Tatsuniya Online (GIZO DA GOGI)

Started by IBB, March 27, 2003, 10:28:08 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 31 Guests are viewing this topic.

IBB

hey guyz how about tatsuniya online. eg Gizo da gogi. 'Yar

bora da 'yar mowa. ajebutters full here i dont know if una sabi

that one

gata nan kata nan ku, tazo mujita
IHS

sdanyaro

Assalamu alaikum;

This topic sounds very interesting. Can you please share with us one or more of the Tatsuniyoyin with us here? I think it is a good idea...

Twinkle

UNCLE SALIS, BA'A YI MAKA TATSUNIYA BANE KANA YARO? KO DAYAKE DUK BATA BACI BA IBB BAMU MU SHA.. BARI NIMA NA ZAUNA NA TANKWASHE KAFA YADDA UNCLE SALIS YAYI A BAMU MU SHA!!!!!!!!!!! ;D
color=red]I RULE IN A UNIQUE WAY!

[/color]
[/i]

Ihsan

IBB, ya ka fara abu kuma munji shiru??
To ni bari na bude mana filin ... ;)

Duk kun hallara? To madallah

Kunnen ku nawa...kara biyu ku sha labari... ;D

Gata nan Gata nan ku...

Gizo ne dai watarana yana tafiya, sai yaga wani katon sa! To shi wannan san girma ne dashi sosai wanda ko a shanun sarki babu mai girman shi. sai kuwa gizo ya tafi wajen Sarki yace mashi "sarki sarki kunnen ka nawa? sarki yace "biyu" gizo yace mashi "kara biyu kasha labari!!! yau naga wani katon sha!"

Gizo ya ja hanya suka tafi a ga wannan katon sa. Da aka je sai aka tarar wannan san na wata tsohuwa ne... akai mata dole aka ce sai an yanka shi!

Aka tambayi tsohuwa me take so a jikin san. Tace ita kayan ciki take so! Aka yanka sa, tsohuwa ta samu kayan ciki.

Tsohuwa ta kai kayan ciki gida ta ajiye har dai watarana suka zama 'yan mata masu kyawawa!

Sai watarana Gizo yana yawo sai yaga daya daga cikin 'yan matan!!! ay kuwa sai gaban sarki! yace "sarki sarki kunnen ka nawa? sarki yace "biyu" gizo yace "kara biyu kasha labari!!! yau naga wata yarinya kyakykyawa wadda ban taba ganin kyanta ba!!!

Aka ce to gizo ya ja hanya aje wajen da yaga yarinyar. Suka tafi da bafaden sarki zuwa gidan tsohuwa! Suka isa gidan aka ce ana Sallama da tsohuwa. Sai tsohuwa tace da daya daga cikin 'yan matan "ta hanji ta hanji debo ruwa ki kaiwa bakon da ke waje" ta hanji tace "uhm, na ci kwalliya, in debo ruwa in kai wa bakon da ke waje! sannu iya"

Tsohuwa ta cewa ta huhu ta kai wa bakon ruwa, itama tace abunda ta hanji ta fadi. Har dai sai da tsohuwa ta zo kan ta kitse, wadda kuma tafi duk 'yan matan kyau. Da aka ce ma ta ta kai ruwa waje, sai tace "to iya".

Ta kitse tana fita waje sai bafaden sarki ya dauke ta sai gudu! Ya kaiwa sarki ita, ya (sarki) aureta.

Sarki ya bada kashe di kar a sake a bar ta kitse tayi wani aiki na kusa da wuta. Su kuwa sauran matan gidan haushin ta suke ji! saboda tana da kyau sosai, gashi kuma sarki yana sonta! Rashin sa'a watarana sarki ya fita yaki, sai kuwa sauran matan gidan suka ce ay sai ta kitse ta fito tayi masu girki.

Saboda hakurin ta kitse, sai ta fito tsakar gida zata yi masu girki. ay kuwa da wuta ta buge ta! sai ta narke!!

Ashe wata tsunsuwa tana wajen ta gan me ya faru! Sai ta tafi wajen da sarki yake yaki tana waka tana cewa "sarki sarki a maida yaki baya ta kitse ta narke, ta narke ta zama ruwa sakar gida" tun sarki bai ji me tsunsunwa take cewa ba har dai yaji!

Sarki yana ji! sai kuwa ya hau dokinshi sai gida! yana zuwa aka zuba mata ruwa ta farfado ( ::)) ya tambaya waye yayi mata haka...aka ce mashi sauran matan ne. sai kwai sarki yasa aka gille masu kai!

Sarki da ta kitse kuma suka zauna cikin jin dadi....

kurunkus kan dan bera... da ban dan gizo ba da nayi karya...(lol)



Kai! in banda ta tsuniya ma, yaushe haka take faruwa... ::)

This sooo much reminds me of the olden days... ;D
greetings from Ihsaneey

Rose

Kai Ihsan! :D
Amma wallahi angaisheki
wannan irin tatsuniya kamar daga bakin granny :)
Agaskiya kintunamin da jiya
Think of some more please
aNo Ta DaBo ChiGaRii, GaRi Ba KaNo Ba DaJin ALLaH.

Ihsan

l Ice...nima sai y atuna mun da baya :)

To gyara zama...ga wata nan tafe... 8)


Ruwan Bagaja

Gata nan gata nan ku...

Wani mutum ne yana da mata biyu;da mowa da bora. ko wace mace tana da 'ya guda daya. An sani bora da 'yar ta a gidan!

Watarana 'yar mowa tayi fitsarin kwance sai aka ce ay 'yar bora ce tayi dan haka dole taje kogin bagaja ta wanke abun da tayi fitsarin akai.

'Yar bora ta kama hanya ta tafi neman kogin bagaja! Akan hanyar sai ta hadu da wani kogi tace "kogi kogi ko kaine ruwan bagaja bagajar gayya ta dan sarki. domin kirgi aka aiko ni inzo in wanke a ruwan bagaja" And the kogi (river) replied "yarinya ni ba kogin ruwan bagaja bane. ni kogin tuwo da miyar taushe ne zauna ki ci idan kina so" 'yar Bora tace a'a ta gode amma ta koshi.

Ta kara yin gaba and she came across another river and asked it ko shine kogin bagaja and the river replied "yarinya ni kogin shinkafa ne da miya idan zaki ci zauna ki ci" tace aa ta gode amma ba ta ci.

She continued on her journey and came across another river...asked it same question and it replied "ni kogin alkaki ne da nakiya...da dai sauran irinsu". she said same thing to this river as she said to the other.

Tana ta tafiya tana wuce all sorts of rivers na kayan abinci har hadari ya hado...garin yayi duhu za'a yi ruwa! Then she saw a hut sai ta shiga ciki. Inside the hut she saw a thigh (YES A THIGH lol),a dog,a pot, rice, and some eggs

Tana shiga sai cinya tace "kan kan" sai kare yace wai cinya tana maki maraba.'Yar bora tace ta gode. Cinya ta kara cewa "kan kan" sai karen yace mata thigh din tace wai ta dauki kwayar shinkafa guda daya!!!ta girka masu.  She didn't argue. She cooked the single rice in the pot and it became da yawa har ya cika tukunyar.

Suka ci suka koshi. Next day tayi sai 'yar bora tace zata tafi neman kogin bagaja. Sai cinya tace "kan kan"  karen yace cinyar tace ta dauki eggs guda daya (big and small) taje wani waje dashi (can't remember the place) and say "in fasa" idan taji an ce "fasa fasa musha ruwan kawai" she shud not fasa it. But idan taji shiru sai ta fasa. 'yar Bora ta dauki karamin egg din tayi godiya ta ta kama hanya.

When she came to the place sai ta ce "in fasa" taji an ce fasa fasa musha ruwan kwai. Sai bata fasa ba tayi gaba. asked again but sai taji shiru, ta kara tambaya ta ji shiru...she asked three x b4 ta fasa.

Tana fasawa kuwa sai ga mutane akan doki...mutanen sun sha ado sosai ana ta busa algaita. Suka dora 'yar bora akan doki sai gida.

Suna shiga cikin gari sai garin ya fara kanshi yara suna ta binsu. Mutanen suka kai 'yar mowa har gida mamanta ta fito tana ta murna. Mutanen suka bawa bora da mamanta kudi sosai...sannan sai suka tafi. Bora da 'yarta suna ta murna.

Hmmm ashe anyi creating a monster!!! coz da mowa ta ga haka ya faru da 'yar bora, sai tace ay itama 'yarta sai taje kogin bagaja gobe...dan haka tayi fitsari gobe ta tafi wanke kirgi a bagaja.

The next day 'yar mowa set off in search of kogin bagaja. And she came across one river tace "kogi kogi ko kaine ruwan bagaja bagajar gayya ta dan sarki. domin kirgi aka aiko ni inzo in wanke a ruwan bagaja" And the kogi (river) replied "yarinya ni ba kogin ruwan bagaja bane. ni kogin tuwo da miyar taushe ne zauna ki ci idan kina so" and she replied "yau naji wani rin kogi!!! ina ganin tuwo da miyar taushen in wuce ban ci ba! lallai ma!!!" ta zauna ta ci tuwo ta koshi.

Ta kara yin gaba and she came across another river and asked it ko shine kogin bagaja and the river replied "yarinya ni kogin shinkafa ne da miya idan zaki ci zauna ki ci" nan ma tace lallai ma ya za'a yi ta wuce kogin shinkafa da miya...ta zauna ta ci ta koshi.

Tana ta tafiya tana wuce different kind of rivers na abinci and duk inda taje sai ta ci abinci. Dare ya fara yi ga kuma hadari ya taso za'a yi ruwa. Sai ta hango wata hut and sai ta shiga.

Da ta shiga sai taga cinya da kare (and all the things 'yar bora saw). Tana shiga sai cinya tace "kan kan" sai kare yace wai cinya tana maki maraba. 'yar mowa na jin haka sai kuwa cewa tayi "wannan wace irin cinya ce mai magan?? da kare mai magan?? yau naga ikon Allah" cinya ta kara cewa "kan kan" kare yace tace wai ki dauki kwayar shinkafa guda daya ki dafa. 'yar mowa tace ita kam ba zata dafa shinkafa daya ba! bayan ga shinkafar nan da yawa sannan wani ace ta dafa guda daya!!! ta debo shinkafa da yawa ta dafa! and the rice became kadan...basu ma koshi ba.

Next day tayi sai 'yar mowa ta shirya zata tafi sai cinya tace "kan kan" sai kare yace tace wai ki dauki kwai guda daya and go to some place and say in fasa...idan kinji an ce fasa fasa musha ruwan kwai, kar ki fasa sai inda kika ji shiru. 'Yar mowa tace tabdijan ina jin mutane sunyi magana inki fasawa?? lallai ma. 'yar mowa ta dauki big egg din and left without thanking the thigh and the dog!!

Tana zuwa wajen kuwa sai tace in fasa...sai taji ance fasa fasa musha ruwan kwai...ay kuwa sai ta fasa!!! hmmmm tana fasawa sai ga kuture da makafi on donkies gudaje sai binsu suke yi...ga wari da yake ta tashi!!!

Aka dora 'yar mowa kan jaki sai gida. Suna shiga cikin gari sai garin ya kama wari...yara sai gudu ake yi!!! Aka je kofar gidan su 'yar mowa mamanta ta fito ta tare ta...sai kuwa ta ga kutare da makafi...nan tai ta masifa wai 'yar ta ta kwaso mata gayyar wari da kazanta. Haka dai suka sauki mata 'yarta ba tare da sun bata komai ba sai rabon wari!!!

'Yar bora kuwa da mamanta suna can suna cin dadinsu...they lived happily ever after ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Kurunkus kan dan bera...... till we meet again.... 8)
greetings from Ihsaneey

Ihsan

WHOA  :o amma fa na rubutu da kyau... da badan na gaji ba da na rubuta wata yanzu...but tomorrow insha ALlah... :)
greetings from Ihsaneey

Ibro2g

This is very interesting...I`ll make a rendevous here.
Safety and Peace

IBB

QuoteUNCLE SALIS, BA'A YI MAKA TATSUNIYA BANE KANA YARO? KO DAYAKE DUK BATA BACI BA IBB BAMU MU SHA.. BARI NIMA NA ZAUNA NA TANKWASHE KAFA YADDA UNCLE SALIS YAYI A BAMU MU SHA!!!!!!!!!!! ;D

kai dodon kodi. to zauna kasha tasuniya
IHS

IBB

gata nan ga tanan ku

wata rana sarkin abasha yasa gasar shan yaji. amma mutum

ba zai yi shan-jayi (shii) ba, wanda yaci gasar za'a bashi

sarautar rabin ragin inka fadi 'a kashe ka. kowa yace ba sai

iya ba. sai ga oga gizo yazo yace ai shi zaiyi aka ba shi jayi

yake sha dogari na tsaye akan sa. idan gizo ya sha ya sha sai

ya kalli dogari yace ai kaji ban ce shii ba ko in an jima sai ya

kara tambayar sa ko yace shii sai yace 'a'a.


TO BE CONTINUED
IHS

Blaqueen

da Hunniez Gettin Money Playin Niggaz Like Dummy

ummita

Quote
kai dodon kodi. to zauna kasha tasuniya

Wat amuses me d most iz wat IBB had, anywayz jjc'z cud b stupid @ tyms ::)...........du u know UNCLE SALIS sune masu nen wajen.......Did sum1 juss kall Salis dodon kodi :o :o(ummita fainted as well juss lyk her blad did) :-X
Despite ur slammin, am still jammin!!!

Ihsan

AM BACK and iiiiiitttttttttttt'sssss STORY TIME... ;D

Gata nan Gata nan Ku...

Daskindaridi

A wani gari da akwai wasu 'yan mata wanda suke living tare in one house. Da alkama, shinkafa, dawa, ... , and last but not the least, daddawa.

Sun sani daddawa kamar me. Komai ba'a yi da ita. Sai watarana aka yi shela a gari cewa duk 'yan matan gari su hadu a wani fili za'a yi gasa. Ita wannan gasar ta a yi guessing sunan dan sarki ne! duk wanda yayi guessing zai aure dan sarkin.

Su alkama, dawa, and the rest ana ta murna za'a tafi filin gasa. Ranar gasar ta zo duk 'yan matan suka ci kwaliyya banda daddawa saboda bata da abun sakawa! kuma sauran 'yan matan suna ta yi mata dariya.

Haka suka shirya suka tafi ba tare da daddawa ba. Abun tausayi daddawa ta saka 'yan kayanta wadanda take ji dasu ta kama hanyar filin gasa.

On their way, sai 'yan matan nan suka hadu da wata tsohuwa tana wanka a rafi. The old lady asked one of them to wash her back and the girl replied lallai ma iya baki ganin na ci kwaliyya ki ce wani na wanke maki baya! sannu ma. Duk a cikin 'yan matan nan aka rasa me wanke wa tsohuwa baya!

Bayan 'yan matan sun wuce sai ga daddawa ta taho. 'Yar tsohuwa tace mata dan Allah 'yan mata wanke mun bayana. Daddawa tace to iya... tana cikin wanke wa 'yar tsohuwa baya sai kuwa bayan tsohuwa ya burme  :o.

Daddawa ta rasa yadda zata yi! sai tace iya dan Allah yi hakuri bayanki ya burme. Tsohuwa tace me kika gani a ciki? tace wasu boxes guda biyu (big and small). Tsohuwa ta ce ta dauko small one din. When she opened (I can't remember what's inside the box) but I think kaya ne. Tsohuwa tace mata ta saka kayan.

Daddawa ta saka kaya tayi kyau sosai. The old lady then asked her ko ta san sunan dan sarkin? sai tace aa...and so tsohuwa whispered the name in her ear. Daddawa tayi godiya ta kama hanyar filin gasa.

A can kuma wajen gasar ana ta fafata da 'yan mata. Kowacce ta zo wajen dan sarkin sai ta gaya mashi sunan ta idan ya tambayeta sunan shi sai ta ce bata sani ba...shi kuma idan yaji haka sai yace koma da baya ki sha kuka...'yan mata sai kuka ake yi.

Ana cikin haka sai ga daddawa ta iso. 'Yan mata na ganinta sai aka fara zunden ta ana cewa ita kuma wannan daga ina? waya bata aron kaya? muma bamu san sunan shi ba bare ita? suna ta dai maganganu irin haka.

Ita dai daddawa bata ce komai ta karasa wajen tent din dan sarki

daddawa: "Assalaam salaam dan yaro, assalaam salaam"

dan sarki: "wacece nan take mana assalaam salaam"

daddawa: "daddawarka ce take maka assalaam salaam, me dadi a miya dan yaro, me dadi a miya"

dan sarki: naji naki suna yarinya kawo nawa suna

daddawa: daskindaridi dan yaro, daskindaridi

dan sarki: bude ki shigo yarinya, bude ki shigo ki sha dadi.
[/b]

Daddawa ta bude labulen tent ta shiga ciki...sauran 'yan matan suna ta jin haushi suna mamakin yaya aka yi ma ta san sunan dan sarkin!!!

The next day daddawa and daskindaridi got married and they lived happily ever after...

and this writer is tired and need some rest... ;D
greetings from Ihsaneey

Ihsan

Me is Back... And today's story is...

Sarma Sarma du duf

Gata nan ga ta nan ku...

A wani a gari da akwai wata yarinya wacce tace ita baza ta aure kowa ba sai mara tabo (mark) a jikin shi!!! ko wani namiji ya zo wajen ta sai tace aa yana da tabo on his body.

Haka dai ko da yaushe take yi har watarana wasu doddani su biyu suka ji labari. Sai suka je gidan tururuwa suka yi wanka suka zama samari masu kyau.

Suka kama hanya sai garin da yarinyar take. Da suka isa sai suka karasa gidan su yarinyar. Aka yi masu sallama da ita ta fito. Da ta duba na farko ashe tururuwa ta chije shi a wuya dan haka sai tace ay shi yana da tabo. Sai second guy din he had nothing on his body sai tace to she'll marry him.

Suka yi aure and he took her to his house where he lives with his mother. First day bayan sun kwanta bacci ita da kanwarta (sister), sai kuwa suka ji a bakin kofa ana "sarma sarma du duf" ashe mother-in-law din ce
yarinya: wane ne nan yake mana sarma sarma du duf?

mother-in-law : uwar mijin ki ce taki miki sarma sarma du duf

yarinya: me kike so ki ke mana sarma sarma du duf?

mother-in-law: wuta nake so nake maki sarma sarma du duf

and then sai yarinyar ta debo wuta a kasko ta mika mata

yarinya: gashi nan ki diba ki bar mana sarma sarma du duf.

Da ta mikawa mother-in-law din, sai uwar mijin ta kase wutar and asked the girl for wuta again. They repeated the same thing as before and again uwar mijin ta kara kashe wutar. Suna tayin haka har gari ya waye sannan aka hakura. kuma duk hakan da ake yi lokacin maman miji ta zama dudanniya (not in her human form).

In the afternoon kuma sai kanwar (sister) ta tafi kai wa mijin yayarta abinci a gona (farm) sai kuwa ta gansu sun zama dodanni suna ta cin kwadi (frogs) :o. Ita kuma sai ta kama waka tana cewa "mijin yata ci da kwadi, mijin yata sha da kwadi"

Haka kullun wannan episode din yake faruwa between mother-in-law and her daughter -in-law and kuma kanwar matar and mijin matar.

Rannan dai suka (the girl and her sister) gaji sai suka hada plan na su gudu. Safiya nayi kuwa suka bi ta wani hole suka gudu. Da suka isa gida sai tace ita bata son auren.

Daga sannan bata kara duba tabo jikin namiji ba idan yazo wajen ta...har dai a karshe ta aure wani daga cikin masu zuwa wajenta...


:-/ :-/ :-/ hmmmm *scratching ma head*
greetings from Ihsaneey

ummita

U keep em cumin Ihsaneey we've got Gizo, Daskenderidi,Mora & Mora..............Nyc one babes ;)[/b]
Despite ur slammin, am still jammin!!!