Show Posts

This section allows you to view all posts made by this member. Note that you can only see posts made in areas you currently have access to.


Messages - jaybee

Pages: [1]
1
Culture / Re: tatsuniya online (GIZO DA GOGI)
« on: May 24, 2007, 12:34:09 PM »
Assalam Alaikum Ihsan,
A gaskiya na ji dadin Tatsuniyarki ta Diskindaridi, sai dai kash kina amfani da abin nan da ake kira Ingausa wajen bayar da labarinki. Don Allah ki daure ki daina hada Ingilishi da Hausa, idan Hausa, Hausa kawai, idan Ingilishi, Ingilish kawai. Da fatan ban bata miki rai ba. A huta lafiya.
Jibril

2
Assalam Alaikum, Gaskiyarka Saahib,
Don a gaskiya ya kamata a rika tace wakoki kafin a fitar da su, domin kuwa wasu wakokin ba za ka game me suke nufi ba, amma insha Allahu nan gaba za a dace.
Wasslam :D

3
Assalamu Alaikum,

A gaskiya na ji dadin bayaninki  HUSNAA kwarai da gaske, Allah ya saka da alheri, Allah kuma ya sa 'yan uwa su gane.Domin kuwa abin da kika fada gaskiua ne, ba 'yan wasan Hausa ba ne suke bata tarbiyyar 'ya'yan Hausawa ba, su dai suna nuni da irin abubuwan da suke faruwa ne a zamani, domin a yi hattara

Ashe daman akwai JAKIN MUMBAI ;D, wallahi ban taba ji ba sai a wajenenki
Ma'assalam

4
Assalam Alaikum!
Ni a gani na komai na bukatar lokaci, domin kuwa idan ka yi la'akari da samuwar fina-finan Hausa za ka ga abin jariri ne, idan ka kwatanta shi da suaran wasu abubuwa na Adabi. Kuma shawara a nan ina ganin ya kamata a shiga wannan harka ta fina-finai a santa ciki da waje, sannan a gano inda ta yi gibi, to unsha allahu wata rana za su dace da rayuwar Hausawa.
Ma'assalam.

5
Culture / Re: REAL TRADITIONAL NAMES (sunanka da sunanki)?
« on: February 12, 2007, 10:51:38 AM »
Hi, Ummita
I just wanna let u know that Asibi is not a Hausa traditional name,it is a name that Alago tribe called a girl who was born on Saturday. But the name was originated from a Hausa name Asabe. U can learn more about this if u check one B.A. Dissertation title "Dangantakar Al'adun Hausawa Da Na Kabilar Alago Da Ke Cikin Karamar Hukumar Doma Ta Jahar Nassarawa" Department of Nigerian Languages Bayero University, Kano.
Thank U.

6
Culture / Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
« on: February 07, 2007, 12:21:45 PM »
wata sabuwa kuma... in ji 'yan caca

7
Culture / Re: mu kya kya ta online
« on: February 07, 2007, 12:17:40 PM »
Assalam Alaikum 'yan'uwa. Da fatan dan wannan gajeren labarin nawa zai sa mu kyaykyata.
Wai wani Bafulatani ne ana koya masa farillan alwala, sai aka ce masa "wal fauru" wai shi irin ya san fassarar sai ya ce "da kura". wai ashe sunan kura da Fulatanci (Fauru).

8
Culture / Re: mu kya kya ta online
« on: February 01, 2007, 01:24:45 PM »
Assalamu Alaikum. Da fatan wannan dan labari nawa zai sa dan kyakyata.

Wai wata rana ne wani Buzu ya je jin wa'azi wajen wani malami, sai ya ji malamin yana ta jero manyan alkaba'irai (manyan zunubai),ashe kuma shi Buzun duk yana aikata wadannan munanan kaba'iran. Da malamain ya gama wa'azi sai Buzu ya mike tsaye ya ce"Malam! ya aka yi kag gane ne?" 

9
Culture / Re: Karin magana
« on: January 16, 2007, 01:39:36 PM »
Gima ya fadi, Rakumi ya shanye ruwan Kaza...

10
Culture / Mu Kyautata Rubutunmu
« on: January 10, 2007, 02:22:42 PM »
Assalam Alikum 'Yan uwa. Bayan gaisuwa mai yawa da fatan an yi sallah lafiya, kuma ina fatan an shiga sabuwar shekara lafiya.
Ina so in yi amfani da wannan dama domin in yi kira ga marubuta litttattafan soyayya na zamani mai suna ( Adabin kasuwar Kano/ Kano Market Literature) da su daure su rika karanata littattafansu sosai kafin a kai ga bugawa, wato (proof reading). domin akasari idan kana karatu za ka rika karo da kurakurai da dama, wani lokacin za ka ga an hada kalmar da ya kamata a raba ko kuma a raba kalmar da ya kamata a hada, da dai makamantansu.
Marubuta don Allah a kula, mu kara kyautata rubuntunmu na Hausa.
Daga Jibril Shu'aibu Adamu

Pages: [1]

Powered by EzPortal