Ina ganin lokaci ya yi da mutanen Kano za su lura da cewa wani muhimmim bangare na tarihinsu da kuma diyaucinsu na rugujewa a hankali.
Ganuwar birnin Kano na daya daga cikin manyan abeban tarihi na wayewar kan Bahaushe, amma ga alama mun yi watsi da ita muna ganin a idanuwan mu tana rugujewa.
Shin ba abin kunya ba ne a ce Turawa da suka ci Kano ba su rusheta ba, amma gata tana faduwa a gaban mu.
Kanawa lokaci ya yi da za ku sake yin sabon tunani akan makomar ganuwar birnin Kano.
In aneman ra'ayin jma'a!
Daga
Yusuf Adamu a Birmingham, Alabama.