News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

Amurka Ta Yi Kiran Da A Cire Shugaban Hukumar Zabe Ta Nijeriya Maurice Iwu

Started by bamalli, April 06, 2010, 04:22:32 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

bamalli

Amurka Ta Yi Kiran Da A Cire Shugaban Hukumar Zabe Ta Nijeriya Maurice Iwu 
Marubuci Ibrahim Alfa Ahmed
06/04/2010
   
Wani babban jami'in diflomasiyya na Amurka ya ce ya kamata Najeriya ta maye gurbin shugaban hukumar zabenta idan har tana son gudanar da zabe na gaskiya ba tare da ha'inci ba a shekara mai zuwa.

Mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da nahiyar Afirka, Johnnie Carson, ya ce irin rawar da Maurice Iwu ya taka a zaben 2007 da aka kushe saboda magudinsa, ta isa a cire shi daga kan wannan kujera.

'Yan kallo sun ce an tabka mummunan magudi ta hanyar cika kwatunan zabe da kuri'un karya tare da cin zarafin abokan hamayya a zaben na 2007 a Najeriya.

Wa'adin Mr. Iwu kan kujerar shugaban hukumar zaben Najeriya, INEC, zai kare a watan Yuni na shekarar 2011, wata guda a bayan lokacin da ake sa ran Najeriya zata gudanar da zabubbuka na kasa.

Carson ya yi wannan magana kwana guda kafin Amurka da Najeriya su kaddamar da wata sabuwar Hukumar Tuntubar Juna ta Hadin Guiwa.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta ce kasashen biyu zasu yi kokarin fadada hadin kansu a fannoni da dama da suke da muradu guda kai, ciki har da kyautata mulki, da makamashi, da bunkasa samar da abinci da kuma tabbatar da tsaron yankin.