News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

Kira ga matasan Arewa

Started by Anonymous, August 05, 2002, 02:16:21 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Anonymous

Assalam Alaikum yanuwa,
Abin bakin ciki ne ga duk mai kishin kasa, ganin irin halin da kasarmu Nigeria ta shiga a wannan zamani.
Gaskiya, rukon amana, da yarda duk sun zama sai a tarihi.
Ba sai an bayyanawa duk wanda ya ba ashirin baya ba, irin yadda halin rayuwa gaba daya ya tabarbare.
Ni a ganina babu abun da ya jawo mana shiga wanna hali sai rashin kyakkyawar niyya. Domin duk abun da za ka aikata idan ba kyakkyawar niyya to fa ba zai yi kyawon karshe ba.
Kiran da zanyi, awannan lokaci na karantowar zabe, ga yanuwana ne matasa, da ayi hattara. Duk wanda ya dauki alkawarin zaiyi wa jamaa aiki, to fa ya cika.
Kada mulki ko kudi ya rudeka/ki ka cuci talakawan da suka zabe ka/ki. Mu lura cewa fa tun a duniya Allah yana nuna mana ishara. Dayawa wadanda giyar mulki ta hau kansu yanzu muna ganin yadda suke karewa. Ko basu tozartaba a duniya, ai mutuwa na nan. Kuma wallahi duk gafarar da Allah zai yi maka/ki ta abunda ke tsakanin ka/ki da shine. Mutanen da ka/kika zalunta sai fa an saka musu.
Mu hada kai don gyarar kasarmu domin kuwa bamu da wata kasar da tafita.
Kuhuta lafiya, wasalam naku,
Suleiman.

dayyabs

Assalamu Alaikum Suleman,
Naji dadin wannan bayani naka amma kar in katse maka hanzari, a gaskiyar lamari, abin daya cuci matasa 'yan arewa shine jahilcin addinin mu. Kuma Allah yana cewa bazai canjawa al'umma ba har sai sun canja halayen su. Babu amana, gaskiya, taimakwan juna kai kowa kansa ya sani, kaga kuwa bazamu ga daidai ba har sai munyi yi kanmu kiyamullaili.
Kuma wani abin bakin ciki ma mafiyawancin matasanmu  zasuyi biyu babu domin babu duniyar balle lahira. Saboda haka;- ( Aword is enough for a wise ). :o

Anonymous

Assalamu Alaikum

Lalle kan duk abubuwan da aka fadi a baya dangane da tabarbarewar lamurra a Nigeria musamman ma a Arewa gaskiya kuma babu wani kokwanto cikin haka.

A hakikanin gaskiya rashin kishin kasa, handama, rashin tsoron Allah da kuma rashin dan adamtaka sune suka sa shuwagabanninmu suka mance da kowa sai dai kansu kawai, su ke zaluntan al'umma da kuma shan jininsu. Lalle akwai babban kalubale a kan mu matasa da mu gyara kanmu, kada mu yi koyi da wadannan shuwagabanni masu son kansu kawai.

Maasalam

Awwal

Anonymous

Assalamu Alaikum.
Naji dadin yadda yan'uwa suke nuna yadda Al'amurra suka kasance a Arewa, amma ni a ganina gaskiya tabarbarewar halayyar mu yan Arewa ta samo asaline daga wadanda muke bi a yanzu.
Amma a  nawa tunanin sai mu matasa na yanzu mun kyamaci abin da manyanmu na yanzu sukeyi na nuna halin ko oho ga arewa.
Misali: A yau bamu da wani shugaba da ya amsa sunan shi shugabane kamar yadda SIR AHMADU BELLO Sardaunan Sokoto ya amsa sunan.
2.Rikon da yan mazan jiya suka yima Arewa yasha bamban da rikon da yan arewa suke mata yanzu, don yan mazan jiya Arewar ce a gabansu ba tara abin duniyaba (Zaria ramin kura dagake sai yayanki).  ::)

Anonymous


amira

gaskiya these days ba'ayin abubuwa tsakani ga allah because people these days just think about theirselves,
there are so many problems in nigeria, gosh its soooo sad when you see things happening and cant do anything about it,
wai i dont understand dont people want nigeria to move forward ne or wat ko kuma basa gani ne?????
am not saying its all the people of nigeria cos obviously there are people that want nigeria to move forward,
one example ribadu him and his people are doing there best to combat this corruption that is eating nigeria,
but on the other hand there are sum mindless people that want to stop him from doing his job, don allah meye haka.
*Each day is definately defining me and finding me*

Muhsin

Thank you for this good post.
Allah ya bamu ikon sanin gaskiya da kuma binta.
Get to know [and remember] Allah in prosperity & He will know  [and remember] you in adversity.

amira

To amin muhsin, don abin nigeria ya wuce gona da iri kullum tana cikin problem gaskiya matsaloli sunyi yawa a wannan kasar, kuma mutane ke kin gaskiya don inda anayin things sakani ga allah things will be going well for the country amma greed has taken over, cos ppl are just thinking bout theirselves. wallahi abin tausayi ne ganin naija a wannan halin wen i kno nigeria can do soooooo much better amma fa its cos of the corrupt ppl that don't want it to move forward because they are the ones that are eating wat is not theirs. :cry:  :(
*Each day is definately defining me and finding me*

Sani Danbaffa

Gaskiya ne jama'a. Amma mu duba dukkannin mu mu fara daga gidajen mu da kawunan mu. Ina tsammani lalatar ta faro daga 1970's sanda rashin da'a ya shigo Arewa da sunan 'yanci. Na tuna a da in ana zanga zanga, akan yi ta cikin lumana. Haka idan za ayi wani abu shugabanni sukan sanar ana kuma sauraron su. In shugabanni suka fito ana ganin darajar su kuma ana so a gan su a ji abin da sukan fada! Gen Yakubu Gowon, da gwamnonin sa musamman su Audu Bko (Allah ji qan sa) da abokin sa na Mid West Diete Spif? an so su qwarai, kuma har yanzu aikin marigayi Audu Bako na ciyar da jihar Kano.

A gaskiya ya kamata iyaye su tuna baya kuma su farfado da da'a mai kyau da ake da ita a Arewa tun da can. Allah ji qan Gen Hassan Usman yana daga cikin wadanda suka rage ake jin maganar su kuma ba sa neman komai daga kowa.
Seek knowledge to be usefull to the society, help and spread happiness.

Rais

Quote from: amira on August 11, 2006, 01:42:49 PM
gaskiya these days ba'ayin abubuwa tsakani ga allah because people these days just think about theirselves,
there are so many problems in nigeria, gosh its soooo sad when you see things happening and cant do anything about it,
wai i dont understand dont people want nigeria to move forward ne or wat ko kuma basa gani ne?????
am not saying its all the people of nigeria cos obviously there are people that want nigeria to move forward,
one example ribadu him and his people are doing there best to combat this corruption that is eating nigeria,
but on the other hand there are sum mindless people that want to stop him from doing his job, don allah meye haka.

Gaskiyanki yanzu Nigeria sai a hankali inkace kanaso kanuna halin mazan jiya yanzu za ai destroying din ka wallahi, yazama "GANI GA WANE " saidai Allah ya taimakemu yabamu ikon rike imaninmu Amin sannan mikokari muyi ma diyoyinmu tarbiyya nagari.
Bayan Mutuwa akwai hisaby