Shin menene niyyarku a rayuwarku????

Started by Sas, November 20, 2004, 08:14:35 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Sas

Salamu Alaikum,

Sau da dama in nayi magana da mutane sai suce min ai suna da niyyar su aiwatar da wasu abubuwa a rayuwarsu da zasu kawo ci gaban Hausawan mu.

Amma sai abun mamaki manyanmu basa yi iyaka karfinsu domin suga sun aiwatar da abubuwan da suka bukaci aiwatarwa lokacin suna da kuriciyarsu duk da cewa suna da halin yin hakan.

Me yasa kuke ganin hakan yana faruwa kuma ko kuma zaku zama kamar hakan??

amma babban dalilin wannan shafi shine idan kana da wasu abubuwa da kake so ka aiwatar da kake ganin zasu kawo ci gaban mutanen Hausawa da ma dukkan Nigerian to ka fade su in da hali.

Misali kada ka/ki ce zan samar wa da mutane abinci ka/ki dakata anan. Wannan ba shine abun da nake nufi ba. Ka/ki na iya cewa misali insha Allahu zanyi kokari naga ta hanyar kaza...kaza...kaza zanyi kaza...kaza...kaza da zai samar wa da mutane kaza...kaza...kaza.

A takaice ba fadar cewa zanyi kaza ba amma yaya zakai kaza din?

Ni musali in Allah ya yarda in ina da hali zan ga na samar da wata Gasa ta yara yan firamare da sakandare wanda ya samu nasara zan dauki nauyin karantunsa (In ina da hali). In duk Shekara mutum daya attajiri a kano zai dauki nauyin yaro daya da karatunsa, kuma in ace duk shekara an samu attajirai dari sun yi hakan, bayan shekara goma, an samar da mutum 1000 masu ilimi kuma hakan zai taimakemu da izinin ubangiji. Idan ko wane attajiri zai dauki nauyin mutum biyu kuma dauk shekara a samu atajirai dubu....kuyi lissafin.

Bissalam
ny good thing I said is from Allah and any bad thing I said is from me...So I ask for Allah's forgiveness for my errors both conscious and unconscious ones...Ameen!!!