Kira ga matasan Arewa

Started by Anonymous, August 05, 2002, 02:18:30 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Anonymous

Assalam Alaikum yanuwa,
Abin bakin ciki ne ga duk mai kishin kasa, ganin irin halin da kasarmu Nigeria ta shiga a wannan zamani.
Gaskiya, rukon amana, da yarda duk sun zama sai a tarihi.
Ba sai an bayyanawa duk wanda ya ba ashirin baya ba, irin yadda halin rayuwa gaba daya ya tabarbare.
Ni a ganina babu abun da ya jawo mana shiga wanna hali sai rashin kyakkyawar niyya. Domin duk abun da za ka aikata idan ba kyakkyawar niyya to fa ba zai yi kyawon karshe ba.
Kiran da zanyi, awannan lokaci na karantowar zabe, ga yanuwana ne matasa, da ayi hattara. Duk wanda ya dauki alkawarin zaiyi wa jamaa aiki, to fa ya cika.
Kada mulki ko kudi ya rudeka/ki ka cuci talakawan da suka zabe ka/ki. Mu lura cewa fa tun a duniya Allah yana nuna mana ishara. Dayawa wadanda giyar mulki ta hau kansu yanzu muna ganin yadda suke karewa. Ko basu tozartaba a duniya, ai mutuwa na nan. Kuma wallahi duk gafarar da Allah zai yi maka/ki ta abunda ke tsakanin ka/ki da shine. Mutanen da ka/kika zalunta sai fa an saka musu.
Mu hada kai don gyarar kasarmu domin kuwa bamu da wata kasar da tafita.
Kuhuta lafiya, wasalam naku,
Suleiman.