Show Posts

This section allows you to view all posts made by this member. Note that you can only see posts made in areas you currently have access to.


Topics - Bajoga

Pages: [1]
1
General Board / Ta'aziya Ga Jama'ar Late Moi Fika.
« on: March 11, 2009, 03:01:09 PM »
:'( :'( :'( Salam.

Ina mai mika ta'aziya ga dukkan yan uwa da abokan arziki don rashin da akayi na His Royal Highness, The Moi of Fika & Chairman Yobe state council of chiefs Emir of Fika's palace, Alh. (Dr) Abali Muhammed Ibn Idrissa (CFR, CON, LLB (HONS)). Ubangiji ya jikansa da rahma, Allah kuma ya baiwa Iyalansa, Yan'uwa da kuma dukkan sauran jama'a hakuri wannan rashin.

Mu kuma in tamu tazo Allah yasa mu cika da imani. :'( :'( :'( :'( :'( :'( :'(

2
General Board / Yar Adu'a In Jos
« on: March 10, 2009, 10:31:07 AM »
Salam.

What is happening ne in Jos to Yar Adua, naji labarin wai anjefeshi. Wa yakeda gaskiyar maganar ne?

3
General Board / Bauchi???
« on: February 23, 2009, 04:33:32 PM »
Salam.

Pls what is happening in Bauchi State ne? Naji kamar something is wrong now.

4
General Board / Barka Da Sallah
« on: December 08, 2008, 06:42:05 PM »
Salam,

Ina mai mika godiyata ga Allah madaukakin sarki daya bamu daman ganin wannan lokaci na sallar layya (Eid Mubarak), muna fata Ubangiji ya karba mana dukkan ayyukanmu na alkhari, ya kuma yafe mana dukkan kura-kurenmu. Har ila yau ina mai mika gaisuwar barka da sallah to all members of Kanoonline tare da iyalanmu baki daya Allah yasa munyi aiki karbabbe, amin.

I will like to use this great opportunity in roki Allah da ya amsa dukkan addu'o'in Mahajjatanmu da suke a kasa mai tsarki yanzu, Madaukaki kuma ya basu ladan aikin Hajj.

Allah ya nuna mana next year kuma cikin koshin lafiya tare da kwanciyar hankali.

5
General Board / GSM Network!!!!!!!
« on: April 24, 2008, 02:01:59 PM »
GSM was well welcome a lokacin shigowarsu wannan kasa tamu Nigeria. Because alot of abubuwa was now became easy, take misali kamar making business,sada zumunci, Office work and many other things wadanda ma bazasu kidayo ba.

A yanzu dai almost everybody was now enjoying GSM in one way or the other.

But our main problem yanzu shine 'Network' din, gaskiya yanzu abin is getting worst and worst, don mu a yanzu we can make or receiving a calls in the evening a koda yaushe. (I don't know ko iya area 'n mu nekawai) especially CELTEL (B/cause shine wanda yawancinmu muke anfani dashi a area ,nmu), kuma bamu sani ba ko the are aware of it or not.

Gaskiya yakamata wadanda suke da hakki su sa baki a wannan issue.

I hope to hear from you.

Thanks.

6
General Board / Allah Allah Amin!!!!!
« on: January 21, 2008, 09:54:43 AM »
Alhamdu lillah! Alhamdu lillah!! Alhamdu lillah!!!

Allah cikin ikonsa yasa na sake dawowa cikin wannan majalisa mai albarka bayan kammala aikin Hajj da mukayi a wannan shekara.

Allah ya karba mana ya kuma maimaitamana, amin.

Ina godiya ga dukkan yan'uwa da abokan arziki na wannan majalisa saboda irin addu'o'i da suka rika yimin kafin tafiyarmu, Allah kuma cikin ikonsa ya karbi addu'a, don mun gabatar da dukkan ayyuka cikin jin dadi da koshin lafiya, har ila yau mun dawo ga iyalanmu lafiya kalau.

Allah ya baiwa dukkan musulmin da baisamu damar zuwa ba ikon zuwa, mu da muka je kuma ya bamu ikon maimaitawa, amin.

Alhamdu lillah!!!!!!!

7
General Board / Away From The Forum!!!
« on: November 23, 2007, 05:23:29 PM »
Assalamu Alaikum!!!

Ina so inyi amfani da wannan dama don neman gafara ga duk wanda na batawa either knowngly or unknowngly. Wannan ya faru ne sakamakon shirin tafiya Saudi (Hajji) da nakeyi a yanzu (Kuma hakan nema ya kamata ga dukkan musulmi), kuma i believe za'a iya neman mu a kowane time, kuma may be bazan samu damar yin bankwana ga members ba, that is why i decided to post this topic a matsayi neman afuwa da kuma bankwana.

A bangarena, ni har ga Allah na yafewa duk wanda ya bata mini kuma ina rokon nima a yafemin duk abubuwan da nayi ko ta fannin rubuto ko dai wani abu, Allah kuma ya yafe mana duka.

I will be keep visiting this memorable forum till lokacin da aka nememu don tafiya. Saboda haka in anji shiru dai, tooo................

Daga karshe ina yiwa dukkan members na wannan forum godiya da irin yadda kowa yake bada irin tasa gudun muwa don ciyar da majalisar gaba. Allah ya taimake mu baki daya, amin

In mun dawo Allah ya sada mu da alkairinsa, in kuma Allah ya dauki rayukan mu, to Ubangiji ya sadamu a gidan Aljanna.

Wassalamu Alaikum!

8
General Board / Nigerian Roads For Sale!!!
« on: November 16, 2007, 12:05:38 PM »
Assalamu Alaikum

Toooo yan Nigeria gafa dama ta samu, don gwamnatin tarayya ta kudiri niyyar sayar da manyan hanyoyin sufurinta. But wannan abin gaskiya it's not good and kuma ba adalci bane yin hakan.

Kamar yadda aka fadi a gidan radio na bbc jiya da rana, mataimakin shugaban kasan ta Nigeria Jonathan G. shine yayi wannan jawabi kuma ya jaddada hakan da cewa wai shine hanyar da za'a cimma buri a Nigeria wajen kula/gyara hanyoyinta.

Kamar yadda wasu masu maida martani/wadanda akayi hira da su akan wannan lamari suke cewa-wannan abin dai sun kira shi da cewa kawai zalunci ne, gaskiya basu nuna jin dadin hakan ba, hasalima dai -  an taba fara irin wannan lamarin wanda ba'a cimma nasara ba, sa'annan kuma yanzu ance za'a cigaba. Anya kuwa kwalliya zata biya kudin sabula????

Kamar yadda wani mutum yayi bayani acikin radio (wanda ba'a fadi sunansa ba) yake tambaya cewa wai shin menene hanyar da talaka zai ci gajiyar gwamnati?  Misali:-

1. Akwai Asibitoti
2. Akwai ruwan sha
3. Akwai wutan lantarki
4. Akwai tsaro
5. Kula da hanyoyi
6. Samar da aikinyi
7. Ingantaccen ilmi

 Da dai sauransu, yake cewa kuma gashi ana ta sayar da abubuwan, to talaka ya zaiyi nekan? Gaskiya wannan tambayar abin dubawa ne idan akayi la'akari da irin yadda kasar take a yanzu.

Allah dai yasa mu dace da ayyukan kirki/na gari.

Amma nasan akwai wadanda suka fini sanin wani abu akan wannan lamari, may be they can help us to have more light about this issue.

 

9
General Board / Poll {Hausa Fim!!!}
« on: October 07, 2007, 10:40:13 AM »
Assalamu Alaikum!!!!
[/b][/u]
Sakamakon irin yadda mukayi ta rubutu akan wannan topic din "Hausa Fim" wanda kuma nine na sanya topic din (duk da cewa akwai wani dama can), naga cewa ya kamata in sanya wannan poll din don ganin yadda amsoshin zasu kasance.

Muna maraba da duk wani gyara ko shawari akan wannan, harma a wani bangaren daban.

Wassalam

10
General Board / FLIGHT TO FIRDAUSI ISLAND IS NOW AVAILABLE
« on: October 07, 2007, 07:44:39 AM »
Assalamu Alaikum
,
 
Important announcement for intending passengers to Firdaus.
 
This is to inform you that the free flight to Firdaus is now at the Ramadan Airport. All you need to do is to obtain your ticket at the Tarawih and Tahajjud booking offices closest to you while the offer last. It just  9 days to go (Almost 3-4 days remain). This may be the last flight in your life time!
 
Remember, Firdaus is a One Trillion Star Hotel, the duration of your stay there is eternal!

Think of different type of delicious dishes, assorted drinks, conducive atmosphere you cannot imagine!
 
I pray will meet there! But don't forget to activate your Lailatul Qadr on the 21, 23, 25, 27 & 29 days of this blessed month, browse your Quran  and text a lot salat to our beloved Prophet Muhammad (SAW).

Allah ya sadamu a chan, amynnnn.

GOOD LUCK
[/b]

11
General Board / Masarautun Gargajiya!!!
« on: August 03, 2007, 05:57:10 PM »
Assalamu Alaikum!!!

Ina so inyi amfani da wannan dama don in gabatar wannan topic din kamar yadda yake a sama.

Naso in bada dan tarihin sarautan gargajiya kadan kafin in iso bayanin da nakeson yi. Infact we all agree that sarautan gargajiya dai wani abu ne wanda yake da tumbun tarihi tare da kyawawan al'adu, in the previous days, zakaga basarake shine kamar uba a kowane gari, a duk time din da wani abu ya rikice they are the ones to judge.

Let me not to take more time, Idan muka duba a wannan zamani zamuga cewa yanzu sarautan gargajiya ta zama ba komai ba.
Today! Sarakuna basu da say! sai abinda aka gaya musu. Yan siyasa da masu kudi sun maida sarakuna kamar bayi, su kuma sarakuna sun maida kansu kamar maroka don roko (sorry ba ina son in tozarta fada bane wallahi).

To gaskiya if we think about it, we can realise that abin idan ka gani sai ya baka kunya ko mamaki.

Shin menene dalilin faruwar haka?
Wake da alhakin lalacewar wannan abun?
Ta yaya mutuncin sarakuna zai koma kar da?

Na rubuta wannan ba don in ci zarafi wani/wata ba, in akwai wanda na batawa, to ina neman afuwa.

Jibrin.

12
Islam / saving/current account
« on: July 30, 2007, 03:22:07 AM »
Assalamu Alaikum!

May i pls get more information on the above topic?

I was very very comfuse, some people are saying there is something haraam in it, while some are saying not.

What was the reality?

13
General Board / Hausa Fim
« on: July 26, 2007, 04:41:26 AM »
Asslamu Alaikum!!!

Ina son inyi amfani da wannan dama don inyi magana akan harkan shirin fim (musammanma na hausa) wanda shine muke tare dashi a kusa da mu kuma muke yawan mu'amala dashi.

Dukkan mu dai mun yadda cewa Hausa wata abace wadda take da al'adu wadanda basu saba ka'idodin shariar musulci ba, kuma tana koyar da kyawawan dabi'u ga iyalanmu baki daya.

Farko fitowar fim na hausa lallai mutane sunyi matukar farin ciki da hakan, domin ko ba komai tofa zamu fahimci al'adummu na hausa sosai (mai makon yawan ganin fina-finan da ba al'adunmu ba). Abin yana kara bunkasa mutane suna kara son ganin fina-finan hausa.

To amma fa a yanzu abubuwan sun fara lalacewa, don idan kaga wani abun, harma bazaka iya bada labari ba. Misali ka lura kaga yadda ake sanya kaya musammam mata, kai kace wallahi ba ya musulma kuma ba haushiya ba, haka idan kaga yadda mace take rawa tana jijjiga dukkanin jikinta, abin har ba'a cewa koma.

Gaskiya ina ganin yakamata masu fada aji su sa baki acikin wannan harka domin kuwa watara fa yayammu ne ko kannemu.

Lalle ban fadi/rubuta wannan magana don in bata wa wani ba, imma akwai wanta ransa ya baci to ya feni, nayi ne da niyar gyara.
Allah ya taimakemu, amin.

Jibrin M. Yusi Bajoga. :)

Pages: [1]

Powered by EzPortal