Show Posts

This section allows you to view all posts made by this member. Note that you can only see posts made in areas you currently have access to.


Messages - sister

Pages: [1]
1
chit-chat / Re: Wata Sabuwar Member
« on: March 14, 2007, 07:32:02 PM »
madalla madalla da fatan na same ku kalau. Amin summa amin. to dan uwa kana neman ragon da za ka saya ne? idan ranar cin kasuwa ce to farashin ya kan tashi daga $900,000 US wato dallar Amurka. Amma idan yau yau kake so to za ka iya biyan $1,000,000 US zuwa $1,500,009.99c dallar amurka. ya dangantaka da tsufa da size da weight da kuma kallar hakorin ragon. Wanda ake musu buroshi tare da makileen kullum sau biyu a rana sun fi tsada amma kuma sun fi dadi a rokototo wato naman kai da waina. amma masu warin baki (wanda ko aswaki ba a yi masu) su ne masu araha. Duk masu neman ragunan su yi placing order dinsu da lumbar kati wato credit card a nan idan na dawo zan baku guarantteed. Kalam Wahid.

2
chit-chat / Wata Sabuwar Member
« on: March 14, 2007, 05:17:37 PM »
assalamualaikum. na shigo wannan faggen da kafar dama da fatan za'a karbe ni hannu biyu. sannan kuma ina da kawa, yar uwa kuma babbar aminiyata a wannan wurin. to kullum sai na ga tana zuwa tana duba wannan website dai naku. shine yau na ce bara nima na fara ba dan komai ba dan karin ilimi da kara fahimtar halayen mutane na arewa. ina fatan ba za a samu misunderstanding dani ba dan ni mai hakuri ce. Nagode. kuma yar uwata sai a dan koya min harkar taku ta kimiya da fasaha wato 'tekanology' da kuma harshen language din naku wato 'ingilishi'  dan kinsan mu dai daga kauye muke. sannan kuma ki dinga yi kina dan aiko mana text ko da dan fflashing din nan. Allah ya ce a hada zumunci. ko ya kuka ce yan uwa? ko dayake masu magana sun ce shuru ma lafiya ce.

Pages: [1]

Powered by EzPortal