -baba na daka, gemu na waje

 -takanda ba kashi ba

 -baba ya zaga iya ta zaga basu hadu ba


 -yadda dillin yakanyi dillin haka ma dillin ya kanyi dillin

 - tsimagiyar kan hanya make yaro make babba


 Wanda ya san ansa ya bayar in kuma kun bada gari na fada maku ansar


ANS TO UR RIDDLES

TSINTSIYA
WUTA DA HAYAKI
KANWA
KUNNE
KAZA DA KWAI
YUNWA
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Ibro2g on April 21, 2003, 03:48:52 AM

Thats very Impressive you two
I'll try and get some too
I shoulda used da blue.... :-/
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: kilishi on August 07, 2003, 07:48:32 PM
Yadda dillin takan yi dillin haka ma dillin yakan yi dillin
'yan matan gidan mu masu fararen kunnuwa
kogi ya aki ya kawo a gefe nake wanka
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: IBB on September 17, 2003, 09:01:10 PM
yarda kaza ta kanyi kwan nan haka ma kwan nan ya kanyi kaza

tunkiya?
i dont know the last 1
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: kilishi on October 14, 2003, 02:49:33 PM
Quote
yarda kaza ta kanyi kwan nan haka ma kwan nan ya kanyi kaza

tunkiya?
i dont know the last 1


FATE-FATE is for the zazzagawa's abincin su ne
Title: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Shiekh on May 17, 2004, 04:55:16 PM
wasa kwakwalwa da muhawara kuma fa? are they all this part of this room? like:"wani mutum sun tafi fatauchi da abokinsa, sai suka samu dukiya.  sai ya sai plot of land. shi kuma abokin sai ya gina daki daya a wannan filin.
 sai suka nemi aure, kowannensu aka bashi.
to wanene zai tashi ya bar dakin between the friends?"  

if none can afford to build another room
Title: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Anonymous on April 07, 2005, 08:56:14 PM
Shiekh I definitely think just like you.
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: IBB on May 24, 2007, 01:33:26 AM
the owner of the land? he owns the property in the 1st place
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Ihsan on June 08, 2007, 10:57:26 PM
gaskiya kam IBB...tunda idan babu land din ay the other guy cannot build a room on air. dan haka sai ya tashi ya bashi plot din shi (idan ma rushe dakin zai yi sai yayi) amma dai wuri na mai plot ne.
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: amira on July 31, 2007, 12:59:57 AM
Lets see if anyone can get the answers to theses riddles:

rawanin sarki ya faskari nadewa.....................

Uku Uku gama gari................

Dakin saurayi babu kofa.....................

kasuwa taci ta watse, ta bar kare kala.................
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: IBB on July 31, 2007, 10:36:55 AM
Na bada gari
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: amira on July 31, 2007, 06:40:57 PM
Haba dai, well hia are the answers in order

Hanya

murfu

Kwai

Harshe

Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: IBB on August 01, 2007, 04:57:36 AM
sum more pls i like the egg riddle (dakin saurayi ba kofa) lol
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: amira on August 01, 2007, 06:21:43 PM
okay here goes..........

godiyata tana da ciki, bana hawan godiyar sai ciki na ke hawa.....................

Rigata guda, aljifunta dari......................

Hanya daya ta rabu biyu...............
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: IBB on August 01, 2007, 10:15:33 PM
Nwah woh I'm loosing my Hausa ne? I dont know these ones again. Ni dai na bada gari. Anybody wanna try before our Lady Amira drop the ans
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: amira on August 04, 2007, 08:38:21 PM
hia are the answers in order

Daki da gado a ciki

Gidan gara

wando
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: amira on November 08, 2007, 12:03:14 AM
IBB and other members, ku dan nemo mana other riddles cos am out of them.
Thanks ;)
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: MySeLf on November 08, 2007, 12:26:08 AM

Well here we go amira:-

Shanuna dubu ma daurin su daya....


Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: gogannaka on November 09, 2007, 02:24:50 PM
Tsinstiya.
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: gogannaka on November 09, 2007, 02:29:18 PM
Iya ta zaga baba ya zaga basu hadu ba?
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Bayya on November 09, 2007, 02:38:33 PM
Kunne.
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Bayya on November 09, 2007, 02:40:55 PM
Dan baka a bayan shuri.....
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: gogannaka on November 09, 2007, 03:38:02 PM
Kunne.

Bayya kayi saurin amsawa.
Da ka yi irin ta wani bakatafe,da aka tambaye shi 'iya ta zaga baba ya zaga basu hadu ba'
His answer was 'Dan b*&^% uba, wata ta buya'  ;D
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: MySeLf on November 12, 2007, 12:42:04 PM
Dan baka a bayan shuri.....

Farce..

Yan matan gidanmu masu farin kai
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Bayya on November 12, 2007, 02:26:02 PM
To yaya gogan,
In na amsa yanzu banyi sauri ba?
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: gogannaka on November 14, 2007, 08:42:11 PM
LOL...yes bayya ba ka yi sauri ba.
Carry on!
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Dan-Borno on November 14, 2007, 09:37:50 PM
 ;D  ;D i can answer this one

Tabarya?
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Bayya on November 20, 2007, 07:32:20 AM
Well done DB ;D ;D ;D
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: gogannaka on April 28, 2008, 02:20:37 PM
Ba wani kacici kacici ne?
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: amira on May 12, 2008, 06:52:56 PM
Sai dai ka samo mana ;)
Title: Re: Kacici-Kacici (riddles)
Post by: Ahmed.WANG on December 23, 2008, 10:59:32 AM
To, da ban sha'awa. Akwai saura...... Me ne?

     Na sara ta ki saruwa, na bizne ta ki biznuwa.

     Sarki ya sauko daga kan doki.

     Kogina ya kai ya dawo. Babu mai iya ketarewa sai Bello mai dan warki.