News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

hauka ko jahilci?

Started by Dan-Borno, March 17, 2010, 02:04:50 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Dan-Borno

musulunci ya koya mana yanda zamu gudanar da rayuwarmu
na yau da gobe, kuma al-qur'ani mai girma tare da hadisan
manzon tsira sun fayyacemana wadihan rayuwar zamantakewa
tsakanin uwa da uba, yaya da kani, makwabci na kusa da
kuma makwabci na nesa, tsakanin musulmi da wanda ba
musulmi ba, amma kash, lamarin ya juye.

an wayi gari mu musulmai mune muke da rauni wajen harkar
mu'amalar mu da yan'uwanmu musulmai.

dalilin kawo wannan shimfida ba wani abu bane face wani labari
da na samu wanda ya zamo mini abin bakin ciki.  labarin itace
shekaranjiya aka yi wa wani dan taxi kisan wulakanci a cikin
birnin kano abisa dalilin da ba a fayyace gaskiyartaba, kai, daga
baya ma an tabbatar cewa lamarin ba haka bane, he is innocent.

bayan an yi masa kisan walakanci wanda addinin musulunci bata
yarda da shi ba, aka kona motarsa kirar golf sa'annan kuma aka
yanke mai kai aka dora a kan motar - wanda akayi wannan abin
agabansa shine yabani labarinnan.

makasudin wannan labarin ba wai don anyi wannan lamarin a kano
ba, a'a, sai dai irin halin da mu musulmai muka samu kanmu a
ciki, maimakon mu rika duba tsari irin wanda musulunci ya zayyana
mana sai mu rika amfani da son zuciyoyinmu. 

musulunci ya tsara yanda za a hukunta mai laifi, kuma dole sai an
tabbatar masa da laifinsa da shaidu, kuma ko kisace, ai musulunci
ta tanadar hanyar da za abi ayi hukuncin kisa din.

nasihata zuwa ga al'umman musulmai shine, a ji tsoron Allah kuma
a rika yin bincike ayi hattara da kece haddin yan'uwa ko abokan
zama.  duk lokacin da lamari ta taso, yana da kyau a rika kai kara
zuwa gun malamai da sarakuna ko kuma akai wa hukuma ta dau
mataki amma ba wai mu mu dau fansa ba - lallai wadanda suka
aikata wannan mummunan aiki wa dan taxi sun aika laifi mai girma
kuma muna fatan Allah zai gafarta musu.

hauka ko jahilci?
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

HUSNAA

Iskanci ne da Jahilci DB. Lokacin da abin bai tsanani ba, ni ina kan wannan titin da abun ya faru ina tuki na fito da BUK goshin laásar. Sai gamu mun shiga wani dan karamin go-slo; ashe wannan abin alajabin ne. Muna tsaye sai na ga wani da gudu  ya yanko da ga bangaren titin inda motoci suke nufar BUK, yana rike da wani zandamemiyar pipe na karfe. Yana zuwa gaban legal (school of Legal studies) sai ya rotsa wannan pipe din a kan wani machine ne ko moto bike. Sai wani dake  biye da shi a baya shi kuma da itace ya fara kururuwa wai Wallahi a barsu su kashe shi. Ni dai sai nace tayar mota mai naci ban baki ba? Wa yansu ma har sun fara yin Uturn  a daya lane din suna koma wa baya. Ni dai addua na ke yi Allah Ya fidda mu da ganan wurin kada wata masifa ta ritsa da mu. Da Allah kuwa Ya Bamu Saá muka kutsa kai cikin hargitsin motoci sai na sha kwana na  yi gaba. Da ga baya ne na ruka jin labarin kissar da akayi a wurin.
Haka ma kwanankin baya wata tsohuwa Allah Yayi mata gyadar doguwa,. Yan acaba suka tsai da ita da suka ganta da jariri a goye, suka ce wai sato yaron tayi. Su kai mata dukan tsiya za su kashe ta, sai wani bawan Allah yana shigewa, ya gano wannan aikin ta asa din sai ya sa baki.  Ya ceci tsohuwa, aka tambaye ta daga inda take. Sai tace ai yaron jikan tane. Sai su yan acaba suka ki yarda suka ce sai ta  nuna masu  inda ta fito. Tsohuwa a ka tasa ta gaba da ita da jariri aka je har unguwar su. Sai ta ce gidan su a lungu ya ke sai suka ki barinta ta shiga lungun, wai a cewar su in ta shiga lungun, bace wa zatayi. Sai suka kira mutanen da ke wurin suka rika tambaya wai ko ansanta. Da yake ba harabar gidansu bane, sai ba wanda ya shaida tsohuwa. Sai yan acaban dan suka yinkuro wai su sai sun zartar da hukunci nan take. Allah Dai Ya Taimaki tsohuwannan yan sanda suka karbe ta a ka tafi da ita Police station a ka far bincike. Da yake in an yi irin haka a unguwa kowa da kowa sai ya ji, sai uwar yaron da wannan tsohuwa ta goya ta ji labari, mijinta ya je police station a ka bailin din tsohuwa. A she da gaske ne jaririn jikan tane, kuma wai yaron an haife shi ba ya kuka, kuma uwar ba lafiya. Sai aka basu shawara wai akwai wani mai magani a  wata unguwa, sai kakar yaron ta ce ita bara ta kai shi tunda yar tata ba lafiya.  Shine a kan hanya yan acaba su kai mata wannan kazafin kuma su ka kusa kashe ta. Shi jaririn kuwa dalilin wannan abun da yafaru bai rayuba sai mutuwa yayi kafin a je gidan maganin.
Yan iska ne su kayi yawa a Kano. Shugabannin na mu na kano wai suna maraba da kowane dan acaba da aka koro da ga wata jiha, wai ai su a wurin su, karin jamaa albarka ce. Basa la akari da cewa, wace irin jama a ke shigowa cikin birnin Kano a kullum.
Ghafurallahi lana wa lakum

amira

Gaskiya those yan achaba basu kyauta ba for doing what they did to the old lady,
Shes an old woman for goodness sake, wannan bugun ma can lead to her death
kai wannan rashin mutunci da imani na mutane is too much. However i dont blame them
Why?
Bcos its become a norm in nigeria now that people are going round snatching/Stealing kids
even adults and killing them a wulakanche , u cant trust anyone these days its terrible.

Though they shudnt have dealt with her the way they did, they should have spoken to
her and relate there questions, so that she can answer them. If its true that the baby is her jika then
no problem let the women be on her way, and if not take her to the police station where the matter
would be taken further.
The old woman should demand for compensation it aint right what they did.............................

*Each day is definately defining me and finding me*

gogannaka

Ai akwai jan aiki a Kano.
Muna tafe ne sakaka kowa baya son a fadi gaskiya.
An riga an raina gwamnati (da taimakon gidan rediyo freedom). Idan an yi magana sai ace ai kowa na da 'yanci ya fadi ko mai ya ga dama.
Ba sau daya ba sau biyu ba an sha bawa gwamnatin Kano shawara( har a nan forum din) da ta duba sana'ar achaba a garin Kano,if not for the pollution then for the nuisance they have become but me aka yi? Hana karya dai an kafa 'committee' da suka yi rajistar yan achaba,kuma sun gano cewa akwai yan achaba miliyan uku a Kano.
They have really become a nuisance just like Yan daba once become a nuisance to the state.
Yanzu idan dai har kana tuki to ba abun da kake tsoro irin sharrin yan achaba.
What happened regarding the taxi driver is condemnable. It is not only the okada's that were at fault har da masu zaman banza a unguwa.
It is sheer barbarism.
The whole problem is a societal problem and i'm afraid it might be too big for the government to handle now.
Na farko dai wadannan yan achaban yawancin su almajirai ne da suka baro iyayen su tun suna kanana therefore basu san wani abu wai home training ko dicipline ba.
Na biyu kuma sana'ar tana kawo musu kudi masu yawa and they feel independent.Nothing to loose.
Na uku kuma ga yawaitar shan kwayoyi,wee-wee(according to the NDLEA Kano has the largest consumption of indian hemp) da hade hade iri iri wanda suke saka maye ko kuma karfi a jika.
Na hudu kuma kamar yadda Husnaa ta fada, gwamnati tana maraba da sana'ar achaba saboda tana ganin cewamutane suna samun aikin yi.

To aikin yi dai idan ya kunshi kashe innocent souls and being a nuisance to the society then ban ga amfanin shi ba.
The government should act now before it is too late (honestly its too late but it is better late than never). The government has to be strong on this one and the officials should know that for every life lost to these miscreants,they have a share of the blame.

The Kano state govenment need to show the people that it can exert its authority on anyone.
They don't have to ban achaba outrightly. They can set up an Okada management agency just like lagos did LASTMA.
A kafa dokokin da zasu yi guiding sana'ar sannan kuma a tabbatar ana bin dokokin.
Money should not be a problem because the agency can take care of itself from the revenue.
A rinka karbar N100 from them daily.
N100 X 200,000 okadas daily = N20million daily
N20million X 30 days = N600million monthly
N600million X 12 months = N7.2billion naira from achaba kawai.
Surely after suffering comes enjoyment

HUSNAA

an raina gwamnatin kano? well of course an raina ta mana!! Gwamnatin da kwamishinonin ta za su handame kudi wai sai gwamnaan yayi musu Allah Ya Isa kawai, how can u take it seriously? Gwamnatin da wai tana gyare gyaren titi amma ba tsarin yadda mutane za su yi tafiya kan hanya? Go slo ya cika gari  shara ta cika gari sace sacen mutane ya cika gari, daukar doka a hannu ya fara zama ruwan dare etc etc. Yet gwamnati bata fito wa tai komai sai dai tace wai mutane su cigaba da yin addua Allah Ya Tsare mu daga sace sacen mutane?!!!!!!!!!!!!!!!
I am a strong believer in addua da kariyar ubangiji. Amma wanda Allah Ya Baiwa wuka da nama (i.e. mulki) da kuma ikon zartar da hukunci da bincike don a da dadawa al umma wajen walwalar zaman gari, ai bai kamata ya ce kurum mutane su yi addua ba, sai ya fada wa mutane matakin da gwamnati ke dauka wajen warware wa yannan ta asa da ake yi a gari  ba kunya ba tsoron Allah sannan kuma sai ya ce wa mutane su cigaba da addua don Allah Ya Kawo saukin abun. Gaskiya I am not happy with gwamnatin Kano. It is doing less than it should especially when u juxtaposition it with what Lagos state is doing presently. That is why I applauded heartily when Sanusi Lamido Sanusi in his opening speech at the preconvocation lecture at BUK appropriated Lagos as his state when he saluted Raji Fashola as ''the governor of MY state, Lagos'', while he saluted the kano state gov as just that the governor of kano state.
Ghafurallahi lana wa lakum

Dan-Borno

naji dadin maganar abokina gogannaka da kuma labari
da karin bayani da shugaban matan arewa na kanoonline
tayi.

lallai lamarin yan achaba ayi tsamari amma kuma ina son
mu fahimci cewa gwamnati bazata iya yin wani abuba a
halin da ake ciki yanzu, dalili kuwa shine;

a borno, musamman doka a tsara a shekaran 2008 saboda
ya baiwa yan achaba sense of direction, daga cikin dokan,
gwamnati ta
1.  wajabta sa hulan kwano
2.  daina yin achaba daga karfe 7 na yamma
3.  sa uniform
4.  yin register a ko wace unguwa
5.  daina goyon mutum fiye da guda daya
6.  daina kunce salansar mashin
7.  babu gangami fiye da yan achaba guda biyu
     etc

kuma gwamnati ta dora kotuna a kan titi wato (mobile court)
saboda duk wanda aka kama sai a ci taronsa a nan take.

wane mutum, yan sanda suka nuna cewa enforcing din wannan
dokan tafi karfinsu saboda rashin enough manpower.  daga nan
sai gwamnatin jahar borno tayi mandating din kungiyar sojojin
kawance ta musamman mai suna operation flush II su tsaurara
mataki kuma su tabbatar cewa kowani dan achaba ya bi doka
da oda.

karshen labarin dai, komai ya tafi dai dai, saboda ko kabi doka
ko kuma soja yayi maka dan karen duka har da tsallen kwado,
wannan lamarin yayi wa mutanen gari ciwo saboda a hali irin
namu na yan arewa ba mu son bin doka da oda.

dama komai akeyi, dole a samu casualties, aka dan samu wasu
kura kurai amma a gaskiya an samu lafiya matuka a cikin garin
maiduguri saboda wannan doka.

daga baya dai sai mutane suka fara kuka, infact aka mayar da
lamarin zuwa addini, a ka matsa wa mai girma gwamna har a
wajen taron tafsiri na shekara shekara da kuma yawaita samun
sammaci daga kotu daga gun lauyoyi, sai gwamnati ta janye
sojojin operation flush daga kare wannan dokar.

yau, lamarin kamar ba a taba yin hular kwano ba, infact, idan an
ganka da hular kwano, yan achaba sai suyi maka dukan kawo wuka.
daukan mutum biyu kuma sai yan koyo, amma turmi a keyi yanzu
a kan mashin. babu uniform, babu lokacin aiki - amma kuma sace
sace ya dawo, rashin kunya kuma dama kamfaninta ne, asibiti
tun tuni ta bude ward din yan achaba sa'annan kuma gawa na
dan achaba its on everyday basis.

lamarin yana bukatan jama'a suyi aiki tare da gwamnati, lokaci
yayi wanda malaman zaure zasu fahimci cewa bawai fatiya kawai
ne aikinsu ba, lallai hakki ya rataya a wuyansu su fadawa
gwamnati gaskiya kuma su jagoranci jama'an da ke karkashinsu.

dole a hada kai a yaki jahilci da hauka.

jumu'at mubarak
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

gogannaka

Husnaa,ke kin ji da kunnen ki lokacin da shekarau yayi wannan Allah ya isan ne ko kuma a freedom radio kika ji?
I remember Shekarau handed over officials of the state's board of internal revenue to the EFCC so i don't want to believe that he is that slack on his commissioners. He also removed the former Agric commissioner,Rogo when allegations were much on him.
I don't want to believe he is that soft on the commissioners.
The bulk of the problem lies on the people of Kano state.
We love trading blames on the government and the Governor in particular.
I agree his methods of exertion of authority is weak and i am sure if he brings out his sharp sword he would be criticized for being dictatorial kamar yadda aka rinka yi wa kwankwaso.

So bakane ba'a mai daidai.
The sooner we change our attitude the better idan ba haka ba we will be worse than where we are now.
The abuses and what have you in the radio will NEVER help the state in anyway.
Duk alummar da bata ganin shugabannin ta da mutunci to alumma ce mara mutunci.

Regarding the roads that the government is building, i know for sure that access roads have been temporarily provided to ease access.
You cannot expect free flow of traffic when a central and strategic metropolitan road,like ibrahim taiwo road,zoo road or BUK road is reconstructed. There has to be inconvenience for a while. I am even quite impressed with the pace of execution.
A lagos da muke ganin babu inda ake aiki kamar nan,the govt decided to re-do the drainage system of Victoria Island. Har yanzu da nake magana ba'a gama ba and it started since around august last year. Dama chan ya aka kare da 'go-slon' VI ballantana yanzu da aka rufe tituna da dama. It is chaotic amma the people of lagos never complain because they know it is done for their own benefit.
When the third mainland bridge was closed, who did u hear complain?
Amma mu kawai sai dai muyi cirticizing gwamnati a rediyo and kuma a zo a rinka justifying.

The okada problem is not just a problem the executive alone can handle.
The state house of assembly needs to come in.
Our politicians also need to come in and like DB said the malaman gargajiya that incite the public too.
The house should promulgate the law that will guide the achaba business.
The executive should uphold the law wholeheartedly and disregard all criticisms.
The politicians should henceforth stop distributing motorbike as dividend of democracy.

Just like they did in Borno,we should emulate. We should look at their own weakness and make ours stronger.
We should stop having the mentality that nothing can be done because 'tun ran ginin tin ran zane'
It is a current problem that if not tackled our children will not forgive us.
Surely after suffering comes enjoyment

Ibro2g

Quote from: HUSNAA on March 19, 2010, 08:53:41 AM
an raina gwamnatin kano? well of course an raina ta mana!! Gwamnatin da kwamishinonin ta za su handame kudi wai sai gwamnaan yayi musu Allah Ya Isa kawai, how can u take it seriously?


lol lol lol, I cant stop laughing, wai Gov na musu Allah ya isa, lol.
Well, as it turns out in our simplicity we have begotten our biggest difficulty. We do not believe in this law of the state, we seldom carry it out. Kano is the only place in Nigeria ma dat u'll find a Layin Alfirma and a very legitimate one at that. By God we claim to be modest but we are least disciplined in our attitudes and action. This is the result.

Shouldnt we be talking solutions? Like Goggs said about the Achaba union, shouldn't we not take the fight to our people. Wai sai ache Kano baza ta taba gyaruwa ba, or there are some scumbags that wouldnt let it happen, are they up to a million? in a population of wat 10 million? tsk wannan abu da ban haushi yake
Safety and Peace

Bashir Ahmad

Wannan ba komai bane illa jahilci da rashin tausayi, ko kadan wannan ba koyarwar addinin Musulunci bace, Addinin Musulunci bai ce mutum ya dau hukunci a hannunsa ba. Amma wadannan mutane sabida jahilci yayi musu yawa kawai basu tabbatar da laifi ba amma har suka dau hukunci da hannunsu ba tare da iznin doka ba. Tabbas muna goyon bayan ayiwa wadannan mutane hukunci daidai da laifinsu sabida masu tunani irin nasu...
Above All Fear Allah (S.W.A)