Show Posts

This section allows you to view all posts made by this member. Note that you can only see posts made in areas you currently have access to.


Messages - Ahmed.WANG

Pages: [1]
1
Culture / Saye
« on: December 23, 2008, 11:32:16 AM »
Saye watau kin kiran abu da sunansa ta hanyar sayawa a yi amfani da wasu kalmomi daban amma da ma'ana iri daya.

Misali: A wajen haihuwa, akan ce "Ta sauka" ko "Ta rabu lafiya".
         A wajen mutuwa, akan ce "Ya riga mu gidan gaskiya" ko "Ya kai takarda".
         Da ka ce "cin kwan makauniya", kana nufin ba ji ba gani.
         Idan an ce wani "mai dogon hannu" ne, ma'anarsa barawo ke nan.

Akwai sauran misalan da ka/ki san su?

2
Culture / Re: Kacici-Kacici (riddles)
« on: December 23, 2008, 10:59:32 AM »
To, da ban sha'awa. Akwai saura...... Me ne?

     Na sara ta ki saruwa, na bizne ta ki biznuwa.

     Sarki ya sauko daga kan doki.

     Kogina ya kai ya dawo. Babu mai iya ketarewa sai Bello mai dan warki.

3
Culture / Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
« on: December 23, 2008, 10:47:43 AM »

In ka ga gemun 'dan uwanka ya kama wuta shafa wa naka ruwa.

Gwanin ruwa shi ruwa ke ci.4
Sarkingida, ka yi kokari.

Pages: [1]

Powered by EzPortal