JIYA BA YAU BA

Started by mlbash, September 03, 2004, 09:17:53 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

mlbash

JIYA BA YAU BA.

Hakika duk wanda  yayi karatun Hausa a zamanin day a shude nana baya kadan , yasan cewa, Marubutan da sunyi matukar aiki ban a wasa ba . Duk inda aka ambaci sunan mutane kamar su Alhaji Abubakar Imam, wanda a duk marubutan littattafan Hausa, babu mutumin da yayi tashensa da shahararsa, wajen nuna fasaha tare da gogewa. Alhaji  Abubakar Imam, yayi nasarar lashe gasar rubutun littafi a shekerar 1933, yayi wannan nasara ne kuwa da littafinsa na farko, wato ?RUWAN BAGAJA?

A wannan littafi Alhaji Imam, ya nuna fasaha da kwazo. Kuma abin burgewar anan shine Alhaji Imam yana da shekaru 22 kacal a wancan lokacin yayi wannan mashahurin aiki! ALLAH sarki, Jiya ba Yau ba. Yanzu wannan zamani namu da muke ciki ya rigaya ya sauya, marubutan wannan zamani basu san komai ba banda rubutun littattafan soyayya, wanda ba fasaha, ba tunani,sai zancen banza,wanda ba ilmi acikinsa.

A duk cikin littatafan zamanin nan da muke ciki kadan suke bada ma?ana, wanda basira da hankali suke ciki. Kamar littafin nan wato, ?SUDA? na DAN KANE. Wannan littafi hakika ya sami karbuwar jama?a, wanda an nuna basira da ilimi tare da nasiha a cikinsa.
To Jama?a rokona shine marubuta suke aiki da tunani da nutsuwa, basira da fasaha tare da duban abin da mutane ke bukata wanda zaiyi musu amfani Duniyarsu da Lahirarsu. Ba wai ayita rubutu ba kawai da ka wanda ba ilimi da tunani.
ALLAH yasa mugane, kuma ya taimakemu, Ameen!
 
t is my intention to make the neglected aspect of our societies viable

Nuruddeen

o try and fail is atleast to learn. That will save one the inestimable loss of what might have been (positive or negative).

SAAHIB 92

mlbash,
allah sarki ka tuna jiya ko??  kowa ya tuna bara lallai bai ji dadin bana ba.
shawarata a gareka shine yi kokari ka samo irina da irinka wadanda suke da kishin gyara ta fannin rubuce-rubuce, sai a dawo da martabar rubutu mai ma'ana.amma har yanzu akwai nagartattun marubuta masu fikira da hangen nesa,kamar yadda kace labarin BABA SUDA ...don haka shin  ko za KA FARA RUBUTU yanzu ni ma ina da tunani irin naka. :idea:
Radina billahi Rabban,
Wa bil Islami Dinan,
Wa bi Muhammadin Nabiyya!"

 ABBAS A YAKASAI

Ihsan

Salaam
mlbash, kayi gaskiya kam akan zancen litattafan hausa na zamani. Amma fa ba duka aka hadu aka zama daya ba. Dan kuwa wasu litattafan suna koyar damu zamantakewar dan adam ne. Na yadda suna hadawa da soyayya amma dai ay suna fada mana ne abun da ke faruwa a wannan zamani ne.  Ina son karatun hausa amma fa ba kowane irin littafi nake karantawa ba dan kuwa yanzu kowa ma ya tashi sai ya ce zai rubuta littafi. Sai ka karanta ka ji duk shirme...dan ni kam da na fara naji bai zuwa ko ina na ke ajiye shi.

Wani abun kuma shine litattafan hausa suna kara koyar damu hausa (a karance da rubuce). Karatu da rubutun hausa da na iya saboda nayi hausa ne a makaranta but mostly saboda ina karatun litattafan hausa ne. Coz that is where I learned new words I never thought existed.

So I'll say litattafan hausa na zamani suna da kyau kuma basu da. Amma na wasu yafi na wasu.
greetings from Ihsaneey

Eskimo

MHN......
ANYA KUWA!!!???
NI KUWA NA KASA GANIN MATSALOLIN RUBUTUN HAUSA NA ZAMANI? INA ZATON KO WANE SOCIETY SUNA DA RUBUCE RUBUCE AKAN FANNONI DA BAN DA BAN, DAGA CIKI KUWA HAR DA SOYAYYA. KILA DAI INA ZATON KU A NAKU RAAYIN KUN FI SON IRIN LABARUN BARKWANCI....AMMA WANNAN BA WANI KWAKWKWARAN DALILI BANE NA SUKAR SAURAN.

ZAMANI YANA CANZAWA...KUMA KOWANE ZAMANI DA ABU DABAN YAKE ZUWA. BAN GA DALILIN DA ZAN RINKA KARANTA LABARIN DA MAGE KO JAKI KO BERA YA KE MAGANA DA DAN ADAM BA. KO LABARIN DA BASHI DA WANI JIGO KAMAR "SUDA" DA KEKE YABO. KOWA DA RAAYINSA...GASKIYA NE.

A KULLUM MUNA SUKAR SATAR ALADUN WASU. KAMAR SATAR ALADA WANI MUGUN ABU NE, BAYAN KUWA KOWACE ALADA TANA SATAR WATA..SHINE TUSHE NA CI GABA. IN MA HAR SATAR LABARU KO ALADA MUGUN ABUNE TO AI ITA KANTA MAGANA JARIN LABARUN LARABAWA DA TURAWA...EH...TURAWA..AKA FASSARA ZUWA HARSHEN HAUSA!

LITTAFAI KAMARSU RUWAN BAGAJA. JIKI MAGAYI, SHEHU UMAR SUNA DA MUTUKAR SHAAWAR KARANTAWA, AMMA NA TABBATA AKWAI LITTAFAN ZAMANI DA SUKA FISU SHAAWA GA MAI RAAYINSU.

BABBAR MATSALAR MALAM BAHAUSHE ITACE KIN YARDA DA CANJIN ZAMANI. SHI KUWA ZAMANI IN BAKA YARDA DASHI KA CHANZA YANAYIN ZAMANKA YA DACE DASHI BA, TO SHI TABBAS ZAI CANZA KA. MISALI IN HAUSAWA BASU RUBUTA LABARANSU DAKANSU BA WASU KABILUN ZASU RUBUTA LABARIN HAUSAWA.

MAIMAKON MUYI TUNANIN YADDA ZAMU GYARA WADANNAN ABUBUWA KAMR FIM NA HAUSA, RUBUCE RUBUCEN SOYAYYA, DA WAKOKIN ZAMANI (YAN RAWAR ZOO ROAD..HEHEHEHE) KULLUM SAI DAI SUKARSU MUKE YI. SU KUWA WADANNAN ABUBUWA SUNZO KENAN BA CANJI..IDAN MUTUM YAGA WANI ABU DA BAI YI MASA SAI YA YI NASA..KILA NASAN YAFI KARBUWA A CIKIN JAMAA, KAGA YA KAWO GYARA KENAN.

ALLAH YA GYARA MANA...AMIN.


color=blue]NOBODY is PERFECT and I am NOBODY.[/color]

mlbash

DUKKANNINKU GODIYA NAKE SABODA GUDUNMAWARKU, ALLAH YAYI MANA JAGORANCI! :)
t is my intention to make the neglected aspect of our societies viable

Nuruddeen

Quote from: "mlbash"DUKKANNINKU GODIYA NAKE SABODA GUDUNMAWARKU, ALLAH YAYI MANA JAGORANCI! :)


Bash, kwana biyu. ya ya garin ne? I am sorry for not responding to this topic accordingly though i have a lot to say but it just so happened that I lost somebody. I will try to cope with the happenings around.

Thanks.
o try and fail is atleast to learn. That will save one the inestimable loss of what might have been (positive or negative).

mlbash

Quote from: "Nuruddeen"
Quote from: "mlbash"DUKKANNINKU GODIYA NAKE SABODA GUDUNMAWARKU, ALLAH YAYI MANA JAGORANCI! :)


Bash, kwana biyu. ya ya garin ne? I am sorry for not responding to this topic accordingly though i have a lot to say but it just so happened that I lost somebody. I will try to cope with the happenings around.

Thanks.

ALLAHU AKBAR! ALLAH YA JIKAN RAI!
t is my intention to make the neglected aspect of our societies viable