Author Topic: Hasashen sakamakon zaben gobe da abinda zai biyo bayansa:  (Read 5865 times)

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Offline Abu-Fatima

 • Full Member
 • ***
 • Join Date: Feb 2009
 • Posts: 52
  • View Profile
Hasashen sakamakon zaben gobe da abinda zai biyo bayansa:
« on: April 15, 2011, 03:18:33 PM »
(a) Gobe PDP zata lika jam’iyyar CPC, ACN da duk sauran jam’iyyun adawa da kasa, saboda taurin kai, sonrai da rashin kishin talakawa yahanasu hada kai. (b) Faduwar CPC a gobe zai hana jama’a fitowa zaben 26 ga wata, saboda kusan duk ‘yan CPC suna CPC ne saboda Buhari, don haka bazasu fito zabeba bayan gwaninsu yasha kaye. (c) Kin fitowar jama’a zaben 26 ga wata, zaisa ‘yan takarar CPC susha kasa, PDP tayi galaba. Gwamnoni irin su Ibrahim Shema zasu tsallake! (e) Bayan an kafa gwamnati, tsirarun ‘yan CPC da suka ci zaben majalisun tarayya a makon jiya, zasu sake sheka su koma PDP: dama akasarinsu tsoffin ‘yan PDP ne. (f) 2015 in Allah Yakaimu, lokaci Buhari yabar siyasa sai kuma muga abinda Allah zaiyi.

Offline bakangizo

 • Super Member
 • *****
 • Join Date: Apr 2005
 • Location: Kano
 • Posts: 1925
  • View Profile
Re: Hasashen sakamakon zaben gobe da abinda zai biyo bayansa:
« Reply #1 on: April 18, 2011, 08:14:19 AM »
Abin da ake gudu ya faru!!

Offline admin

 • Administrator
 • Super Member
 • *****
 • Join Date: Apr 2004
 • Location: Kano, Nigeria.
 • Posts: 650
  • View Profile
  • http://www.qs-corp.com
Re: Hasashen sakamakon zaben gobe da abinda zai biyo bayansa:
« Reply #2 on: April 18, 2011, 02:53:21 PM »
Allah ya banu zama lafiya.
To Amma a halin yanzu Kano ta kama da wuta ko ina sai kone kone, har da kashe kashe....

Mun samu labarin rashin zaman lafiya a Zariya, Kaduna, Gombe, Minna da kuma wasu ruraren...
Kaini Kano ko a buhun barkono!!!

Offline Abu-Fatima

 • Full Member
 • ***
 • Join Date: Feb 2009
 • Posts: 52
  • View Profile
Re: Hasashen sakamakon zaben gobe da abinda zai biyo bayansa:
« Reply #3 on: April 19, 2011, 09:00:22 AM »
Hakane. Abinda hasashenmu bai hangoba shine cewa samari da matasa zasuyi bore bayan sun fara jin sakamakon zaben. Abin takaici kuma shine hasashena na biyu dana uku sun kama hanyar tabbata, domin labari ya ishemu cewa a wurare da dama wasu ‘yan uwa sun fara bankawa katin zabensu wuta saboda wauta. Wanda ya kone katin zabensa ai tamkar ya burmawa cikinsa wukane kana ya daga hannu sama yana kirari.

 


Powered by EzPortal