Saye

Started by Ahmed.WANG, December 23, 2008, 11:32:16 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Ahmed.WANG

Saye watau kin kiran abu da sunansa ta hanyar sayawa a yi amfani da wasu kalmomi daban amma da ma'ana iri daya.

Misali: A wajen haihuwa, akan ce "Ta sauka" ko "Ta rabu lafiya".
         A wajen mutuwa, akan ce "Ya riga mu gidan gaskiya" ko "Ya kai takarda".
         Da ka ce "cin kwan makauniya", kana nufin ba ji ba gani.
         Idan an ce wani "mai dogon hannu" ne, ma'anarsa barawo ke nan.

Akwai sauran misalan da ka/ki san su?