News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

santi

Started by baby_gal_84, May 30, 2003, 10:25:22 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 2 Guests are viewing this topic.

IBB

There is this my flatmate he always does santi. But the funny thing about his is, he always either says; when ever he takes 2-3 spoons 'I have never eating food like this in my life (Tinda nake 'a rayuwa ta ban taba cin abinci irin wannan ba) or Your wife is in trouble (Kai IBB matar ka ta shiga uku)
IHS

thegood

always believe in w't you do

amira

Quote from: thegood on October 10, 2007, 10:17:06 AM
Bari in baku wani labarin santi da wata sister tayi muna cin freesh fish pepper soup kuma lokacin buda baki ne, bayan kowa ya dukufa yana fama, sai kawai ta ce in tambaye ku mana. sai muka amsa mata cewa Allah yasa mun sani. Budar bakinta ke da wuya sai tace amma wannan kifin ba a samun sa a kowane irin ruwa ko?  ;D sai duk muka kwashe da dariya.
Quote from: waduz on October 16, 2007, 09:17:39 PM
Wannan santin nina tafka shi, amma dai ya koya man hankali dan friends din basu man da wasa ba! Wato a wajen aikinmu aka gina mana sabon ofis. Ran da muka shige sabon ofis din da karfe sha biyu muka fito break. Da ma mu biyar ke taruwa kullum mu ci lunch mu koma aiki. To, a rannan dai, an hau kan su shinkafa da salad ana ta faman ci. Da cokali cike a hannuna, sai na daga kai na dubesu na ce, "yau fa mun koma sabon ofis din mu." Shegu, sai suka yi shuru kamar ba su ji abinda na fadi ba. Sai can wani daga cikinsu ya ce, "shago!" Aka tuntsure da dariya, har na tashi ina zaginsu na shiga daki. ;D
Quote from: IBB on October 19, 2007, 06:48:02 AM
There is this my flatmate he always does santi. But the funny thing about his is, he always either says; when ever he takes 2-3 spoons 'I have never eating food like this in my life (Tinda nake 'a rayuwa ta ban taba cin abinci irin wannan ba) or Your wife is in trouble (Kai IBB matar ka ta shiga uku)

Tafdijan ana buga santi kuwa lol ;D ;D ;D
*Each day is definately defining me and finding me*

sadiq

Tafdijan ana buga santi kuwa lol ;D ;D ;D
[/quote]

Atleast theirs was without their 32 out. lol!!
oday s beautiful moments are tomorrow s golden memories.

Nuruddeen

Wannan thread din kam lallai azimun ne ya kamata muyi santi.Hmm su Baby gurl manya. To bari na baku labarin mallam Lamiri mai gani har hanji da abokinsa Usman. Mallam ya gaiyaci usman gida suyi sallar magriba a masallacin kofar gidan sa dake kofar na'isa. Bayan sallar magariba Lamiri yasa aka kawo musu abinci, towon Dawa da miyar Kuka, tasha man Shanu. Koda Usman ya yanka lomar farko sai ya kada baki yace: Shin Gafarta mallam, ni  ina ga kunce ba wani abu da Allah baiyi bayaninsa a cikin littafinsa maigirma ba, wato kur'ani.Mallam ya dube shi yace TABBAS, gaskiya ne. Usman da man shanu ya buge shi sai yace shin alagafarta mallam ko Allah yayi bayanin MIYAR KUKA acikin Kur'ani kuwa. Lamiri ya zaburo ya sunkuyar da kai yace: KWARAI da Gaske. Ga ayar nan ta kur'ani da Allah yake cewa: WATARA  KUKA KA'IMA....
Usman ya gyara zama yace lallai kam wannan gaskiya ne. LOL!!!
o try and fail is atleast to learn. That will save one the inestimable loss of what might have been (positive or negative).

IBB

IHS

amira

Quote from: Nuruddeen on October 20, 2007, 08:44:09 PM
Wannan thread din kam lallai azimun ne ya kamata muyi santi.Hmm su Baby gurl manya. To bari na baku labarin mallam Lamiri mai gani har hanji da abokinsa Usman. Mallam ya gaiyaci usman gida suyi sallar magriba a masallacin kofar gidan sa dake kofar na'isa. Bayan sallar magariba Lamiri yasa aka kawo musu abinci, towon Dawa da miyar Kuka, tasha man Shanu. Koda Usman ya yanka lomar farko sai ya kada baki yace: Shin Gafarta mallam, ni  ina ga kunce ba wani abu da Allah baiyi bayaninsa a cikin littafinsa maigirma ba, wato kur'ani.Mallam ya dube shi yace TABBAS, gaskiya ne. Usman da man shanu ya buge shi sai yace shin alagafarta mallam ko Allah yayi bayanin MIYAR KUKA acikin Kur'ani kuwa. Lamiri ya zaburo ya sunkuyar da kai yace: KWARAI da Gaske. Ga ayar nan ta kur'ani da Allah yake cewa: WATARA  KUKA KA'IMA....
Usman ya gyara zama yace lallai kam wannan gaskiya ne. LOL!!!

Ai lallai  ;D ;D ;D
*Each day is definately defining me and finding me*

thegood

always believe in w't you do

waduz

Wani ne ya kafa rumfa a cikin gidansu lokacin babansa ya tafi gona. Da tsoho ya dawo ga yunwa ga kishin ruwa daga gona, gashi kuma ya gaji sosai sai ya zauna cikin rumfa. Aka kawo masa tuwo da miyan kuka, ya fara ci, hankalinsa na dawowa jikinsa. Can sai ya daga kai sama, ya ga ashe a cikin sabuwar rumfa ne ma ya ke zaune! Sai ya kwala wa dansa kira. Da zuwan dan yace masa, "kai yaushe aka yi wannan rumfan?" Sai dan ya ce, "wallahi baba, inna ce ta ce ba wajen shanya ganyen kuka, shi ya sa na mata inda zata rinka shanya wa!" ;D

thegood

Kasan kuwa in an shaya kuka ta sha rana tafi dai sosai, mutum har sai ya manta da sunan sa.......
always believe in w't you do

sadiq

Quote from: thegood on October 24, 2007, 12:21:31 PM
Kasan kuwa in an shaya kuka ta sha rana tafi dai sosai, mutum har sai ya manta da sunan sa.......

Sink zis one is ours too Kauyus, or what do you sink? Ip not, how did he get to know za sekerate
oday s beautiful moments are tomorrow s golden memories.

waduz

Quote from: sadiq on October 24, 2007, 12:54:36 PM
Quote from: thegood on October 24, 2007, 12:21:31 PM
Kasan kuwa in an shaya kuka ta sha rana tafi dai sosai, mutum har sai ya manta da sunan sa.......

Sink zis one is ours too Kauyus, or what do you sink? Ip not, how did he get to know za sekerate

A yu seying zat olli kauyus dirink miyan kuka? filis sink agen, kuka fa is unibasal.

Dan-Borno

live - ebin yesterday i have taken a handful of it,
i heard zat it cures so many ailments, especially
the long-age disease - yunwa-heatis  ;D
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

Lawwali

SANTI is sweet in itself you ill do it without knowing that you did. i spent my night in my boss' house.Today, when i woke up i was accorded a befitting breakfast and i was given a soap to bath. in the cause of my bath iwas tempted to sneak out with the soap for i enjoyed every bit of my bath. i forgotten that santi can be done by feeling. i asked my boss the name of and whwre he bought that soap. it is when he laughed then i realised i had done santi.
it takes oppressed and oppressor for oppression to occur

waduz

Wai ana zaune ana ta hira da abokai. Can sai aka fito da abinci, kuma shinkafa da wake da man shanu da yaji. Aka hadasu aka garwaya, mai ya ratsa ko ina, sai ci! Can anyi shuru anata hadiya, sai wani ya tunada wani bakon da yazo jiya da akaci abinci dashi. Ba tunani kawai sai yace, "amma bakon jiyannan dan sarauta ne ko.?" Can sai wani ya bashi amsa, yace, "aiya baka sani ba ashe, ai dan sarkin damawake ne." ;D