News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

santi

Started by baby_gal_84, May 30, 2003, 10:25:22 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 2 Guests are viewing this topic.

Dante

Ramadhaan Kareem,

Wow, after searching and some clicks i finally found this lost topic!

_________________________
Gaskiya tafi komai..........هو الذي

bakangizo

So u found it. What happen? Kayi santi da sahur ne, ko da buda baki? Gaya mana!

gogannaka

Quote from: Bakan~Gizo on August 27, 2009, 06:28:16 PM
So u found it. What happen? Kayi santi da sahur ne, ko da buda baki? Gaya mana!

LOL,gaskiya kam.
Har yanzu dai baá san sunan santi da turanci ba.
Surely after suffering comes enjoyment

Jibo

Quote from: gogannaka on August 28, 2009, 12:14:14 AM
Har yanzu dai baá san sunan santi da turanci ba.
Tofa! Ina turawan gidan nan!Shin wannan na cikin al'adar bature yayi santi? In akwai a al'adarsa to za'a sami kalmar santi a turanci!
Wa ya taba cin Doya da 'blueband'?
A lazy youth is definitely a begging adult! Bata hankalin Dare ka yi suna!: Fas'alu ahalil zikri, inkuntum la ta'alamun!

gogannaka

Jibo yam with butter or margarine is sweet.
You should spread the margarine over hot boiled yam. It is sweeter when you season the yam with a lot of pepper.
Har ka sa yawu na ya tsinke.
Surely after suffering comes enjoyment

HUSNAA

Quote from: gogannaka on August 28, 2009, 12:24:11 PM
Jibo yam with butter or margarine is sweet.
You should spread the margarine over hot boiled yam. It is sweeter when you season the yam with a lot of pepper.
Har ka sa yawu na ya tsinke.

Hahaha GGNK kenan. Konline's professional chef ;D ;D ;D ;D ;D ;D

How about doya da manja? It is tasty and healthier than margarine. I like yam fried into crispy wafers and eaten with lots of pepper. yummmy
Ghafurallahi lana wa lakum

bakangizo

Quote from: gogannaka on August 28, 2009, 12:24:11 PM
Jibo yam with butter or margarine is sweet.
You should spread the margarine over hot boiled yam. It is sweeter when you season the yam with a lot of pepper.
Har ka sa yawu na ya tsinke.

Kai wannan wane irin kwamacala ne, butter da pepper ::)

waduz

#127
Goga mai bakin taba romo! Kai ashe dai akwai masu kwadayi da yawa nan. Goga, ko ka taba cin burodi da kwakwa? Wayyo dadi! Ai kana taunawa wallahi sai ka ji wani dan mai mai na fita kana hadiya ba ko shan ruwa! Dan Allah ka gwada ka bani labari.....

Husna, da alaman kina san yaji sosai. To, sai ki sami dan yajin ki hada da mangyada da dan gishiri daidai. Sai ki sami kosai, ko takalallabi, ki dinga dangwala kina ci! Har kunnenki sai ya motsa ba baki kawai ba!....

Jibo

Haka ne goga doya da margerine sai wanda ya gwada!
To amma gasasshiyar masara da kwakwa mai zaki fa?!
A bani labari! ;D ;D
A lazy youth is definitely a begging adult! Bata hankalin Dare ka yi suna!: Fas'alu ahalil zikri, inkuntum la ta'alamun!

gogannaka

QuoteHow about doya da manja? It is tasty and healthier than margarine. I like yam fried into crispy wafers and eaten with lots of pepper. yummmy

Abun mamaki ban taba cin doya da manja ba.Abincin yan boarding school kenan.
An ce yana da dadi but ni manja na kama min makwogwaro musamman irin fake manjan da ake sayarwa yanzu.

QuoteKai wannan wane irin kwamacala ne, butter da pepper

@ BKGZ,ka gwada ka bani labari. Kwamachala ai sai sakwara da ketchup ko jallof da miyar kuka.

@ waduz wacce irin kwakwa? Kwakumeti ko kwakwa zalla? I love coconut bread sha.
Surely after suffering comes enjoyment

waduz

Goga, ai kwakwad da ka sani ake sayarwa, mai fari a ciki. Ka saya ka na gutsura da burodi. Ai wallahi in baka yi hankali ba, ka sahur da komai kenan! ;D

IBB

Ga wani jukon. Garin kwaki da kuli-kuli mai yaji (irin kulikulin nufawa).

Ina yan boarding? Waya taba cin kwadon-kanzo
IHS

bakangizo

IBB, da alama kana cikin irin masu shan koko/kamu da kulikulin nufawa.

IBB

Wannan bani da labarin sa Ale Gizo. Bamu mu sha, kaga ma gwada
IHS